Sarki Sanusi II Ya Yi Shiga Ta Musamman a Kano domin Tunawa da Annabi SAW
- Mai martaba Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya sauya tufafi yayin zaman fada a ranar 20 ga watan Ramadan 1447
- Sanarwar da Legit Hausa ta samu daga masarautar ya nuna cewa Sarki Sanusi II ya yi shigar ne domin tunawa da tarihin Musulunci
- An ce sanya bakin rawani na cikin al'adar Sarkin a ranar 20 ga Ramadan domin tunawa da wata nasarar da Annabi Muhammad SAW ya samu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - A ranar 20 ga watan Ramadan, 2026, mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II ya yi wata shiga ta musamman yayin zaman fada.
Masarautar Kano ta bayyana cewa Sarkin ya saba yin irin shigar duk ranar 20 ga watan Ramadan saboda wani muhimmin abu da ya faru a tarihin Musulunci.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da wani bakin rawani da mai martaba Khalifa Muhammad Sanusi II ya sanya a wani sako da shafin masarautar Kano ya sanya a X.
Me yasa Muhammad Sanusi II sa bakin rawani?
Fadar mai martaba Muhammadu Sanusi II ta sanar da cewa yana sanya bakin rawani ne domin tunawa da nasarar da Annabi Muhammad ya samu ta bude garin Makkah.
Tarihi ya nuna cewa a ranar 20 ga Ramadan Musulmai suka samu nasarar karbar garin Makkah, wanda hakan ke sanya Sarkin shiga ta musamman a irin ranar duk shekara.
Fadar ta wallafa cewa:
"Mai Martaba Sarkin Kano na ci gaba da al’adar sanya rawani baki a ranar 20 ga watan Ramadan domin tunawa da ranar nasarar da aka samu a Makkah, lokacin da Annabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ma ya sanya rawani baki shekaru 1447 da suka gabata."
Tarihin nasarar bude garin Makkah
Shafin Islamic Information ya ce a shekarar 630 Miladiyya (shekara ta 8 bayan Hijira, a cikin watan Ramadan), Musulmai suka hada wata runduna mai karfi kuma mai tsari.
Hakan ya zo ne bayan karya yarjejeniyar Hudaybiyyah, Annabi Muhammad (SAW) ya fara shirye-shiryen tafiya zuwa Makkah. Ya boye shirinsa ga mafi yawan mutane domin a samu nasara cikin gaggawa ba tare da zubar da jini ba.
Annabi Muhammad (SAW) ya tashi daga Madina yana jagorantar rundunar Musulmai kimanin 10,000 — daya daga cikin manyan rundunonin da aka taba hadawa ba a yankin Larabawa a wancan lokaci.

Source: Facebook
Da suka kusanci Makkah, shugabannin Kuraishawa sun fahimci cewa yin yaki ba zai yi amfani ba, sai suka mika wuya. Daga cikin su akwai Abu Sufyan ibn Harb.
Abu Sufyan ya zo sansanin Musulmai inda ya karbi Musulunci kafin rundunar ta shiga Makkah. Annabi (SAW) ya girmama shi ta hanyar sanar da cewa duk wanda ya shiga gidansa zai samu kariya.

Kara karanta wannan
Mojtaba Khamenei: Babban basarake a Najeriya ya tura muhimmin sako ga sabon jagoran Iran
Rundunar Musulmai ta shiga Makkah ta hanyoyi daban-daban, tare da umarni daga Annabi cewa kada su cutar da wadanda ba sa fada, kada su lalata dukiya, kuma kada su fara yaki sai an kai musu hari.
Aminu Ado zai yi hawan sallah a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa zai yi hawan sallah bayan kammala Ramadan 2026.
Legit Hausa ta gano haka ne a cikin wata wasika da Sarkin ya tura wa jami'an tsaro yana sanar da shirye-shiryen da ya tsara zai yi a Kano.
A daya bangaren kuma, har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a samu wani sako game da shirin hawan sallah daga mai martaba Muhammadu Sanusi II ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

