AbdulJabbar Kabara Ya Rubuta Takardar Zargin Gwamnatin Kano da Shirya Masa Makarkashiya
- Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ya aika wa shugaban kotun daukaka ƙara ƙorafi kan zargin ana shirya masa makarkashiya a Kano
- Malamin ya ce shirin rushe gidan yari na Kurmawa a Kano na iya zama dabara domin bacewar muhimman takardun shari'ar da ake yi da shi
- Gwamnatin Kano na shari'a da malamin a kan zargin batanci ga Fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW har an yanke masa hukuncin kisa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara, ya rubuta takardar tunatarwa mai shafuka shida zuwa ga shugaban kotun daukaka ƙara ta Najeriya.
A cikin takardar Malamin ya yi zargin cewa akwai wani shiri da gwamnatin Kano ke yi na kulla masa makarkashiya a shari'ar da ya daukaka bayan an yanke masa hukuncin kisa.

Source: Facebook
A koken da Ashabul Khafi ta wallafa a shafinta na Facebook, AbdulJabbar Kabara ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Kano na shirin lalata wasu muhimman takardun shari’arsa.
AbdulJabbar Kabara ya yi koke kan gwamnatin Kano
A cikin takardar mai kwanan wata 13 ga watan Maris, 2026, Abduljabbar Nasiru Kabara ya gwamnatin Kano na rushe tsohon gidan yarin Kurmawa domin mayar da shi gidan tarihi.
Ya bayyana cewa wannan mataki na iya zama wata dabara ta hana ci gaban ƙarar da yake yi a kotun daukaka ƙara.
Malamin, wanda a yanzu yake tsare gidan gyaran hali da ke Kuje a Abuja, ya ce wasu takardun shari’arsa suna nan a cikin tsohon ɗakinsa a gidan yarin Kurmawa da ke Kano.

Source: Facebook
A cewarsa, wata majiya da ya kira “tabbatacciya” ta bayyana cewa Mai ba gwamnan Kano shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ya tabbatar da shirin rushe gidan yarin.
Ya kuma zargi cewa an taɓa samun yunƙurin shiga ɗakinsa domin taɓa takardun, inda ya ce an taɓa karya makullin ɗakin a lokacin da ya fita domin ganawa da baƙi.
Sheikh AbdulJabbar Kabara ya nemi daukin kotu
A cikin takardar tunatarwar, malamin ya kuma ja hankalin shugaban kotun daukaka ƙara kan abin da ya kira manyan kura-kurai da sauya ma’ana wajen fassara bayanan shari’ar da aka tura kotun. A cewarsa, waɗannan bambance-bambancen na iya janyo ruɗani ga kotun daukaka ƙara tare da hana ta fahimtar cikakken yanayin shari’ar. Malamin ya kuma dage cewa shari’ar da ake yi masa abu ne da ya ce ya kamata jami’o’i su duba, ba kotunan shari’a na yau da kullum ba.
A cikin buƙatunsa, Abduljabbar ya roƙi shugaban kotun daukaka ƙara da ya ɗauki matakan da za su kare takardun shari’arsa, tare da duba fassarar takardun hujjojin da aka fassara daga Hausa zuwa Turanci. Domin tabbatar da zarginsa cewa takardun suna nan a Kurmawa, malamin ya lissafo sunayen shaidu shida, ciki har da Alhaji Danladi Me Zare da Alhaji Baban Kadawa.
Amirul Wa'izin ya ce sun samu tabbaci daga Babban mai kula da gidan yarin Kurmawa, Isyaku Yakasai, a ranar 19 ga Fabrairu, 2026 cewa takardun suna nan lafiya. Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya roƙi shugaban kotun daukaka ƙara da ya sa baki cikin lamarin domin tabbatar da adalci. A watan Disamban 2022 ne wata babbar kotun shari’ar Musulunci ta jihar Kano ta yanke masa hukuncin kisa bisa zargin ɓatanci, hukuncin da yake ƙalubalanta a kotun daukaka ƙara har zuwa yanzu.

Kara karanta wannan
"Ba za mu lamunci cin amana da rashin biyayya a jihar Kano ba": Gwamna Abba Kabir
An mayar da AbdulJabbar Kabara Abuja
A baya mun wallafa cewa hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Kano ta tabbatar da cewa ta mayar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wani gidan gyara hali a Abuja.
Mai magana da yawun hukumar, Musbahu Kofar Nassarawa, ya ce matakin ya yi daidai da dokokin aiki da tsarin tsaro da hukumar ke bi, saboda haka ana kan turba.
Hukumar NCoS ta tabbatar da cewa sauya wurin ba zai shafi hakkokin shari’a, walwala da damar kare kansa ta doka ta ba Abduljabbar ba, kuma an sauya masa wuri ne saboda tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

