Iran Ta Yi wa Trump Martani daga Najeriya kan Maye Gurbin Ayatollah Khamenei

Iran Ta Yi wa Trump Martani daga Najeriya kan Maye Gurbin Ayatollah Khamenei

  • Gwamnatin Iran ta yi wa shugaba Donald Trump martani game da cewa zai saka baki a kan batun zaben sabon jagoran addini na kasar
  • Jakadan Iran a Najeriya, Gholamreza Ahdavi Raja ne ya yi magana game da batun a wani taron manema labarai a birnin tarayya Abuja
  • Donald Trump ya fara magana kan tsarin shugabanci a Iran ne a daidai lokacin da aka fara rade-radin wanda zai gaji Ayatollah Ali Khamenei

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT , Abuja - Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Najeriya, Gholamreza Ahdavi Raja, ya soki kalaman shugaban Amurka, Donald Trump kan tsarin shugabanci a kasar sa.

Trump ya nuna cewa zai shiga cikin masu tantance wanda zai jagoranci Iran bayan rasuwar jagoran ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka kashe a harin da aka kai ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Yaki na kara zafi, Trump ya ja da baya, ya ki tura sojoji Iran

Gholamreza Ahdavi Raja
Jakadan Iran a Najeriya, Gholamreza Ahdavi Raja. Hoto: Hope Uzodimma
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Jakadan Iran ya jaddada cewa ba za su amince da wani tasiri daga waje cikin harkokin cikin gida ba.

Martanin Iran ga Trump daga Najeriya

Raja ya ce Iran za ta yanke shawara da kanta kan shugabancinta da makomar siyasar ƙasar ba tare da tsoma bakin wata ƙasa daga waje ba.

“Amurka kullum tana ƙoƙarin tsoma baki cikin al’amuran cikin gidanmu. Mu ƙasa ce mai cin gashin kanta. Ba za mu bari Amurka ta tsoma baki cikin harkokinmu na cikin gida ba,”

- Inji Trump.

Maganar da Trump ya yi kan Iran

Kalaman Gholamreza Ahdavi Raja sun biyo bayan furucin Trump bayan tabbatar da mutuwar Ayatollah Ali Khamenei a harin da Amurka/Isra'ila suka kai.

A wata ganawa da ya yi da Firaministan Jamus Friedrich Merz a Fadar White House, Trump ya ce jerin hare-haren Amurka da Isra’ila sun kashe wasu mutane da yake ganin an shirya su domin karɓar manyan mukamai a Iran.

Kara karanta wannan

Lissafi zai kwabewa Trump, mayakan Kurdawa sun ki taya shi yaki da Iran

“Yawancin mutanen da muka so su gaje shi sun mutu. Abin ba zai yi kyau ba a ce wanda ya fi shi muni ya karbi mulkin kasar bayan mun kashe shi."
Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump a wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Haka zalika, wata hira da ya yi, Trump ya ce dole ne ya shiga cikin masu zaɓen sabon jagoran Iran:

“Dole ne na shiga cikinsu, kamar yadda aka yi da Delcy a Venezuela,”

Da yake mayar da martani ga Trump, PM News ta ce jakadan ya yi watsi da batun, yana mai jaddada cewa al’ummar Iran ne za su yanke hukunci kan shugabancin ƙasarsu.

Trump ba zai tura soji Iran ba

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa ba zai tura sojojin kasa zuwa Iran ba a yakin da suke yi.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin da aka masa tambaya a kan matakin da zai dauka domin ganin ya samu nasara a kan Tehran.

Trump ya ce ba zai tura sojoji ba saboda yana ganin ya samu nasarar da ya ke nema, ya ce sun riga sun lalata wasu makaman Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng