Hadimin Kakakin Majalisa Ya Rasu Awanni bayan an Sha Ruwa da Shi a Ramadan

Hadimin Kakakin Majalisa Ya Rasu Awanni bayan an Sha Ruwa da Shi a Ramadan

  • Kakakin majalisar tarayya, Tajudeen Abbas ya bayyana jimaminsa kan rasuwar mataimakinsa wanda ya rasu yana da shekara 54
  • Marigayin ya kasance tare da Abbas da sauran abokan aiki wajen buda baki na watan Ramadan a daren Juma’a, sa’o’i kadan kafin rasuwarsa
  • Abbas ya ce Nnamdi ya bar tarihi na sadaukarwa, hidima da jajircewa ga aiki kafin mutuwarsa a jiya Asabar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Tajudeen Abbas, ya bayyana matukar alhininsa kan rasuwar Mataimakin Shugaban Ma’aikatansa a Majalisa.

Shugaban majalisar ya tura sakon ta'aziyyabayan rasuwar Dunkwu Chamberlain Nnamdi, wanda ya rasu a safiyar ranar Asabar yana da shekaru 54.

Hadimin Tajudeen Abbas ya riga mu gidan gaskiya
Shugaban majalisar, Hon. Tajudeen Abbas da marigayi hadiminsa, Dunkwu Chamberlain Nnamdi. Hoto: Musa Abdullahi Krishi.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Musa Abdullahi Krishi wanda ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

"Kada a dagula siyasar Kano": NNPP ta aika sako kan shirin tsige Mataimakin gwamna

Hadimin kakakin majalisar tarayya ta bar duniya

An ce marigayin ya kasance cikin koshin lafiya sa’o’i kadan kafin rasuwarsa, domin ya halarci buda baki na watan Ramadan tare da Abbas da sauran abokan aiki a daren Juma’a.

Nnamdi, dan asalin Uteh Okpu da ke karamar hukumar Ika ta Arewa maso Gabas a jihar Delta State, zai cika shekaru 55 a ranar 21 ga watan Maris, 2026.

Ya ce marigayin ba kawai mataimaki ba ne a gare shi, har ila yau abokin aiki ne mai aminci da jajircewa wanda ya yi hidima da kwarewa har zuwa karshen rayuwarsa

Abbas ya ce:

“Cikin jimami nake jajanta rasuwar Mataimakin Shugaban Ma’aikatana (Majalisa), Dakta Dunkwu Chamberlain Nnamdi, wanda ya rasu a safiyar ranar Asabar, 7 ga Maris, 2026.
“Dakta Chamberlain mutum ne mai kuzari, kuma sa’o’i kadan kafin rasuwarsa ya kasance tare da ni da sauran abokan aiki wajen buda baki na Ramadan a daren Juma’a."

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar tsohon ministan Tinubu ya yake shi, yana kus kus da kusoshin adawa

Majalisar dokoki ta yi babban rashi a Abuja
Kakakin majalisar tarayya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas. Hoto: House of Representatives.
Source: Facebook

Yabon da marigayin ya samu bayan mutuwarsa

Shugaban majalisar ya kuma bayyana cewa marigayin ya bar tarihi na sadaukarwa, jajircewa da hidima ga al’umma.

Har ila yau, Abbas ya ziyarci iyalan marigayin domin jajanta musu tare da rarrashin matar sa da ‘ya’yansa.

Ya ce:

“Ya nuna jijircewa da sadaukarwa, aiki tukuru, Za mu yi kewarsa matuka. Tunanina da addu’o’ina suna tare da iyalansa a wannan lokaci mai wahala.
“Duk abin da yake da farko yana da karshe. Ku daure. Abin ya girgiza mu sosai, amma ba za mu iya tambayar hukuncin Allah ba.”

An nada Nnamdi a matsayin Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Majalisar (bangaren majalisa) a watan Yuni na shekarar 2023.

A baya ya taba zama mai ba shugaban majalisar shawara kan harkokin ‘yan majalisa a majalisar ta tara, sannan daga baya ya zama shugaban ma’aikata ga Femi Gbajabiamila.

Jigon APC ya mutu awa 24 bayan samun mukami

Kara karanta wannan

Malamai sun yi magana, sun fadi yadda yakin Iran da Amurka ya shafi Najeriya

Mun ba ku labarin cewa jam'iyyar APC reshen jihar Legas ta tabbatar da rasuwar mataimakin sakataren yada labaranta, Karamo Yesiro bayan zabensa a karo na biyu.

Mai magana da yawun APC ta jihar Legas, Seye Oladejo ya bayyana cewa rasuwar Yesiru babban rashi ne ga jam'iyyar mai mulki tun a 2014.

APC reshen Legas ta kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalansa, abokan siyasa da magoya bayansa, tana mai addu’ar Allah Ya ba su hakuri da juriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.