Yakin Iran da Amurka Ya Kara Taba Dangote, Ya Canza Farashin Fetur Karo na 3 a Najeriya

Yakin Iran da Amurka Ya Kara Taba Dangote, Ya Canza Farashin Fetur Karo na 3 a Najeriya

  • A karo na uku cikin mako guda, matatar Dangote ta kara farashin litar man fetur a wuraren da take ba yan kasuwa sari a Najeriya
  • Wannan kari da ake yawan samu a bayan bayan nan na da nasaba da yakin Iran da Amurka/Isra'ila, wanda ya jawo tashin danyen mai a duniya
  • Kungiyar PETROAN ta yi hasashen cewa idan ba a dakatar da wannan yaki ba, farashin fetur zai iya kai wa N2,000 a Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Matatar mai ta Dangote da ke jihar Legas ta sake kara farashin kowace litar fetur (PMS) a rumbunan ajiya da take bai wa 'yan kasuwa sari a fadin Najeriya.

Matatar Dangote ta kara farashin kowace lita daga N995 zuwa N1,175, lamarin da ake ganin yana da alaka da tashin gangar danyen mai a kasuwannin duniya.

Kara karanta wannan

Fetur ya kara tsada: Yadda yakin Iran ya jawo farashin gangar mai ya haura $100

Dangote.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote a wani taron kasuwanci a Amurka Hoto: Dangote Group
Source: Getty Images

Sabon karin farashin shi ne karo na uku da aka yi a cikin kwanaki bakwai da suka gabata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro.

Rahotanni sun ce an sanar da ‘yan kasuwar mai da masu rumbunan ajiya na mai karin da aka yi a ranar Litinin, 9 ga watan Maris, 2026.

An kara N180 a farashin fetur cikin kwanaki 3

Karin da aka yi na N180 kan kowace lita ya nuna an samu karuwar kashi 18.1 cikin kwanaki uku kacal, lamarin da ya tayar da hankalin ‘yan kasuwa da masu amfani da mai kan yiwuwar samun kari a gidajen mai a fadin Nigeria.

Masana harkar man fetur sun ce wannan karin zai iya kara tsadar sufuri da kuma kayan masarufi, wanda zai kara wa al’umma nauyi a daidai lokacin da ake fama da hauhawar farashi.

Matatar Dangote ta kara farashin dizal

Haka kuma, matatar hamshakin dan kasuwar ta kara farashin dizal (AGO) zuwa kusan N1,620 kan kowace lita.

Kara karanta wannan

Iran ta gamu da gagarumar matsala tana tsakiyar musayar wuta da Amurka/Isra'ila

Wannan karin farashin na zuwa ne a daidai lokacin da kasuwar danyen mai ta duniya ta fara shiga halin rashin tabbas, inda farashin danyen mai ya karu sakamakon rikicin yakin Iran, Amurka da Isra'ila.

Man fetur.
Yadda ake zuba fetur a gidajen mai a Najeriya Hoto: Bloomberg
Source: Getty Images

Rahotanni sun nuna cewa farashin gangar danyen mai ya tashi zuwa $104.4 daga $92.69 da yake a jiya Lahadi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A gefe guda kuma, kungiyar masu gidajen man fetur ta kaaa (PETROAN) ta yi gargadin cewa farashin litar fetur na iya kai wa N2,000, yayin da dizal kuma zai iya kaiwa kusan N3,000 idan yakin Gabas ta Tsakiya ya ci gaba.

Matatar Dangote ta kulla yarjejeniya

A wani rahoton, kun ji cewa matatar Dangote ta kammala yarjejeniya da manyan kamfanonin mai 12 domin rarraba litar fetur miliyan 60 zuwa 65 a kowace rana a fadin Najeriya.

Ana sa ran wannan mataki zai taimaka wajen daidaita wadatar mai tare da karfafa dogaro da kai a bangaren makamashi a kasar nan.

Aliko Dangote ya ce tsarin zai tabbatar da samun fetur a ko ina cikin Najeriya, tare da ba wa matatar damar fitar da rarar da ta wuce bukatar ƴan ƙasa zuwa kasashen ketare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262