Ana Wata ga Wata: An Kai Korafin Kasar Iran gaban Majalisar Dinkin Duniya
- Qatar ta tura wasiku biyu zuwa Majalisar Dinkin Duniya kan hare-haren da Iran ta kai kasarta musamman wurin da fararen hula ke zaune
- Wakiliyar Qatar a Majalisar Dinkin Duniya ce ta mika wasikun, wadanda ke kunshe da korafin kasarta kan rikicin da ya barke tsakanin Iran, Amurka da Isra'ila
- Ta yi ikirarin cewa Iran ta harba makamai masu linzami 83 da jirage marasa matuƙi 12 zuwa Qatar a ranar Asabar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Qatar - Ƙasar Qatar ta kai korafi Majalisar Dinkin Duniya kan hare-haren da Iran ke kaiwa yankinta tun bayan barkewar yaki tsakaninta da Amurka da Isra'ila.
Qatar ta yi kakkausar suka kan hare-haren da Iran ta kai yankinta da kuma wasu ƙasashen Tekun Fasha, tana mai cewa hakan tashin hankali ne da ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar yankin.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Majalisar Dinkin Duniya ta hango abin da zai faru sakamakon yakin Amurka da Iran

Source: Getty Images
Qatar ta kai korafin Iran Majalisar Dinkin Duniya
Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa hakan na kunshe a cikin wasiƙu biyu da Qatar ta aika wa Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, da kuma shugaban kwamitin tsaro na Majalisar.
Wakiliyar Qatar a Majalisar Ɗinkin Duniya, Sheikha Alia Ahmed bin Saif Al Thani, ta bayyana cewa ƙasarta na da haƙƙin mayar da martani kan hare-haren da Iran ke kai wa.
Yadda Iran ta yi barin wuta a Qatar
A cewarta, Iran ta harba makamai masu linzami 83 da jirage marasa matuƙi 12 zuwa Qatar a ranar Asabar, bayan hare-haren da Amurka da Israel suka kai, wanda ya yi sanadin mutuwar jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Ta ce Qatar ta samu nasarar kakkabo makamai masu linzami 81 da jirage marasa matuƙi 11, amma wasu biyu daga cikin makaman sun tsallake kariya inda suka bugi sansanin sojin sama na Al Udeid, inda sojojin Amurka ke zaune.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Ana tsaka da yaki da Iran, 'dan Majalisar Amurka ya dauko batun Najeriya
Har ila yau, wani jirgi mara matuƙi ya lalata wani tsarin kariya na Qatar amma duk da haka, rahotanni sun ce ba a samu asarar rayuka ba sakamakon hare-haren.
Wakiliyar Qatar ta ce wasu daga cikin makaman da aka kakkabo sun biyo ta kan yankunan da mutane ke zaune, ciki har da wuraren kasuwanci da gidajen zama kamar unguwar West Bay da Barwa City.
Ta ƙara da cewa zuwa safiyar ranar Lahadi, 1 ga Maris, Qatar ta gano makamai masu linzami 92 da jirage marasa matuƙi 17 a sararin samaniya, cewar rahoton NBC News.

Source: Getty Images
Bukatar dakatar da rikicin Gabas ta tsakiya
Qatar ta kuma sake kira da a dakatar da duk wani mataki da zai iya kara tsananta rikici, tare da komawa kan tattaunawa da diflomasiyya domin shawo kan rikicin.
Sanarwar ta jaddada buƙatar yin amfani da hankali da hikima, domin kare tsaron yankin da kuma hana rikicin ya rikide zuwa babban yaki a Gabas ta Tsakiya.
Qatar ta yi watsi da bayanan Iran
A wani rahoton, kun ji cewa Qatar da Iran sun tashi baram-baram yayin wata tattaunawa ta wayar tarho kan rikicin da ya barke a Gabas ta Tsakiya.
Kasar Qatar ta yi watsi da duka bayanin da Iran ta yi game da hare- haren makamai masu linzami da aka kai kasarta kwanan nan.
Qatar ta jaddada cewa hujjojin da ta tattara sun nuna cewa hare-haren sun shafi yankunan da fararen hula ke zaune da kuma muhimman ababen more rayuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
