Najeriya Ta Kai wa Mutanenta da Suka Makale a Yaƙin Ƙasar Iran Agaji

Najeriya Ta Kai wa Mutanenta da Suka Makale a Yaƙin Ƙasar Iran Agaji

  • Gwamnatin Tarayya ta fara fitar da ‘yan Najeriya da suke son barin ƙasar Iran sakamakon rikicin da ke ƙaruwa a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Jami’an ofishin jakadancin Najeriya a Tehran na jagorantar su zuwa kan iyakar Armenia domin tsallakawa ba tare da ko kwarzane ba
  • Shugabar hukumar 'yan Najeriya a ketare, Abike Dabiri-Erewa, ta ce har yanzu babu wani ɗan Najeriya da rikicin ya shafa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara shirin fitar da ‘yan Najeriya da suke son barin Iran yayin da yakin Gabas ta Tsakiya ke tsananta.

Hukumar kula da yan Najeriya da ke kasashen waje ta sanar da cewa ana raka mutanen zuwa kan iyakar Armenia domin tabbatar da tsaron lafiyarsu.

Kara karanta wannan

Iran/Isra'ila: Bama bamai sun hana 'yan Najeriya sakat, ana kokarin tsamo su

Najeriya ta fara fitar da yan kasarta daga Iran
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa Shugabar hukumar NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa, ce ta tabbatar da haka a ranar Talata, 10 ga watan Maris, 2026.

An fara kwaso 'yan Najeriya a Iran

Premium Times ta ruwaito Dabiri-Erewa ta bayyana cewa jami’an ofishin jakadancin Najeriya da ke Tehran suna aiki tare domin shirya fitar da duk wani ɗan Najeriya da yake son barin ƙasar.

A cewarta, jami’an diflomasiyyar Najeriya ne ke jagorantar su zuwa kan iyaka domin su tsallaka zuwa Armenia cikin aminci.

Ta ƙara da cewa jami’an jakadancin na ci gaba da kasancewa a kan iyakar domin karɓar ‘yan Najeriya da suke son barin ƙasar, tare da taimaka masu wajen tsallakawa cikin sauƙi.

Ana ci gaba da yaki a gabas ta Tsakiya
Shugaban kasar Iran, Masoud Pazeshkian Hoto: Getty
Source: Twitter

A cikin saƙon nata, ta ce:

“Ana rakiyar ‘yan Najeriya da suka amince su bar Iran zuwa kan iyakar Armenia ta hannun jami’an ofishin jakadancin Najeriya domin tsallakawa cikin aminci."

Ta kuma tabbatar da cewa zuwa yanzu babu wani ɗan Najeriya da rikicin ya shafa ta kowace fuska.

Kara karanta wannan

Kasar Muslunci ta Iran ta nuna sha'awar taimakawa Najeriya wajen yaki da ta’addanci

Rikicin Iran, Amurka da Isra'ila na tsananta

Wannan mataki na gwamnatin Najeriya ya biyo bayan ƙara tsanantar rikicin da ya fara a ranar 28 ga watan Fabrairu.

Rikicin ya ɓarke ne bayan hare-haren soji da aka kai wa Iran da haɗin gwiwar Amurka da Isra'ila, har aka kashe jagoran addinin kasar, Ayatollah Khamenei.

Bayan hare-haren, Iran ta mayar da martani da harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa zuwa wasu sassan yankin.

Saboda wannan yanayi, ƙasashe da dama suna sa ido kan lafiyar ‘yan kasarsu da ke zaune a yankunan da rikicin ya shafa.

Najeriya ma ta ɗauki wannan mataki na fitar da ‘yan kasarta da suke son barin Iran domin kare rayukansu.

Makaman Iran sun jikkata Sojojin Isra'ila

A wani labari, kun ji cewa ana cigaba da samun bayanai game da illar da Iran ta yi wa Amurka/Isra'ila a yakin da aka shafe sama da kwana 10 ana yi a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Iran/Isra'ila: Matakan da gwamnatin Tinubu ke dauka kan 'yar Najeriya da suka makale

Hare-haren da kasar Iran ta kai kasashen da Amurka ke da sansanonin soji ya kashe sojoji da raunata sama da 100 a cikin dakarun Washington da ke taya yakin.

Tuni aka mayar da gawar wasu daga cikin sojojin Amurka zuwa gida daga Gabas ta Tsakiya, inda shugaba Donald Trump ya karbi wasu daga cikinsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng