Akwai Matsala: Kasar Qatar Ta Samu Sabani da Iran a Yakin da Ya Barke da Amurka da Isra'ila

Akwai Matsala: Kasar Qatar Ta Samu Sabani da Iran a Yakin da Ya Barke da Amurka da Isra'ila

  • Qatar da Iran sun tashi baram-baram yayin wata tattaunawa ta wayar tarho kan hare-haren da ake kai wa bayan fara yaki a Gabas ta Tsakiya
  • Iran ta shaida wa Firaministan Qatar cewa tana kai hare-hare kan sansanonin Amurka ne kadai, amma ba ta da niyyar cutar da kasar
  • Sai dai kasar Larabawar ba ta gamsu da duka bayanan ba, inda ta ce hujjojin da ta tattara sun nuna Iran na kai hari kan fararen hula

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Qatar - Duk da tattaunawar da kasashen suka yi, Qatar da Iran ba su fahimci juna ba kan wasu hare-hare da Jamhuriyar Musulunci ta kai bayan barkewar rikici a Gabas ta Tsakiya.

Kasar Qatar ta yi watsi da duka bayanin da Iran ta yi game da hare-haren makamai masu linzami da aka kai kasarta kwanan nan.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta farmaki wani jirgin yaki, ta kara yi wa Amurka da Isra'ila babbar illa

Abbas Araghchi.
Ministan harkokin waje na kasar Iran, Abbas Araghchi Hoto: KARIM JAAFAR
Source: Getty Images

Kasar Qatar ta yi sabani da Iran

Tribune Nigeria ta tattaro cewa Qatar ta jaddada cewa hujjojin da ta tattara sun nuna cewa hare-haren sun shafi yankunan da fararen hula ke zaune da kuma muhimman ababen more rayuwa.

Wannan matsayar ta fito ne yayin wata tattaunawa da aka yi ta wayar tarho tsakanin Firaministan Qatar kuma Ministan Harkokin Waje, Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi.

Wakilan kasashen biyu sun tattauna ta wayar tarho ne a daidai lokacin da takun-saka ke kara ruruwa a Gabas Ta Tsakiya.

Rahoto ya bayyana cewa Ministan cewa kasarsa ta kai hare-haren ne domin maida martani ga Amurka, amma ba su da niyyar cutar da Qatar.

Abin da Qatar ta fadawa Ministan Iran

Sai dai, Al Thani ya yi watsi da wannan bayanin, inda ya ce hujjojin da mahukuntan Qatar ke da su sun nuna cewa makaman da Iran ta harbo sun fada kan yankunan fararenbhula.

Kara karanta wannan

Yaki na kara zafi, Trump ya ja da baya, ya ki tura sojoji Iran

Al Thani ya ce wasu daga cikin wuraren da makaman suka fada suna kusa da Filin Jirgin Sama na Hamad, wanda shi ne babbar cibiyar zirga-zirgar jiragen sama ta kasar.

Ya kuma yi gargadin cewa hare-haren sun jefa masana'antu da wuraren samar da iskar gas (LNG) cikin hadari, bangaren da ke taka muhimmiyar rawa a tattalin arziki da kuma samar da makamashi ga duniya.

Qatar da Iran.
Firaministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani da Ministan Harkokin Wajen Uran, Abbas Araghchi Hoto: Karim Jaafar
Source: Getty Images
"Wannan babban cin mutunci ne ga yancin Qatar na cin gashin kanta, kuma ya saba wa dokokin kasa da kasa. Ba za mu taba amincewa da ayyukan da ke jefa rayukan mutane cikin hadari ba,” in ji Firaministan.

Duk da cewa Qatar ta sake jaddada kudurinta na wanzar da zaman lafiya ta hanyar diflomasiyya, Al-Thani ya jaddada cewa kowace irin barazana ga iyakokin kasarsa za a dauke ta da matukar muhimmanci, cewar tashar Al-Jazeera.

Trump ya yi maganar jagoran addinin Iran

A wanu rahoton, kun ji cewa Shugaba Donald Trump na neman a sanya shi a cikin wadanda za su zabi sabon jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Wannan na zuwa ne yayin da Iran ke ci gaba da shirye-shiryen nada sabon jagora bayan kashe Ayatollah Ali Khamenei a hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra'ila.

Shugaba Trump ya ce Iran na “ɓata lokacinta” idan ta yi ƙoƙarin naɗa sabon jagora ba tare da sa hannun kasar Amurka ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262