Yakin Amurka da Iran: Matatar Dangote Ta Yi Magana kan Yiwuwar Samun Man Fetur a Najeriya

Yakin Amurka da Iran: Matatar Dangote Ta Yi Magana kan Yiwuwar Samun Man Fetur a Najeriya

  • Matatar man Dangote ta yi tsokaci kan yadda abubuwa faruwa wajen samun danyen mai a duniya sakamakon rikicin da ake yi a Gabas ta Tsakiya
  • Ta bayyana cewa rikicin ya jawo farashin gangar danyen mai ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin duniya
  • Sai dai, duk da haka matatar ta ba 'yan Najeriya tabbaci kan yiwuwar samun isashshen man fetur a cikin gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Matatar man Dangote ta yi magana kan samar da isashshen man fetur a Najeriya yayin da ake ci gaba da rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.

Matatar Dangote ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa za ta ba da fifiko wajen samar da mai a cikin gida domin hana fuskantar karancin man fetur.

Matatar Dangote ta ce za a samu isashshen man fetur a Najeriya
Motocin daukar man fetur a matatar man Dangote Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da matatar ta fitar ranar Alhamis, 5 ga watan Maris 2026 a shafin X.

Kara karanta wannan

Najeriya ta shiga jerin kasashe 3 da za su samu alheri sakamakon yakin Iran da Amurka

Ta bayyana cewa tana nan daram kan alkawarinta na kasancewa ginshikin daidaita kasuwar makamashi ta Najeriya a daidai lokacin da ake samun matsala wajen samar da mai a duniya sakamakon yakin Gabas Ta Tsakiya.

Me matatar ta ce kan rikicin Gabas ta Tsakiya?

A cewar matatar, wannan rikicin ya tilasta rufe wasu matatun mai da kuma rage yawan man da ake tacewa a kasashe da dama, wanda hakan ya jawo karancin kayayyakin man fetur a duniya.

Haka kuma, matatar ta yi nuni da cewa kasar China ta dakatar da fitar da gas da dizal zuwa kasashen waje, lamarin da ya kara dagula harkar samar da mai a duniya.

Tabbacin da matatar Dangote ta ba 'yan Najeriya

Matatar ta ce za ta tabbatar da cewa Najeriya ba ta dandana radadin wadannan matsalolin ba, ta hanyar tabbatar da cewa an fi ba wa kasuwar cikin gida muhimmanci.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“Wannan yana daya daga cikin alfanun tace mai a cikin gida."

An samu karin farashin danyen mai

Sanarwar ta nuna cewa rikicin ya tura farashin danyen mai da kudin sufurinsa sama sosai, inda farashin danyen mai na Brent Crude ya tashi da kashi 26 a cikin kankanin lokaci zuwa sama da 84 kan kowace ganga.

Kara karanta wannan

Aminu Gwarzo: Matakai 8 da majalisar Kano za ta bi don tsige mataimakin gwamna

Sakamakon wannan tashin gwauron zabi na kudin sayo danyen mai, matatar ta ce ta aiwatar da karin N100 kan kowace litar man fetur da take sayarwa 'yan kasuwa, wanda hakan ke nuna karin kashi 12 cikin 100.

Sai dai, matatar ta ce ta dauki nauyin kashi 20 cikin 100 na tsadar kudin domin saukakawa al’ummar Najeriya radadin hakan.

Matatar Dangote za ta yi wa 'yan Najeriya kokari kan fetur
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Yadda matatar Dangote take sayen danyen mai

Matatar ta bayyana cewa tana sayen danyen mai ne a farashin kasuwar duniya, ko daga cikin gida ko daga waje.

Ta kara da cewa danyen man Najeriya yakan kasance da karin tsadar dala 3 zuwa dala 6 sama da farashin Brent, yayin da kudin sufuri ke karuwa da dala 3.50 kan kowace ganga.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“Sakamakon haka, danyen mai yana isa matatarmu ne a kan farashin tsakanin $88 zuwa $91 kowace ganga."

Ta nuna cewa a baya danyen man yana isowa ne a kan $68 lokacin da ake sayar da litar mai a kan N774.

Dangote na shirin bunkasa arzikinsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya shirya fadada harkokin kasuwancinsa.

Kara karanta wannan

Malamai sun yi magana, sun fadi yadda yakin Iran da Amurka ya shafi Najeriya

Dangote na da shirin fadada kasuwancinsa zuwa fannin samar da karafa, samar da wutar lantarki, da kuma haɓaka tashoshin jiragen ruwa.

Hamshakin attajirin ya nuna cewa tace mai wani mataki ne kawai na babban burin da yake da shi wajen bunkasa nahiyar Afrika.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng