Magana Ta Girma: Amurka Ta Hararo Barazanar kai Mata Farmaki a Najeriya
- Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da gargadi game da zargin cewa ana barazanar kai hari kan wasu kadarorin kasar
- A makon da ya wuce ofishin ya dakatar da aiki a Najeriya biyo bayan fargabar barkewar zanga-zanga a wasu sassa daban-daban
- Amurka ta yi gargadi ne bayan kai hare-hare kan kadarorinta a kasashe da dama a dalilin yakin da ya barke tsakaninta da Iran
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya gargadi cewa akwai yiwuwar barazanar ta’addanci da yiwuwar kai hari kan kadarorisa a kasar nan..
Hakan na zuwa ne yayin da Amurka ke cigaba da fuskantar kalubale game da yakin da ta fara da Iran a karshen watan Fabrairun 2026.

Source: Getty Images
A wata sanarwar tsaro da ofishin jakadancin ya fitar ta shafinsa na yanar gizo a ranar Litinin, ya ce an fitar da gargadi ne domin sanar da ’yan kasar Amurka da ke Najeriya.

Kara karanta wannan
Ana rade radin kafa sansanin sojin Amurka a Najeriya, dakarun kasar sun yi bayani
Gargadin Amurka a Najeriya
Amurka ta gargadi 'yan kasarta game da yiwuwar kai hari, tare da shawartar su da su kara daukar matakan kariya idan za su je ofisoshin Amurka da cibiyoyin da ke da alaka da ita.
Sanarwar ta bukaci ’yan kasar su kara sanya ido da taka-tsantsan yayin da suke tafiya zuwa ofisoshin Amurka da ke Abuja da Legas, da kuma makarantu masu alaka da kasar.
“Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja yana sanar da ’yan kasar game da yiwuwar barazanar ta’addanci kan kadarorin Amurka da kuma makarantu masu alaka da Amurka a Najeriya.
Sanarwar ta ce:
“Ofishin jakadancin yana ba da shawarar cewa ’yan kasar Amurka su kara daukar matakan kariya idan za su je ofishinsa a Abuja da Legas, da kuma makarantu masu alaka da Amurka, ciki har da sauya lokutan tafiya da hanyoyin da suke bi,”
Ofishin jakadancin ya kuma shawarci ’yan kasar Amurka da su rika sauya lokutan tafiyarsu da hanyoyin da suke bi, su guji yin abubuwan da ake iya hasashe, kuma su tabbatar wayoyinsu na hannu suna da caji idan wani lamari na gaggawa ya taso.

Kara karanta wannan
Najeriya ta shiga jerin kasashe 3 da za su samu alheri sakamakon yakin Iran da Amurka

Source: Facebook
Karin matakan kariya daga Amurka
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa Amurka ta bukaci 'yan kasar su rika sauya hanya a yayin da suke zirga-zirga a Abuja da Legas.
Cikin dabarun da aka ba Amurkawan da ke Najeriya har da yadda za su rika shammatar jama'a.
“Ku rika lura da abin da ke faruwa, ku kasance masu takaita shiga jama'a, ku kara matakan tsaro, ku sauya hanyoyin da kuke bi a kai a kai.
'Yan Shi'a sun yi zanga-zanga
A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan Shi'a sun yi zanga-zanga a jihohin Najeriya bayan kashe jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Zanga-zangar ta shafi jihohin Kano, Bauchi, Lagos, Yobe da sauransu, inda suka rika Allah wadai da matakan da Amurka da Isra'ila suka dauka kan Iran.
A ranar 28 ga Fabrairun 2026 ne Amurka da Isra'ila suka hada kai suka kashe jagoran addinin Iran bayan kai jerin hare-hare gidansa a Tehran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng