Martanin Malaman Addini 5 game da Yaƙin Iran da Isra’ila a Gabas Ta Tsakiya
Yakin da ake ci gaba da yi tsakanin Iran da Isra'ila na daukar hankalin mutanen duniya gaba daya musamman kan zafafan hare-hare da ke jawo rasa rayuka a yankin Gabas ta Tsakiya.
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Ana ci gaba da kazamin fada tsakanin Iran da Isra'ila wacce ke samun goyon bayan Amurka karkashin jagorancin Donald Trump.
Yakin ya yi sanadiyyar rasa rayukan al'umma ciki har jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei da wasu manyan jami'an tsaro.

Source: Facebook
Malaman da suka yi magana kan rikicin Iran/Isra'ila
Hukumomi a kasar Iran sun tabbatar da mutuwar Khamenei a harin ranar Asabar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 da ake ciki, cewar Al Jazeera.
Manyan malaman addinin Musulunci da kuma na Kirista sun yi martani kan ci gaba da yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.
Legit Hausa ta duba wasu daga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu kan lamarin bayan barkewar yaki.
1. Fafaroma Robert Francis Leo XIV
Shugaban darikar katolika, Fafaroma Leo ya bayyana damuwa game da yakin da ya barke a yankin Gabas ta Tsakiya a wannan lokaci.
Fafaroma ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X inda ya bukaci a zauna kan teburin sulhu domin neman mafiya.
Ya ce zaman lafiya da kwanciyar hankali ba sa samuwa ta hanyar barazanar juna ko amfani da makamai da ke haifar da barna, wahala da mutuwa, sai dai ta hanyar tattaunawa cikin hankali da gaskiya.

Source: Getty Images
2. Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana kan kisan jagoran addinin kasar Iran, Imam Ayatollah Ali Khamenei.
Babban malamin addinin ya bayyana Khamenei a matsayin mai sa'a, wanda ya rasu wajen kare mutanen da ake zalunta.
Sheikh Gumi ya ce mutuwar Khamenei ta faru ne a abin da ya kira jihadi kan masu kashe kananan yara da mata a Gaza wanda hakan zalunci ne.

Kara karanta wannan
Bayan rantsar da shi, shugaban 'yan sandan Najeriya ya tabo batun yakin Iran da Amurka
“Mutum ne mai sa'a, ya mutu a jihadi kan masu kashe kananan yara da mata marasa laifi a Gaza da sauran wurare.”

Source: Facebook
3. Fasto Elijah Babatunde Ayodele
An gargadi Amurka da Isra'ila cewa watakila ba za su yi nasara a yakin da suke yi da Iran ba, bayan kisan Jagoran addinin Iran, Ali Khamenei.
Fitaccen limamin coci a Najeriya ya ce Amurka da Isra'ila ba za su yi nasara a yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya ba, wadanda suka fara farmakar Iran.
Ya ce Amurka ba za ta ci nasara a wannan yaki ba kuma Shugaba Donald Trump ba zai cimma burinsa ba kamar yadda ya yi a kan Venezuela.

Source: Facebook
4. Sheikh Abdullahi Bala Lau
Shugaban kungiyar Izala ta JIBWIS, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bukaci limamai su tsayar da addu’ar Al-Kunuti a fadin kasar baki daya.
Bala Lau ya ce mafi yawan wadanda rikice-rikicen ke shafa Musulmi ne da ba su da laifi, yana mai nuna alhini kan salwantar rayuka musamman a yakin Iran da Isra'ila.
Malamin ya roki Allah SWT ya kawo karshen zubar da jini tare da dawo da zaman lafiya a duniya da Najeriya baki daya.

Source: Facebook
5. Dr. Bashir Aliyu Umar
Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Dr. Bashir Aliyu Umar ya bayyana damuwa kan rigimar da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.
Shehin ya bayyana haka ne a yayin tafsirinsa wanda aka wallafa a shafinsa na Facebook inda ya zargi makircin da ake shiryawa.
Ya ce:
"Barnar da suka shirya ba ta tsaya kan Iran kadai ba, sun fuskanci kasashen Musulmi, suna son ruguza karfin da Musulmi suke da shi, bayan Iran sai kuma Pakistan da kasar Turkiyya."
Malamin ya nuna damuwa kan harin Isra'ila a Iran wanda ya yi sanadiyyar Ali Khamenei inda ya yi addu'ar Ubangiji ya kare Musulunci da Musulmi.

Source: Facebook
6. Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemu
Babban malamin Musulunci a Najeriya, Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi maganganu game da yakin da Iran ke yi da Amurka da Isra'ila.
A wajen tafsirin Ramadan a garin Bauchi, Shehin malamin ya nuna takaici game da yadda harin Amurka da Isra'ila ya jawo ana kai hari kasashen Larabawa.
Farfesa Rijiyar Lemu ya koka game da yadda Iran ta ke kai hari makwabta da sunan tarwatsa sansanonin Amurka, yana mai tsoron hakan ya kara matsala a yankin.
AU ta yi magana kan rikicin Iran da Isra'ila
A baya, mun ba ku labarin cewa kungiyar AU ta fitar da sanarwa cewa hare-haren soji da kuma martanin da Iran ta mayar ma nuni da ƙarin tsananta rikici mai hatsari da matuƙar tayar da hankali.
Ƙungiyar ta ce lamarin da ke tsananta a Gabas ta Tsakiya na barazanar jefa yankin gaba ɗaya cikin wani yanayi na tashin hankali da zai gagari kundila.
Ta kuma buƙaci dukkanin ɓangarorin da su mutunta dokokin ƙasa da ƙasa da kuma yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya domin kare zaman lafiya da tsaro na duniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


