Iran/Isra’ila: Matakan da Gwamnatin Tinubu ke Dauka kan ’Yar Najeriya da Suka Makale
- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi magana game da matakan da take dauka kan yakin da ke faruwa tsakanin kasar Iran da Isra'ila
- Gwamnatin ta bayyana cewa tana yin haka ne domin kare ‘yan Najeriya da ke Gabas ta Tsakiya sakamakon rikicin da ake yi a yau
- Ma’aikatar harkokin waje ta ce jakadun Najeriya a ƙasashen yankin an saka su cikin shiri na musamman domin sa ido kan halin da ake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana matakan da take ɗauka domin kare ‘yan Najeriya da ke zaune a yankin Gabas ta Tsakiya.
Hakan ya biyo bayan rikicin da ya ƙara tsananta a yankin yankin Gabas ta Tsakiya da ya shafe mako daya.

Source: Facebook
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ma'aikatar ta wallafa a Facebook.
Yakin Iran/Isra'ila: Matakan da Najeriya ke dauka
Ebienfa ya ce gwamnati ta buɗe hanyoyin diflomasiyya da kuma tsarin gargadi na ofisoshin jakadanci domin tabbatar da tsaron ‘yan Najeriya da ke yankunan.
Jami'in ya ce manufar harkokin wajen Najeriya ta ta’allaka ne kan tattaunawa, warware rikice-rikice cikin lumana da kuma mutunta dokokin ƙasa da ƙasa.
Ya ƙara da cewa Najeriya ta dade tana kira ga dukkan ɓangarorin da ke rikicin su yi haƙuri tare da rungumar hanyoyin diflomasiyya domin rage tashin hankali.
Ebienfa ya ce ofisoshin jakadancin na lura da yadda abubuwa ke gudana tare da ba da taimako ga ‘yan Najeriya da ke zaune a waɗannan ƙasashe.
A cewarsa, dubban ‘yan Najeriya na aiki a yankin Gulf a fannoni kamar gine-gine, lafiya, sufurin jiragen sama, mai da gas da kuma aikin gida.
Sai dai ya ce har yanzu babu rahotannin da suka tabbatar da cewa wani ɗan Najeriya ya samu matsala kai tsaye sakamakon tashin hankalin.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Majalisar Dinkin Duniya ta hango abin da zai faru sakamakon yakin Amurka da Iran
Ya bayyana cewa Iran na daga cikin wuraren da ake ganin ‘yan Najeriya suka fi fuskantar haɗari a halin yanzu saboda tsananin rikicin.

Source: Facebook
Yawan 'yan Najeriya da ke kasar Iran
Ebienfa ya ce akwai kusan ‘yan Najeriya 1,000 a Iran, inda mafi yawansu ɗalibai ne da ke karatu a jami’o’in ƙasar.
Ya ce jakadancin Najeriya na tattaunawa da ƙasar Armenia domin duba yadda za a iya fitar da ‘yan Najeriya daga Iran cikin sauƙi.
Ebienfa ya ce ma’aikatar harkokin waje tana da tsarin gaggawa domin kula da matsalolin da suka shafi ‘yan Najeriya a lokacin rikice-rikicen ƙasa da ƙasa.
Wannan tsarin ya haɗa da shirye-shiryen fitar da jama’a daga wuraren haɗari, haɗin gwiwa da gwamnatocin ƙasashen da ake ciki da kuma hukumomin duniya.
Gwamnati ta shawarci ‘yan Najeriya da ke yankin Gulf su kasance cikin shiri, su bi umarnin tsaro na hukumomin ƙasashen da suke zaune.
Iran ta sha alwashin kare 'yan Najeriya
An ji cewa Jakadan Iran a Najeriya, Mahdavi Raja, ya yi magana kan halin da yan kasar ke ciki yayin da ake yaki tsakaninta da Isra'ila.
Raja ya tabbatar da cewa ‘yan Najeriya da ke zaune a Iran suna cikin koshin lafiya duk da rikicin Amurka, Isra’ila da Iran.
Ya ce babu wani rahoton cutarwa ga ‘yan Najeriya da ke birane kamar Tehran da Qom, yana bayanin matakan tsaro da aka dauka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

