Ana Wata ga Wata: ASUU Ta Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani, Ta Fadi Dalili

Ana Wata ga Wata: ASUU Ta Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani, Ta Fadi Dalili

  • Malaman jami'ar UNILAG sun sanar da fara yajin aiki daga gobe Laraba sakamakon rage musu albashin watannin Janairu da Fabrairu na 2026
  • Kungiyar ASUU ta siffanta shugabannin jami'ar a matsayin azzalumai wadanda suka biya 'gurgun albashi' da kuma rike alawus din mambobinsu
  • Yajin aikin zai ci gaba da gudana a jami'ar har sai hukumar gudanarwar makarantar ta biya cikakken albashin malaman da suke binta bashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legas - Ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) reshen jami’ar jihar Legas (UNILAG), ta sanar da tsunduma cikin yajin aikin sai-baba-ta-gani.

ASUU-UNILAG ta dauki wannan mataki ne sakamakon abin da ta kira "biyan mambobinta gurgun albashi" da jami’ar ta yi a watannin Janairu da Fabrairu na shekarar 2026.

Kungiya ASUU reshen jami'ar Legas sun tsunduma yajin aiki
Motoci na fitowa ta babbar kofar shiga jami'ar Legas, UNILAG. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

ASUU ta tsunduma yajin aiki

Matakin ya fito ne cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Idou Kehinde, da sakatarenta, Adesina Arikawe, suka sanya wa hannu bayan taron gaggawa da suka gudanar yau Talata, in ji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Wasu mutane sun dasa bam a fitaccen masallaci a Borno? Gaskiya ta fito

Ƙungiyar ta bayyana cewa yajin aikin zai fara aiki ne daga gobe Laraba, 11 ga Maris, 2026, kuma mambobinta za su janye ayyukansu har sai jami'ar ta biya su cikakken albashinsu na watanni biyu da suka gabata.

ASUU ta bayyana cewa wannan mataki ya zama dole bayan dogon nazari kan yadda aka zaftare musu albashi ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba, lamarin da ya saba wa ƙa'idar aiki.

"Zalunci ne da rashin tausayi" – Inji ASUU

A cewar ƙungiyar, jami'ar ta zabtare albashin mambobinta dake Akoka, kuma ba ta ba su alawus ɗin EAA a watan Janairu ba, yayin da waɗanda ke Idi-Araba aka hana su alawus na EAA da CATA.

Ƙungiyar ta siffanta wannan mataki na rage albashin watan Fabrairu a matsayin "zalunci, rashin tausayi, da kuma aikin shaidan," inda ta ce hakan ya saba wa mutuncin ma'aikata.

ASUU ta ce ba za su koma koyarwa a jami'ar ba har sai an biya su cikakken albashinsu.
Dalibai na fitowa daga cikin jami'ar Legas, UNILAG. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Sanarwar ta ƙara da cewa:

"(i) Mun yi watsi da wannan mataki baki ɗaya wanda ya kai ga zabatre albashin mambobinmu a Janairu da Fabrairu 2026 saɓanin yadda abokan aikinmu a sauran jami'o'in gwamnatin tarayya suka samu."
"(ii) Mun janye ayyukanmu daga Laraba, 11 ga Maris, 2026, tunda jami'ar ta kasa biyan albashinmu baki ɗaya zuwa ranar 9 ga Maris."

Kara karanta wannan

ICPC ta gano wasu gidajen alfarma da ake zargin El Rufai ya mallaka a ƙasar waje

Kungiyar malaman jami'o'in ta jaddada cewa muddin ba a biya ragowar kuɗaɗen mambobinta ba, to ba za ta koma aji ba.

ASUU ta janye yajin aiki a jami'o'i

A wani labari, mun ruwaito cewa, kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa, ASUU, ta sanar da dakatar da yajin aikin gargadi na makonni biyu da ta shiga a fadin Najeriya.

Wannan mataki na zuwa ne bayan tattaunawa da gwamnatin tarayya da majalisar dokoki ta ƙasa kan cika wasu daga cikin bukatun ƙungiyar.

ASUU ta dakatar da yajin aikin ne saboda sahihin shirin da kwamitin Yayale Ahmed da kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa suka fara don warware matsalolin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com