Ana tsakiyar Musayar Wuta, Trump Ya Yi Magana kan Kawo Karshen Yaki da Iran
- Donald Trump ya gargaɗi Iran cewa Amurka ba za ta dakatar da yaƙi ba har sai ta samu wasu sharuɗɗan yarjejeniyar da take buƙata
- Isra'ila ta kai sabbin hare-hare yammacin Iran yayin da dakarun IRGC suka lashi takobin kashe Benjamin Netanyahu a matsayin ramuwar gayya
- Rayuwar yau da kullum ta fara dawowa a birnin Tehran yayin da kasuwanni suka buɗe domin shirin bikin Nowruz duk da barazanar yaƙin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa har yanzu gwamnatinsa ba ta shirya tsayawa domin ƙulla yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Iran ba.
Trump ya nuna cewa ko da yake yana jin Iran na buƙatar tattaunawa, Amurka za ta ci gaba da kai hare-hare domin samun sharuɗɗa mafi tsauri.

Source: Getty Images
Trump ya yi magana kan sulhu da Iran
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na NBC News, inda har ma ya yi barazanar sake jifan matatar man fetur dake tsibirin Kharg domin nishaɗi kawai.
Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da yaƙin ya shiga mako na biyu, inda ake samun hauhawar farashin man fetur a duniya sakamakon rufe mashigar ruwan Hormuz.
Shugaba Trump ya lashi takobin cewa dakarun Amurka za su ƙara kaimi wajen luguden wuta a gabar tekun Iran domin tabbatar da cewa jiragen dakon mai sun fara zirga-zirga.
"Iran suna son a sasanta, amma ba zan amince da hakan ba saboda ba su gabatar da wasu kwararan abubuwan da hankali zai dauka ba."
- Donald Trump.
Halin da Khamenei yake ciki
Shugaban Amurka ya kuma jefa ayar tambaya kan halin da sabon jagoran addini na Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei yake ciki.

Kara karanta wannan
Harin tsibirin Kharg: Shugaban Amurka ya ga abin da bai yi tsammani ba a yaki da Iran
Duk da cewa Mojtaba ya fitar da sanarwar lashi takobin ci gaba da rufe mashigin Hormuz, Trump ya nuna shakku kan ko yana raye tunda har yanzu ba a nuna shi a fili ba.
Ita kuwa gwamnatin Iran ta dage cewa babu wani mummunan abu da ya samu sabon shugaban, kodayake bai riga ya bayyana a gaban jama'a ba tun bayan rantsar da shi, in ji rahoton The Guardian.

Source: Getty Images
Isra'ila ta kaddamar da hare-hare a Iran
Yayin da kalaman Trump ke ruruwa, rundunar sojin Isra'ila ta sanar da ƙaddamar da wasu sabbin hare-hare kan wasu wurare a yammacin Iran.
Wannan mataki na zuwa ne bayan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun ayyana Firayim Minista Benjamin Netanyahu a matsayin mai babban laifi tare da cewa za ta kashe shi.
Duk da tsauraran kalaman yaƙi, mazauna birnin Tehran sun fara fita harkokinsu na yau da kullum a cikin natsuwa tun bayan fara yaƙin.
An bude sama da kashi ɗaya bisa uku na shagunan kasuwar Tajrish domin shirye-shiryen sabuwar shekarar Farisa dake tafe nan da kwanaki biyar.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Ana cikin gwabza fada, Trump ya fadi bukatar da shugabannin Iran suka nema
Alakar Rasha da Iran a yaki da Amurka
A wani labari, mun ruwaito cewa, Biritaniya ya bayyana cewa Rasha na marawa Iran baya wajen amfani da jirage marasa matuka domin yakar Amurka da Isra'ila.
Ministan tsaro, John Healey ya yi ikirarin cewa Rasha na tura wa Iran dabarun yaki da ta koya a yakinta da Ukraine domin rura wutar rikicin Gabas ta Tsakiya.
Wannan na zuwa ne yayi da Biritaniya ta kakkabo wasu jiragen Iran dake kokarin kai hari sansanonin soji yayin da yakin yake cigaba da tsananta.
Asali: Legit.ng
