Iyalan El Rufa'i Sun Dura a kan ICPC bayan Ikirarin Gano Na'urorin Kutsen Waya a Gidansu

Iyalan El Rufa'i Sun Dura a kan ICPC bayan Ikirarin Gano Na'urorin Kutsen Waya a Gidansu

  • Iyalan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, sun karyata zargin gano na’urar sauraren waya a gidan mahaifinsu da ke Abuja
  • Dan sa kuma dan majalisar wakilai, Bello El-Rufai, ya ce zargin da hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta yi karya ne
  • Iyalan sun ce binciken da aka yi a gidan haramtacce ne saboda takardar izinin bincike da ake zargin an yi magudi da ita

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun yi tir da zargin cewa jami’an hukumar (ICPC) bayan binciken da aka yi a gidan tsohon gwamnan.

Jami'an ICPC sun bayyana cewa sun gano wasu na’urori na musamman da ake amfani da su wajen sauraren wayoyin mutane da kuma wasu takardun tsaro masu muhimmanci.

Kara karanta wannan

ICPC ta samu damar kara garkame El Rufa'i na kwanaki 14, akwai yiwuwar ya yi sallah a tsare

Iyalan El-Rufa'i sun yi magana kan kalaman ICPC
Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa a cikin wata sanarwa da aka fitar a madadin iyalan a farokon wannan mako, dan tsohon gwamnan, Bello El-Rufai, ya ce babu kamshin gaskiya ko kadan a ikirarin ICPC.

Iyalan Nasir El-Rufa'i sun caccaki ICPC

Business Day ta ruwaito cewa sanarwar ta jaddada cewa babu wata na’urar sauraren waya da jami’an hukumar suka samu lokacin da suka kai samame a gidan tsohon gwamnan.

Rahotanni sun nuna cewa Nasir El-Rufai ya shigar da kara a kotu yana zargin cewa kama shi da tsare shi da aka yi ya saba wa hakkinsa na kundin tsarin mulki.

Ya bukaci kotu ta ayyana matakan da hukumomin yaki da cin hanci suka dauka a kansa a matsayin ba bisa ka’ida ba, sannan ta umarci a biya shi diyyar Naira biliyan daya.

Martanin hukumar ICPC ga El-Rufa'i

Sai dai a martanin da ta mayar, ICPC ta gabatar da takarda tare da wasu takardu da hujjoji domin ta kalubalanci karar.

Kara karanta wannan

Bidiyon lokacin da makamin Iran ya fada tsakiyar birnin Isra'ila, mutane sun mutu

ICPC ta ce ta gano kayan kutsen waya a gidan El-Rufa'i
Malam Nasir El-Rufa'i, tsohon gwamnan Kaduna da ke hannun ICPC Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

Hukumar ta roki kotu ta yi watsi da karar, tana mai cewa binciken da take yi har yanzu bai kammala ba, kuma akwai wasu kayayyaki masu tayar da hankali da aka gano a gidan tsohon gwamnan.

A cewar ICPC, an gudanar da binciken gidan ne a ranar 19 ga watan Fabrairu, 2026 inda aka ce matarsa, Hadiza El-Rufai, da kuma dansa na gidan a lokacin.

Hukumar ta ce ta kwato wasu na’urorin lantarki da takardu, daga ciki har da wasu da ta ce suna da alaka da harkokin tsaro.

Ta kuma yi zargin cewa an gano wasu na’urori da za su iya kutsawa cikin wayoyin hannu a saurari abubuwan da mutum ke tattaunawa.

ICPC ta shaida wa kotu cewa tsohon gwamnan ya ki ba su damar yin binciken fasaha a kan wasu daga cikin na’urorin da aka kwato.

Sai dai iyalan tsohon gwamnan sun karyata dukkannin zarge-zargen da hukumar ta yi, suna zargin cewa ICPC na son amfani da shirun mahaifinsu a matsayin hujjar aikata laifi.

Kara karanta wannan

ICPC: Lauyan El Rufa'i ya yi martani kan 'gano' gidajen tsohon gwamna a kasar Masar

Kotu ta amince da bukatar ICPC

A baya kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja na ci gaba da sauraron shari'ar da ake yi tsakanin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da hukumar ICPC.

A zaman kotun na ranar Alhamis, 12 ga watan Maris 2026, ta amince da wata bukata da hukumar ICPC ta gabatar da zurfafa bincike a kan kayan da aka samo a gidan tsohon gwamnan.

A lokacin da ta ke zartar da hukunci, alkalin kotun, Joyce Abdulmalik ta bayyana cewa ta amince da bukatar ne domin ba hukumar ICPC damar gudanar da bincike.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng