ICPC Ta Samu Damar Kara Garkame El Rufa'i na Kwanaki 14, Akwai Yiwuwar Ya Yi Sallah a Tsare

ICPC Ta Samu Damar Kara Garkame El Rufa'i na Kwanaki 14, Akwai Yiwuwar Ya Yi Sallah a Tsare

  • Kotu ta sahalewa hukumar ICPC ta ci gaba da tsare tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a binciken da ta ke masa
  • ICPC na zargin El-Rufa'i da almundahana yayin da ta garkame shi na sama da kwanaki 20 bayan ya fito daga ofishin EFCC
  • Tuni lauyansa ya garzaya kotu yana neman a soke sabon umarnin da hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta'annati ta samu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja –Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta samu sabon umarni daga kotu wanda ya ba ta damar ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai.

A wannan umarni da ta samu, ana da damar ci gaba da rike Nasir El-Rufa'i har na tsawon ƙarin kwanaki 14 a ofishinta.

Kara karanta wannan

ICPC: Lauyan El Rufa'i ya yi martani kan 'gano' gidajen tsohon gwamna a kasar Masar

ICPC za ta ci gaba da tsare tsohon gwamna
Nasir El-Rufa'i a wata ganawa yayin da ya ke gwamna Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

The Nation ta wallafa cewa an ba da wannan umarni ne domin bai wa hukumar damar kammala binciken da take yi kan zarge-zargen da ake yi masa.

Zargin da ICPC ke yi wa El-Rufa'i

Zarge-zargen da ICPC ke yi wa tsohon gwamnan sun haɗa da halasta kuɗin haram da kuma zargin amfani da mukami ba bisa ƙa’ida ba.

Rahotanni sun nuna cewa binciken da ake yi kan tsohon gwamnan ya faɗaɗa fiye da yadda aka fara.

Kotun Majistare da ke Bwari ce ta bayar da wannan sabon umarni a ranar Alhamis, 5 ga watan Maris, 2026 kuma an yi zaman ne a gaban lauyan El-Rufai.

El-Rufai na fuskantar tuhume-tuhumen almundahana
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

Wannan sabon umarni zai ƙare ne a ranar 19 ga Maris, 2026, lokacin da ake sa ran ICPC za ta gabatar da rahoton abin da ta cimma. A cikin rubutaccen umarnin kotu, alƙalin kotun majistare, Okechukwu John Akweke, ya amince da bukatar lauyan ICPC, Dr. Osuobeni Ekoi Akponimisingha.

Kara karanta wannan

ICPC ta gano wasu gidajen alfarma da ake zargin El Rufai ya mallaka a ƙasar waje

Lauyan ya roƙi kotu ta ba hukumar damar tsare El-Rufai na wani lokaci domin ci gaba da bincike.

Kotu ta amince da bukatar ICPC

Kotun ta ce an amince da bukatar kamar yadda aka gabatar, inda ta umarci ICPC ta sake tsare tsohon gwamnan na ƙarin kwanaki 14 har sai an kammala binciken. Rahotanni sun bayyana cewa hukumar ba za ta iya tsare wani mutum ba sai da sahihin umarnin kotu

Ta hannun lauyansa, Ukpong Esop Akpan, tsohon gwamnan ya shigar da sabuwar buƙata a kotu yana cewa kotun majistare ta wuce iyakarta wajen bayar da umarnin tsare shi. A cikin takardar rantsuwa mai sakin layi 20 da Mohammed Salihu Shaba ya gabatar, an bayyana cewa El-Rufai ya ba shi izini ya gabatar da takardar a madadinsa. Takardar ta ce umarnin tsarewar da kotu ta bayar tun a ranar 19 ga Fabrairu, 2026 yana da matsaloli na shari’a kuma bai kamata ya ci gaba da aiki ba. Saboda haka lauyan tsohon gwamnan ya buƙaci kotu ta soke wannan umarni gaba ɗaya, yana mai cewa ba ya da ingancin doka. Yanzu dai ana jiran ranar 17 ga Maris, 2026 domin kotu ta yanke hukunci kan ko za ta soke sabon umarnin tsarewar ko kuma za ta bar shi ya ci gaba da aiki har sai ICPC ta kammala bincike.

Kara karanta wannan

Dalilin gidan gyaran hali na cigaba da tsare Abba Kyari duk da hukuncin kotu

Lauyan El-Rufa'i ya soki ICPC

A baya mun wallafa cewa Ubong Esop Akpan, lauyan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya zargi ICPC da yin abin da ya kira tsangwamar siyasa.

Ya ce rahotannin da ke cewa El-Rufai na da kadarorin biliyoyin Naira a Masar magana ce kawai da zummar ci gaba da rike shi ba tare da wani sahihin dalili ba.

Lauyan ya ce tsare 'dan siyasar sama da kwanaki 20 ba tare da tuhuma ba ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya tare da neman a sako wanda ya ke wakilta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng