Malamin Musulunci Ya Fadi Abin da Zai Faru da Isra’ila bayan Kashe Khamenei

Malamin Musulunci Ya Fadi Abin da Zai Faru da Isra’ila bayan Kashe Khamenei

  • Wani malamin addini, Sheikh Habibullah Adam, ya tsoma baki game da rikicin da ke tsakanin Iran da Israel a Gabas ta Tsakiya
  • Malamin addini ya yi hasashen cewa yakin Iran da Isra'ila na iya rikidewa zuwa yakin duniya na uku duba da yanayin rikicin
  • Sheikh Habibullah ya ce kashe jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, da Amurka da Isra’ila suka yi na iya jawo manyan kasashe su shiga rikicin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Agege, Lagos - Wani malamin addinin Musulunci, Sheikh Habibullah Adam, ya yi magana game da yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila.

Malamin ya yi gargadin cewa rikicin Gabas ta Tsakiya na iya rikidewa zuwa yakin duniya na uku duba da hanyar da aka dauko kan rikicin.

Malamin Musulunci ya yi hasashen makomar Isra'ila bayan kashe Khamenei
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, Sheikh Habibullah Adam da marigayi Ali Khamenei. Hoto: @Fuadoluwadamil, @netanyahu, @khamenei_ir.
Source: Twitter

Malamin Musulunci a Lagos ya bayyana haka ne yayin tafsirin Alkur'ani da yake yi a Ramadan wanda ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Majalisar Dinkin Duniya ta hango abin da zai faru sakamakon yakin Amurka da Iran

Yadda yaki ya barke tsakanin Iran da Isra'ia

Ya bayyana hakan ne bayan harin hadin gwiwa da Amurka da Isra'ia suka kai wanda ya yi sanadin kashe jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Bayan kisan Khamenei, sojojin Iran sun fara harba makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuka zuwa Isra’ila da wasu kasashen yankin Gulf.

Daga cikin kasashen da aka ce hare-haren suka nufa akwai Saudi Arabia, Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar da Kuwait inda Amurka ke da sansanonin soja.

A daya bangaren kuma, Isra'ila na ci gaba da kai hare-haren bama-bamai kan Iran da kawayenta a yankin.

An fadi kasashen da za su taya Iran

Malamin ya ce Musulmi a duniya ya kamata su gane cewa mabiya Shi’a ma Musulmi ne kuma dole a dauke su a matsayin ‘yan’uwa.

Ya kara da cewa manyan kasashe irin su China, Russia da Korea ta Arewa na sa ido sosai kan rikicin da ke faruwa inda ya yi hasashen Isra'ila za ta samu nakasa da asara.

Kara karanta wannan

Iran ta faɗi halin da ƴan Najeriya ke ciki a kasar yayin da ake ci gaba da ɓarin wuta

A cewarsa, akwai yiwuwar wadannan kasashe su dauki bangare idan rikicin ya kara tsananta a Gabas ta Tsakiya.

Malamin ya kuma yi nuni da wasu hasashen tarihi da suka yi gargadin yiwuwar barkewar babban rikici a duniya a shekarar 2026.

A cikin hudubar da ya gabatar da harshen Yarbanci, Sheikh Habibullah ya ambaci wani hadisin Annabi Muhammad (SAW) wanda ke cewa kafin karshen duniya, za a zo wani lokaci da Musulmi za su yaki Yahudawa, kuma ba za su samu wurin buya ba.

Iran ta illata Amurka a Jordan

Mun ba ku labarin cewa wasu majiyoyi sun ce Iran ta lalata wata na’ura mai kare makamai mallakin Amurka mai darajar miliyoyin daloli a wani sansanin soja a Jordan.

Masana tsaro sun ce lalata cibiyar THAAD zai iya barin gibin sa ido kan makamai masu linzami a yankin Gulf, lamarin da ka iya shafar tsarin kariya.

Hotunan tauraron dan adam sun nuna an lalata radar AN/TPY-2 a sansanin Muwaffaq Salti, abin da masana ke cewa na daga cikin manyan hare-haren Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.