Jirgin Sama Dauke da Sanata da Manyan Kusoshin APC 2 Ya Gamu da Matsala bayan Baro Abuja
- Sanatan Taraba ta Kudu, David Jimkuta da wasu jiga-jigan APC sun tsallake rijiya da baya da suka bi wani jirgin sama a Abuja
- Rahoto ya nuna cewa jirgin ya yi gaggawar komawa Abuja jim kadan bayan tashinsa sakamakon wata matsalar fasaha
- Sanata Jimkuta ya tabbatar da cewa duka wadanda suke cikin jirgin saman sun sauka lafiya, ya kuma gode wa Allah da ya cece su
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Wani jirgin sama mai zaman kansa da ke dauke da sanata mai wakiltar Taraba ta Kudu, David Jimkuta, ya samu matsala bayan ya lula sararin samaniya.
Rahotanni sun bayyana cewa jirgin saman da sanatan ke ciki ya samu matsalar fasaha jim kadan bayan tashinsa, lamarin da ya tilasta masa komawa filim jirgin sama a Abuja.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta tattaro cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar yayin da sanatan ke kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman Kashimbila da ke jihar Taraba daga Abuja
A wata sanarwa da ofishin sanatan ya fitar, an bayyana cewa Jimkuta na kan hanyarsa ta zuwa garuruwan Takum da kuma Wukari domin halartar wasu muhimman taruka, lokacin da lamarin ya auku.
Dalilin da ya sa Sanatan zai je Takum
Sanatan zai halarci taron 2026 Zion Conference da za a gudanar a Takum, sannan kuma zai kai ziyarar ta’aziyya zuwa Cocin Katolika ta Wukari bayan gobarar da ta tashi a kwanan nan
Sanarwar ta ce jirgin ya tashi daga Abuja ne bayan wani dan jinkiri da aka samu sakamakon yanayin iska mara kyau.
Sai dai kusan mintuna shida bayan tashin jirgin, wata ƙararrawa ta tashi, inda matukin jirgin ya sanar da fasinjoji cewa an samu wata tangardar fasaha.
Jirgin ya yi gaggawar komawa Abuja
Nan take bayan tabbatar da akwai matsala matukin jirgin ya juya ya mayar da jirgin zuwa Abuja bisa ka’idojin tsaron jiragen sama.
“Da nuna kwarewa da bin ka’idojin tsaro na jiragen sama, matukin jirgin ya dawo da jirgin zuwa Abuja inda ya sauka lafiya,” in ji sanarwar.
Manyan jiga-jigan da ke cikin jirgin
Daga cikin wadanda ke cikin jirgin akwai shugaban cocin Christian Reformed ta Najeriya, Magaji Jirape, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Taraba, Istifanus Gbana da shugaban matasan APC, Adi Shekarau Masa-Ibi.
Sanarwar ta tabbatar da cewa dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin sun dawo Abuja cikin koshin lafiya, inda Sanata Jimkuta ya gode wa Allah da ya tsare rayuwarsu bayan wannan lamari.
Jirgin sama ya yi hatsari a jihar Imo
A wani rahoton, kun ji cewa wani karamin jirgin sama kirar Cessna 172 ya gamu da hatsari a filin jirgin Owerri bayan ya taso daga jihar Kaduna.
An ce jirgin ya yi hatsari ne a filin jirgin kasa da kasa na Sam Mbakwe da ke Owerri, jihar Imo , yayin da yake kokarin sauka bayan ya samu wata tangarda tun a sararin samaniya.
Hukumar NSIB ta tabbatar da cewa jami’an ceto sun isa wurin hatsarin cikin gaggawa bayan faruwar lamarin, domin kai dauki.
Asali: Legit.ng


