An Nemi Na'ibin Liman da Wasu Mazauna Katsina an Rasa bayan Hare Haren Yan Ta'adda

An Nemi Na'ibin Liman da Wasu Mazauna Katsina an Rasa bayan Hare Haren Yan Ta'adda

  • An sake samun hare-haren ‘yan bindiga a Kankara duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattaba wa hannu kafin Ramadan
  • 'Yan ta'addan sun kai hare-hare biyu a cikin dare guda, inda aka fara kai harin farko da 12.00 na tsakar dare tare da kashe mutum daya
  • An kai hari na biyu ana sallar Asubahi, lamarin da ya jefa jama'a a cikin firgici bayan an kwashe wasu daga cikinsu zuwa dawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Duk da cewa an riga an cimma wata yarjejeniya tsakanin shugabannin al’umma da ‘yan bindiga a Kankara da ke jihar Katsina kafin Ramadan, sun kara afka wa jama'a.

Rahotanni sun bayyana cewa an sake samun hare-haren ‘yan bindiga a daren Juma'a 6 ga watan Maris, 2026 da kuma sallar Asubahi.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun sace daruruwan mutane bayan kai hari a Borno

An kai wasu munanan hare-hare Kankara a Katsina
Taswirar jihar Katsina da ke fama da hare-hare Hoto: Legit.ng
Source: Original

Bakatsine ya wallafa a shafinsa na X cewa wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa harin farko ya auku ne da 12.00 na tsakar dare.

'Yan ta'adda sun kai hari Katsina

Rahoton ya wallafa cewa an kai harin yankin Gangaren Mangwarori, garin Kankara, inda ‘yan bindiga suka kai hari suka kashe Malam Surajo.

Bayan hallaka dattijon, sun sace wata tsohuwa mai suna Gwamma. Wannan lamari ya tada hankalin mazauna unguwar, wadanda ke nuna damuwa da rashin tsaro a yankin.

A wani hari daban da ya faru da 6.00 na safe, ‘yan bindigan sun kai farmaki a unguwar Marabar Gurbi, wadda shi ma ke cikin karamar hukumar Kankara.

An tattaro cewa wasu mazauna unguwar sun bace, daga ciki har da Malam Jamilu, Na’ibin masallacin Marabar Gurbi, wanda ya tafi masallaci domin sallar Asubahi bayan sahur lokacin da harin ya afku.

Yadda jama'a ke cikin fargaba a Katsina

Hare-haren sun jefa al’umma cikin fargaba da rashin kwanciyar hankali, musamman ma ganin cewa an yi yarjejeniya ta zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar tsohon ministan Tinubu ya yake shi, yana kus kus da kusoshin adawa

Har yanzu jami'an tsaro ba su yi martani kan harin Katsina ba
Mukaddashin Sufeton yan sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu Hoto: Nigerian Police Force
Source: Twitter

An shiga yarjejeniyar ne a tsakanin shugabannin Kankara da ‘yan bindiga kafin farkon watan Ramadan.

Wannan lamari na nuna cewa tsaro a yankin na ci gaba da kasancewa babban kalubale, duk da kokarin da hukumomi da shugabannin al’umma suka yi.

Mazauna yankin sun bayyana damuwarsu kan yadda ake kai masu hare-haren babu rana, babu dare.

Rahotanni sun nuna cewa har yanzu ba a samu bayanin daga jami’an tsaro game da wadannan hare-haren ba.

Mutane sun mutu a jihar Katsina

A baya, mun wallafa cewa an rasa rayuka yayin rabon Zakkar Ramadan a gidan wani attajiri da ke Kofar Guga a jihar Katsina lamarin da ya jefa mutane a damuwa.

Mutane 18 sun jikkata, an garzaya da wadanda suka ji raunuka zuwa Babban Asibitin Katsina domin kulawar gaggawa bayan faruwar mummunan al'amarin.

‘Yan sanda sun gayyaci wadanda suka shirya rabon Zakkar domin tambayoyi yayin da bincike ke gudana kan iftila'in da ya jefa iyalai da dama a cikin damuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng