'Yan Bindiga fiye da 40 Sun Mutu yayin da Suka Hana Mutane Sallar Juma'a a Ramadan

'Yan Bindiga fiye da 40 Sun Mutu yayin da Suka Hana Mutane Sallar Juma'a a Ramadan

  • Matsalar tsaro na kara jefa rayuwar mutane cikin hadari a wasu sassan jihar Katsina duk da ana cikin watan azumin Ramadan
  • Rahoto daga yankunan Musawa, Kankara da Malumfashi ya nuna cewa akalla kauyuka 10 ba su samu damar fita sallar Juma'a da ta gabata ba
  • Mazauna yankin sun roki gwamnati da ta kawo masu dauki, suna mai cewa an ci gaba da kai masu hare-hare duk da sulhun da aka yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Mutane sun shiga fargaba a wasu kauyuka a jihar Katsina ranar Juma’a da ta wuce bayan wata mummunar arangama da aka yi tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin 'yan bindigan ya ta tilasta wa al’ummar fiye da kauyuka 10 dakatar da sallar Juma’a a makon da ya gabata a Katsina.

Kara karanta wannan

Iran: An kama matashi a Arewa kan magana game da yakin Amurka da Isra'ila

Taswirar jihar Katsina.
Taswirar jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Premium Times cewa musayar wutar ta faru ne kusa da wasu kauyuka da ke iyaka da kananan hukumomin Musawa, Kankara da Malumfashi, inda aka shafe sa’o’i ana fafatawa.

Halin da mutane ke ciki a yankunan Katsina

Tun da farko, mazauna garin Dangani da ke karamar hukumar Musawa, sun ce ‘yan bindiga da dama sun kai farmaki da rana jim kadan kafin lokacin sallar Juma’a.

Wani mazaunin garin ya ce ‘yan bindigan sun zo ne a kan babura sama da 70, inda suka rika fasa shaguna, kwashe wayoyi daga wuraren caji tare da kwace wayoyi daga hannun jama’a.

Ya ce masu sintiri na sa-kai ba su iya fuskantar su ba saboda yawansu amma dai babu wanda ya rasa ransa a harin, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Arangama tsakanin jagororin ‘yan bindiga

Wani jagoran al’umma ya ce rikicin ya samo asali ne bayan arangama tsakanin shugabannin dabar ‘yan bindiga biyu da ake kira Buzaru da Wada.

Kara karanta wannan

Bidiyon lokacin da makamin Iran ya fada tsakiyar birnin Isra'ila, mutane sun mutu

A cewarsa, rikicin ya barke ne bayan wani bangare ya yi kokarin kwace shanun dayan bangaren. Sun yi artabu a tsakanin kauyukan Garangozai, Gidan Mai Maijimina, Inda suka shafe kusan yini guda suna musayar wuta.

Majiyar ta ce kimanin ‘yan bindiga 49 sun mutu a arangamar, yayin da jami’an tsaro suka kashe hudu tare da kwato shanu sama da 50.

Kauyukan da suka gaza sallar Juma’a

Mazauna yankin sun ce tsananin harbe-harben bindiga ya sa kauyuka da dama ba su gudanar da sallar Juma’a ba saboda tsoron a far masu.

Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Unguwar Yarima, Karachi Yamma, Tsabe, Gidan Lado, Gidan Audu Wasa, Walki, Unguwar Gishiri, Gidan Yan Daudu da sauransu.

Gwamna Dikko Radda.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda Ph.D Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Jama’a na neman daukin gwamnati

Mazauna yankin sun ce halin da ake ciki ya kara jefa jama’a cikin fargaba a yankunan karkara na jihar Katsina.

Wani mutumi da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

“Halin da jama’a ke ciki yanzu yana da matukar muni. Muna kara rokon gwamnati ta dauki matakin dawo da zaman lafiya."

Ya kuma ce duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka taba yi tsakanin wasu ‘yan bindiga da shugabannin al’umma, an ci gaba da kai hare-hare.

Kara karanta wannan

Gbajabiamila da yaran Tinubu da suka rike amana yau ake damawa da su a gwamnati

Sojoji sun kashe 'yan bindiga 45 a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 45 a karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.

Majiyoyin tsaro sun ce farmakin da dakarun sojojin suka kai ya biyo bayan sahihin bayanan sirri da suka nuna ‘yan bindigar na kai hare-hare kan jama'a

Manyan yan bindiga da suka sheka barzahu sun hada da Kachallah Alti, wanda ake cewa dan’uwan jagoran ‘yan bindiga Adamu Alieru ne da Kachallah Damale.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262