Luguden Wutar Amurka da Isra'ila Ya Yi Barna a Kasar Musulunci, Sama da Mutum 100 Sun Mutu
- Hukumomin kasar Iran sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 112 a hare-haren da Amurka da Isra'i'a ta kai lardin Kurdista
- Shugaban sashen ba da agajin gaggawa na lardin ya ce mutane da dama sun jikkata a hare-haren da aka kai yankin na Iran
- Bayan haka, gwamnatin Iran ta bayyana cewa yakinta da Amurka ya jawo lalata wasu muhimman wuraren al'adu a sassan kasar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Akalla mutane 112 ne suka rasa rayukansu, yayin da 969 suka jikkata, sakamakon hare-haren da Amurka da Isra'i'a ke kai wa lardin Kurdistan a Iran.
Wannan na zuwa ne yayin da yakin Amurka, wacce ta hada gwiwa da Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke kara kamari tun bayan barkewarsa a karshen watan Fabrairu, 2026.

Source: Twitter
An kashe mutane da dama a kasar Iran
Kamfanin dillancin labarai na Tasnim News Agency ya ruwaito cewa shugaban sashen agajin gaggawa na lardin ya bayyana cewa mutane da dama sun jikkata sakamakon hare-haren jiragen sama da makamai masu linzami.
A cewarsa:
"Mutane 27 na kwance a asibitoci suna karbar magani, wasu biyar suna cikin dakin kulawa ta musamman (ICU) saboda tsananin raunuka
"Hare-haren na daga cikin manyan farmakin da ake kai wa yankin Arewa maso Yammacin Iran tun bayan fara yakin a ranar 28 ga Fabrairu, 2026."
Amurka, Isra'i'a sun lalata wuraren al'adu a Iran
A wani bangare kuma, ma’aikatar al’adu ta Iran ta bayyana cewa hare-haren Amurka da Isra'ila sun lalata akalla wuraren tarihi da al’adu 56 a sassan kasar.
Rahoton ya nuna cewa wuraren tarihi 19 sun lalace a lardin Tehran, sannan kuma 12 daga cikin manyan wuraren tarihi sun lalace a lardin Kurdistan
Wadannan wurare sun hada da gidajen tarihi, tsofaffin gine-gine da wuraren tarihi masu daraja, wadanda ke da muhimmanci ga tarihi da al’adun Iran.

Source: Getty Images
Tun bayan fara yakin tsakanin Iran da hadin gwiwar kasashen Amurka da Isra’ila, rahotanni sun nuna cewa dubban mutane sun jikkata yayin da daruruwan suka mutu

Kara karanta wannan
Amurka da Isra'ila sun yi babbar barna a kasar Musulunci, fiye da mutane 1,400 sun rasu
Haka zalika, bayanai sun nuna cewa kasashen biyu sun kuma lalata kayayyakin more rayuwa da wuraren tarihi a sassan kasar Iran.
Masana na gargadin cewa idan rikicin ya ci gaba, asarar da za a iya samu ta rayuka, tattalin arziki da al’adun yankin na iya kara tsananta, cewar tashar Al-Jazeera.
Sojojin Iran sun yi ikirarin kakkabo jirage 111
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin juyin juya halin Musulunci na Iran sun bayyana wasu daga cikin nasarorin da suka samu a yakin kasar da Amurka/Isra'i'a zuwa yanzu.
Sojojin Iran sun sanar da cewa sun kakkabo jiragen yaki marasa matuki 111 tun bayan fara yakin a Asabar, 28 ga Fabrairu, 2026.
Rahotanni sun nuna cewa rundunar kariyar sararin samaniyar Iran ta harbo wani jirgin yaki maras matuki na Amurka kirar MQ-9 Reaper a kusa da lardin Fars.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
