Ana Shirin Bikin Sallah, Tinubu Ya Yi Umarnin Rabawa Talakawa Shinkafa
- Yayin da azumin watan Ramadan ke shirin karewa, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin raba shinkafa ga 'yan Najeriya
- Rabon shinkafar zai shafi al'ummar Musulmi da Kiristoci a fadin kasa lura da cewa Kiristoci ma suna gudanar da azumin Lent a yanzu
- Shugaban kungiyar Renewed Hope Ambassadors mai goyon bayan Bola Tinubu, Hope Uzodimma ya yi karin bayani kan rabon da za a yi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar Renewed Hope Ambassadors mai goyon bayan Bola Ahmed Tinubu ta samu umarnin raba shinkafa a fadin Najeriya domin tallafa wa al’umma da ke gudanar da azumin watan Ramadan da kuma azumin Lent na Kiristoci.
Rahoto ya nuna cewa shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar.

Kara karanta wannan
Iran: An harba makamai filin jirgin da Amurka ke aiki da shi, bakin hayaki ya tashi

Source: Facebook
Bayani kan raba shinkafar Tinubu
Sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar a X ta ce an shirya rabon ne domin karfafa hadin kan kasa tare da nuna tausayi a lokacin da Musulmi da Kiristoci ke ibadar azumi tare.
Gwamna Uzodinma ya ce wannan mataki yana nuna kudurin shugaba Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da hadin kai da kuma nuna kulawa ga jama’a.
Ya kara da cewa watan Ramadan da kuma lokacin azumin Lent lokuta ne da ke tunatar da mutane muhimmancin sadaukarwa, taimakon juna da kuma kula da makwabta.
Punch ta rahoto sanarwar ta ce:
“Ta hanyar wannan rabon shinkafa, kungiyar Renewed Hope Ambassadors za ta tabbatar da cewa iyalai a fadin Najeriya sun ji dadi a wannan lokaci mai tsarki,”
Yadda za a raba shinkafar Tinubu
Sanarwar ta kara da cewa kungiyar za ta gudanar da rabon ne ta hanyar cibiyoyinta na kasa baki daya domin tabbatar da cewa iyalai a sassa daban-daban na Najeriya sun amfana da wannan tallafi a lokacin da Musulmi da Kiristoci ke azumi.
A baya ma an gudanar da irin wannan shiri a lokacin bukukuwan Kirsimeti, inda aka raba shinkafa domin taimaka wa ‘yan Najeriya a lokacin bukukuwa, a matsayin wani bangare na kokarin gwamnatin na tallafawa jama’a.

Source: Facebook
An ce rabon shinkafar zai shafi al’ummomin Musulmi da Kiristoci baki daya, abin da ke nuna manufar shugaban kasa ta hada kan kowa da kuma tabbatar da cewa babu wanda aka ware.
Sanarwar bata kunshi lokacin da za a fara raba shinkafar ba, abin da wasu ke ganin idan ba sa'a ba azumi zai iya karewa ba tare da farawa ba.
Makari ya yi kira ga Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa limamin masallacin kasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Makari ya yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yunkurin juyin mulki.
Malamin ya bukaci a saki wadanda aka kama bisa zargin suna da hannu a yunkurin juyin mulki amma ba a same su da laifin komai ba.
Ya bayyana cewa cikin wadanda ba a samu da laifi ba akwai babban malamin Darika, Sheikh Sani Khalifa Zariya da ke cigaba da zama a tsare.
Asali: Legit.ng
