Tashin Hankali: Boko Haram Ta Kwace Gari Guda a Borno, an Ji Halin da Ake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
- Mayakan Boko Haram sun mamaye tare da kafa daula a Ngoshe inda suka sace mata da yara sama da 100 bayan kashe sojoji da limamin gari
- 'Yan ta'addan sun canza sunan garin Ngoshe zuwa Daula Islamia tare da yin barazanar kai hare-hare har zuwa birnin Maiduguri da Abuja
- A gefe guda, rundunar sojin Najeriya ta yi amfani da jiragen yaki inda ta kashe yan ta'adda 50 wadanda suka kai hari sansanin sojojin Ngoshe
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Borno - Fiye da kwanaki biyar bayan wani mummunan hari, mayakan Boko Haram na ci gaba da zama masu iko da garin Ngoshe dake ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa ƴan ta'addan sun sace mata da yara fiye da 100, sannan sun kashe sojoji da dama, ciki har da babban limamin garin da wasu dattawa jim kaɗan bayan buɗa baki a ranar Laraba.

Source: Getty Images
Yadda Boko Haram ta kwace garin Ngoshe
Wannan lamari ya jefa tsoro da fargaba a zukatan mazauna yankin dake maƙwabtaka da Ngoshe, musamman a garin Pulka inda ƴan gudun hijira ke neman mafaka, a cewar rahoton Daily Trust.
Ƴan ta'addan sun fara kai hari ne a sansanin soji na bataliyar 82 Division Task Force kafin su karkata ga fararen hula da sansanin ƴan gudun hijira.
Wani soja da ya tsira daga harin ya bayyana yadda ya ga ƴan ta'addan suna yanka abokan aikinsa kamar kaji bayan sun fi ƙarfin sojojin sakamakon yawansu da kuma miyagun makamai.
Sojan da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:
"Mun yi faɗa sosai, amma sun fi mu yawa da makamai. Ina kallo suna fille kan abokan aiki na, sannan suka ƙona motocin yaƙinmu kafin mu gudu cikin daji."
Iƙirarin kafa daula da canza sunan gari
Sai dai rundunar sojin Najeriya ta mayar da martani ta hanyar amfani da jiragen yaƙi, inda ta gano inda ƴan ta'addan suke ta kashe fiye da 50 daga cikinsu yayin da suke ƙoƙarin tserewa.
A cikin wani faifan bidiyo da yake yawo a intanet, wasu matasa biyar, 'yan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunna lidda’awati wal-Jihad ƙarƙashin jagorancin Imam Abu Umaima, sun yi iƙirarin cewa sun mamaye garin Ngoshe tare da canza sunansa zuwa "Daula Islamia".
Shugaban ƙungiyar, wanda ya yi magana da harshen Hausa a cikin babban masallacin garin, ya bugi kirji kan yadda suka sace mata da yara a matsayin "ganimar yaƙi" wadda ya ce addini ya halatta musu.

Source: Original
Sojoji na shirin wani gagarumin farmaki
Wannan jagora ya ƙara da cewa suna nan daram a cikin garin kuma suna shirin yin sallar raga-raga (Eid al-Fitr) a cikin Ngoshe, in ji wani rahoto na jaridar The Guardian.
Ya yi barazanar cewa za su ci gaba da kaddamar da hare-hare daga Ngoshe har zuwa birnin Maiduguri, har ma su kai ga birnin Abuja.
Duk da wannan iƙirari na ƴan ta'addan, majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa rundunar soji na nan tana shirya wani gagarumin farmaki na ƙasa da na sama domin ƙwato garin da kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa da su nan ba da jimawa ba yau.
An birne sojojin da aka kashe a Borno

Kara karanta wannan
Bakin hayaki ya turnuke Tehran, Amurka ta yi wa Iran mummunar barna a karon farko
A wani labari, mun ruwaito cewa, Rundunar sojin Najeriya ta yi jana’izar sojojin da suka rasu yayin fafatawa da ‘yan ta’addan Boko Haram a Jihar Borno.
An birne sojojin ne a makabartar sojoji ta Maimalari Cantonment da ke Maiduguri yayin da jama'a ke cike da jimamin rashin daka yi.
Shugabannin soji da gwamnatin Borno sun yi magana kan jarumtakar sojojin tare da ba wa iyalansu hakurin wannan lamari mai daga hankali.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

