Taɓarɓarewar Tsaro: Minista Ya Shiga Ganawar Gaggawa da Shugabannin Tsaro

Taɓarɓarewar Tsaro: Minista Ya Shiga Ganawar Gaggawa da Shugabannin Tsaro

  • Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya kira shugabannin rundunonin tsaro zuwa ganawar gaggawa
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa ana ganawar a birnin Abuja kan hare-haren da suka karu kan sansanonin sojoji a Arewa maso Gabas
  • Shugabannin da suka halarci taron sun hada da hafsan tsaro, Janar Olufemi Oluyede, hafsan sojoji, Laftanar Janar Waidi Shaibu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya kira dukkan shugabannin rundunonin tsaron Najeriya zuwa ofishinsa.

An tabbatar da cewa ana muhimmiyar ganawar a birnin Abuja kan hare-haren yan ta'adda a baya-bayan nan.

Ministan tsaro yana ganawar sirri da shugabannin rundunar sojoji
Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Shugabannin tsaro sun yi ganawar gaggawa

Daily Trust ta ce taron na gudana ne a hedikwatar ma’aikatar tsaro da ke Abuja, inda shugabannin rundunar tsaro suka hakarta.

Daga cikin shugabannin akwai hafsan tsaro, Janar Olufemi Oluyede da hafsan sojoji, Laftanar Janar Waidi Shaibu.

Kara karanta wannan

Ana shirin daukar matasa 28,000 aiki, Tinubu ya kara albashin sojojin Najeriya

Sauran mahalarta sun hada da shugaban rundunar sama, Air Marshal Sunday Aneke, shugaban rundunar ruwa, Vice Admiral Idi Abass da wakilan hukumar leken asiri ta kasa.

Yadda aka kashe manyan kwamandojin sojoji

Rahotanni sun ce ‘yan ta’adda sun kashe kwamandoji uku masu mukamin Laftanar Kanar a Borno, tare da kashe sojoji da dama da kuma sace fararen hula.

Da yake magana kafin taron ya koma na sirri, ministan tsaro ya ce za su sake duba sabbin dabarun yaki da ‘yan ta’adda duk da cewa sojoji sun yi asara.

Ya ce:

“Mun san cewa mun yi wasu asarori, amma yawanci sun fi shafar ‘yan ta’adda."

- Cewar tsohon janar

Ministan tsaro ya gargadi sojoji game da yaki da ta'addanci
Ministan tsaro a Najeriya, Christopher Musa. Hoto: Defence Headquarters Nigeria.
Source: Facebook

Martanin Christopher Musa bayan taron

Bayan kammala taron, Christopher Musa, ya ce ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga suna shan asara fiye da sojoji, yayin da dakarun ke kara kaimi a hare-hare a fadin kasar.

Ya ce an kira taron ne domin nazarin dabarun soji da ake amfani da su a wuraren da ake gudanar da ayyukan yaki daban-daban a fadin kasar, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Hadimin Kakakin majalisa ya rasu awanni bayan an sha ruwa da shi a Ramadan

Ya ce:

“Mun yi wani gajeren taro da shugabannin rundunonin tsaro domin sake duba dabarunmu a dukkan wuraren da muke gudanar da ayyuka a cikin kasar.
“Mun san halin da ake ciki a kasa, amma ina so in tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa dakarun soji na aiki tukuru domin tabbatar da cewa Najeriya ta zama kasa mai aminci da tsaro.”

Musa ya bukaci ‘yan Najeriya kada su yarda da bayanan karya da ake yadawa a kafafen sada zumunta, yana mai cewa irin wadannan bayanai na iya rage wa sojoji kwarin gwiwa.

Tinubu ya kara albashin sojojin Najeriya

An ji cewa shugaba Bola Tinubu ya amince da karin albashi ga dakarun sojojin Najeriya da kuma alawus na musamman ga jami'an dake gadin Aso Rock.

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan an samu rahoton cewa Tinubu ya amince a dauki sababbin sojoji 28,000 don karfafa tsaro a fadin Najeriya.

Rundunar sojin Najeriya za ta tura jirage masu saukar ungulu zuwa jihar Benuwai domin taimakawa a wajen fatattakar 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.