Juyin Mulki: Farfesa Makari Ya Fadawa Tinubu Abin da ake Tsoron Sanar da Shi

Juyin Mulki: Farfesa Makari Ya Fadawa Tinubu Abin da ake Tsoron Sanar da Shi

  • Limamin masallacin kasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Makari ya yi magana game da tsare mutanen da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulki
  • Malamin ya yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce da yawa daga cikin manyan jami'an gwamnati suna tsoron tunkararsa da batun
  • Babban malamin Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Sani Khalifa Zariya na cikin wadanda aka kama aka tsare kusan sama da wata uku da suka wuce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Farfesa Ibrahim Makari ya yi kira ga shugaban Najeriya game da mutanen da aka kama bisa zarginsu da hannu a yunkurin juyin mulki.

Malamin ya bayyana cewa akwai wadanda rahoton bincike ya nuna cewa ba su da hannu kai tsaye a lamarin, tsautsayi ne kawai ya rutsa da su.

Kara karanta wannan

Da gaske Netanyahu ya bata yayin yakin Isra'ila da Iran? An samu bayanai

Farfesa Ibrahim Makari da Bola Tinubu
Farfesa Ibrahim Makari a hagu, Shugaba Bola Tinubu a dama. Hoto: Bayo Onanuga/Ibrahim Makary
Source: Facebook

Farfesa Ibrahim Makari ya yi magana ne yayin tafsir da ya ke gabatarwa a masallacin kasa da ke Abuja kamar yadda wani bidiyo da Ahmad Mukaddam ya wallafa a Facebook ya nuna.

Wadanda aka kama saboda zargin juyin mulki

A bayanin da ya yi, Farfesa Makari ya ce akwai wadanda aka kama amma ba su da laifi, ya ce akwai wadanda kudi aka tura ta asusun bankinsu bayan sayayya a wajensu amma yanzu suna garkame.

Ya kara da cewa Sheikh Sani Khalifa Zariya kuma kudi aka tura domin ya yi addu'a ba tare da sanin cewa juyin mulki za a yi ba, ya ce hakan kuma ba laifi ba ne.

Makari ya bayyana cewa al'ada ce a tsakanin malamai a roke su su yi addu'a a kuma ba su wani abu, inda ya ce ba lallai su tambayi ina mutum ya samo kudin shi ba.

Kara karanta wannan

An yi wa sojojin Faransa ruwan wuta ana tsaka da yakin Iran da Amurka

Sheikh Makari ya ce har shi da sauran malaman Musulunci a kan ba su kudi da nufin su yi addu'a a Najeriya.

Me ake tsoron sanar da Bola Tinubu?

A cikin bayanin da ya yi, Sheikh Makari ya ce akwai kalubale babba tattare da matsalar, inda kusan kowa da kowa yake tsoron ya tunkari Shugaba Tinubu da zancen juyin mulkin.

Ya ce:

"Kowa tsoro ya ke kar ya tunkari shugaban kasa ya yi laifi."

Makari ya ce sun yiwa wasu daga cikin manyan mutane uzuri saboda yanayin aiki su:

"Kowa a tsorace ya ke."

Saboda haka Malamin ya ce su suna ganin shugaban kasa mutum ne kamar kowa amma suna girmama shi, a kan haka suka masa kira na musamman.

Sheikh Sani Khalifa Zariya
Sheikh Khalifa Zariya da aka tsare a Abuja. Hoto: Sheikh Sani Khalifa Zaria
Source: Facebook

Kiran Makari ga Shugaba Tinubu

A rokon da ya yi, Farfesa Makari ya ce suna rokon Shugaban kasa ya yi aiki da rahoton da aka gabatar masa game da yunkurin juyin mulki domin a saki wanda ba su da laifi su koma ga iyalansu.

Ya ce:

"Don Allah a gaggauta zartar da abin da aka samu na rahoton".

Kara karanta wannan

An fara kiran Tinubu ya ajiye Amurka a gefe, ya dauki darasi daga kasar Iran

Malamin ya kara da rokon cewa wadanda aka samu da laifi ma suna rokon shugaban kasa ya taimaka yasa a musu hukunci mai sauki.

Malaman da aka dakatar daga wa'azi

A wani labarin, mun kawo muku jerin wasu malaman Musulunci da aka taba dakatarwa daga wa'azi a Najeriya a baya bayan nan.

Sheikh Muhammad Nuru Khalid na cikin wadanda aka dakatar saboda wata huduba da ya yi a wani masallaci a birnin tarayya Abuja.

A watan Ramadan 1447, kungiyar Izala mai hedkwata a Jos ta dakatar da Alkali Abubakar Salihu Zariya saboda wasu maganganu da ya yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng