Gwamna Ya Tsige Shugaban Ma’aikatan Jihar Kano, an Nada Mace a Mukamin
- Gwamna Abba Yusuf ya tsige shugaban ma'aikatan jihar Kano Abdullahi Musa inda ya nada Hajiya Bilkisu Maimota a matsayin shugabar rikon kwarya
- Wannan mataki na daga cikin kokarin sake fasalin aikin gwamnati bayan sauyin shekar gwamnan daga jam'iyyar NNPP zuwa APC a jihar
- Gwamnan ya gode wa tsohon shugaban ma'aikatan bisa kokarinsa sannan ya bukaci ya mika ragamar ofishin ga Hajiya Bilkisu a yau Laraba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tsige shugaban ma’aikatan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Musa, daga muƙaminsa.
Sanarwar korar tasa, na kunshe ne a cikin sanarwar da babban mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a daren jiya Talata.

Source: Twitter
Gwamna ya tsige shugaban ma'aikatan Kano
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa korar shugaban ma'aikatan ta fara aiki ne nan take.
Wannan na zuwa ne a matsayin ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin jihar na sake fasalin aikin gwamnati domin samar da ƙwarewa, ladabi, da inganta yadda ake gudanar da ayyuka a hukumomin gwamnati.
Gwamnan ya bayyana cewa akwai buƙatar ganin an samu sabon jini da zai tafi daidai da burin gwamnatin na kawo sauyi a rayuwar al'ummar jihar Kano.
Gwamna Abba Yusuf ya gode wa Alhaji Abdullahi Musa bisa gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake kan muƙamin, yana mai yi masa fatan alheri a ayyukansa na gaba.
An nada shugabar ma'aikata ta rikon kwarya
Domin tabbatar da cewa babu giɓi a harkar gudanarwa, gwamnan ya bayar da umarnin maye gurbin Alhaji Abdullahi da babbar sakatariya mai kula da ayyukan gidaje da gudanarwa a ofishin sakataren gwamnati, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota.
Hajiya Bilkisu Maimota za ta rike mukamin shugabar ma'aikatan Kano a matsayin riƙon ƙwarya har zuwa lokacin da za a nada sabon shugaba.
Wannan naɗi na Hajiya Bilkisu ya nuna amincewar da gwamnan ke da shi ga mata wajen riƙe manyan muƙaman gudanarwa a jihar, in ji rahoton Punch.

Source: Twitter
Sauye-sauye a gwamnatin jihar Kano
Gwamnan ya umarci Abdullahi Musa da ya tabbatar ya miƙa dukkan takardun ofishinsa ga Hajiya Bilkisu kafin ƙarshen yau Laraba, 11 ga Maris, 2026.
Wannan sauyi na zuwa ne a daidai lokacin da jihar Kano ke fuskantar sauye-sauye a fagen siyasa da shugabanci, musamman bayan ficewar Gwamna Abba Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC.
Masu lura da al'amuran yau da kullum sun lura cewa tsige shugaban ma’aikata na ɗaya daga cikin jerin sauye-sauyen da za a ci gaba da gani a gwamnatin jihar Kano.
Gwamna Abba ya kori wasu hadiminsa
A wani labari, mun ruwaito cewa, siyasar Kano na ci gaba da daukar zafi bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP zuwa APC.
Gwamna Abba ya sallami mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Sanusi Surajo Kwankwaso daga mukaminsa, kuma ya maye gurbinsa nan take.
Wannan mataki na zuwa ne sa'o'i 24 bayan Sanusi ya saki wani faifan bidiyo da ke nuna cewa ya yi murabus daga mukaminsa a gwamnatin jihar Kano.
Asali: Legit.ng

