Ana Jita Jitar Kwankwaso zai Kara Aure, Hadiminsa Ya Fitar da Sabon Bayani

Ana Jita Jitar Kwankwaso zai Kara Aure, Hadiminsa Ya Fitar da Sabon Bayani

  • Tsohon dan takarar Shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya musanta jita-jitar cewa zai ƙara aure a karshen watan Maris
  • Katunan gayyatar aure da ake zargin na sa ne sun bazu a shafukan sada zumunta, suna cewa zai auri Hajiya Rabi’atu Idris Labari
  • Mai magana da yawun Sanata Kwankwaso, Saifullahi Hassan, ya bayyana gaskiyar lamari game da shirin angwancewar tsohon gwamnan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fito ya musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa yana shirin ƙara aure nan ba da jimawa ba.

An samu rahotannin da ke ikirarin cewa tsohon gwamnan jihar Kano zai angwance da wata mata mai suna Hajiya Rabi’atu Idris Labari a ranar 29 ga watan Maris 2026 a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ana tsaka da yaki da Iran, 'dan Majalisar Amurka ya dauko batun Najeriya

Ana yada rade-radin cewa Kwankwaso zai kara aure
Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Daily Nigerian ta wallafa cewa a cewar jita-jitar, har ma an riga an buga katunan gayyatar aure kala biyu da ake yadawa a intanet.

Ana rade-radin Rabiu Kwankwaso zai kara aure

Mai taimaka wa Kwankwaso a harkar sadarwa ta zamani, Saifullahi Hassan, ya wallafa a shafin Facebook cewa wannan labari ƙarya ce da aka kirkira ba tare da wata hujja ba.

Saifullahi Hassan ya bayyana cewa gaba daya labarin ba shi da tushe, saboda haka ya bukaci jama’a da su yi watsi da jita-jitar.

Kwankwaso ya karyata cewa zai kara aure
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon dan takarar Shugaban kasa Hoto; Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Ya rubuta cewa:

"Zance ne mara tushe. A guji yada karya jama’a."

Bayan wannan martani, al’amarin ya ci gaba da jan hankalin masu bibiyar siyasar Najeriya, musamman magoya bayan Kwankwaso da sauran masu amfani da kafafen sada zumunta.

Martanin jama’a ga labarin auren Kwankwaso

Bayan karyata labarin, mutane da dama sun shiga dandalin sada zumunta suna bayyana ra’ayoyinsu kan jita-jitar.

Kara karanta wannan

Iran ta yi wa Trump martani daga Najeriya kan maye gurbin Ayatollah Khamenei

Wani mai suna Ibrahim Bello ya ce:

"To meye laifi dan zai aure sai dai kawai yanayin gayyar ne ya saba hankali. Oga ba zai yi gayyatar aurensa haka ba"

Shi kuwa Abdulrahman B. Lawan ya rubuta cewa:

"Allah ya kara kare mutunchin Injiniya Dr Rabiu Musa Kwankwaso."

Haka kuma wani mai suna Auwal Sunusi ya ce:

"Ya ma za a daura aure ranar Sallah. Ai Jagora shi da aure sai idan ba ran Uwarmu Hjy Salamatu."

Alamar tambaya a labarin auren Kwankwaso

Rabiu Kwankwaso yana aure gidan Alhaji Sule Garo kuma kusan ba a jin labari game da abin ya shafi iyalinsa, ya raba harkokin cikin gida da na siyasa.

A cewar masu yada wannan labarin da bai tabbata ba, za a daura auren ne ranar 20 ga watan Maris 2026 wanda ake hasashen zai fado ranar karamar sallah.

Haka zalika Legit Hausa ta lura a katin, an sa karfe 9:30 na safiya a kuma masallacin idin Sarki a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Dalilin gidan gyaran hali na cigaba da tsare Abba Kyari duk da hukuncin kotu

Kwankwaso ya samu kariyar NNPP

A baya, kun samu labarin cewa jam’iyyar NNPP ta rubuta wa Majalisar Dokokin Amurka wasika game da zargin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na da hannu a uzzura wa Kiristoci.

Jam'iyyar hamayya ta NNPP ta yi hakan ne domin kare ɗan takararta na shugaban ƙasa a 2023, Rabiu Musa Kwankwaso bayan zargin da Amurka ke yi masa Shugaban na hannu a muzgunawa Kiristoci.

Jam'iyyar ta ƙara da cewa NNPP ta yi mamakin dalilin da ya sa aka ware Kwankwaso aka saka shi cikin jerin waɗanda ake zargi da tallafa wa ta’addanci inda ake kashe jama'a a kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng