Malamai Sun Nuna Kishi, Sun Goyi bayan 'Dan APC domin Samun Musulmin Gwamna
- Kungiyoyin Musulmi da na malamai a Osun sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar APC yayin da ake shirin zaben gwamna
- Shugaban kungiyar, Sheikh Qozeem Abdul Rahaman, ya ce Musulmi su mara wa Bola Tinubu baya tare da zaben Musulmi a matsayin gwamna domin ci gaba da manufofin gwamnati
- Dan takarar ya ce ba zai dogara da karfin gwamnatin tarayya ba domin lashe zaben Osun, yana mai kira ga jama'a su karbi katin zabe
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Masu ruwa da tsaki da kungiyar malaman Musulunci a Osun sun tabbatar da goyon baya ga APC.
Ƙungiyar malaman ta bayyana goyon baya ga dan takarar APC, Asiwaju Bola Oyebamiji da mataimakinsa Benjamin Adereti.

Source: Original
Osun: Musulmi sun bi bayan dan takarar APC
Sun bayyana hakan ne a wani taron Ramadan inda suka raba kayan abinci ga mabiya addini tare da kira ga jama'a su goyi bayan gwamnatin Bola Tinubu, cewar The Nation.
Shugaban kungiyar Musulmin, Sheikh Qozeem Abdul Rahaman, ya ce ya dace Musulmi su mayar da alherin da aka nuna musu ta hanyar mara wa Tinubu baya.
Ya kuma ce a duk jihohin Kudancin Najeriya 17 babu gwamnan Musulmi a yankin Kudu maso Yamma, yana cewa wannan lamari abin damuwa ne.
Malaman Musulunci sun goyi bayan Bola Tinubu
Sheikh Abdul Rahaman ya ce dole Musulmi su hada kai domin zaben gwamna Musulmi wanda zai taimaka wajen dorewar shirye-shiryen da gwamnatin Tinubu ta fara.
Malamin da ya gabatar da lacca, Farfesa Kamaldeen Busari, ya ce Oyebamiji ba musulmin bogi ba ne, kuma cikakken Musulmi ne mai sadaukarwa.
Ya kara da cewa zai zama abin takaici idan al'ummar Osun suka rasa wannan dama ta zabar Oyebamiji wanda ya bayyana a matsayin jagoran Musulmi nagari.

Source: Instagram
Martanin dan takarar APC a zaben Osun
Da yake mayar da martani, Oyebamiji ya ce ba zai dogara da karfin gwamnatin tarayya ba wajen lashe zaben gwamnan Osun na shekarar 2026.
Ya ce jam'iyyar APC ta riga ta tuntubi dukkan kananan hukumomi 30 da ofishin yankuna tare da sarakunan gargajiya da mata da maza, cewar ThisDay.
Oyebamiji ya ce za su ci gaba da aiki tukuru domin samun damar zama gwamnan Osun, yana jaddada cewa dole su nuna kyakkyawan hali ga jama'a.
Ya kuma roki masu kada kuri'a su tabbatar sun karbi katin zabe na dindindin kafin lokacin zaben gwamna da za a gudanar a watan Agustan shekarar 2026 da muke ciki.
Kwara: Ana neman sauya gwamna da Kirista
Kun ji cewa Kungiyar Kwara Inclusion Advocates (KIA) ta sake kiran a samu gwamna Kirista a Kwara domin samar da adalci.
Ta ce tsarin mulki ya daɗe yana fifita bangare ɗaya wanda ke nuna rashin daidaito inda ta yi kiran samar da adalci gaba daya.
Kungiyar ta ja kunnen ‘yan siyasa su guji siyasar raba kawuna, tana cewa zaben 2027 zai nuna ko Kwara za ta rungumi adalci ko siyasar yaudara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

