Abu Ya Girma: Mataimakin Gwamnan Kano na Tsaka Mai Wuya, Majalisa Ta Tura Masa Sako
- Majalisar dokokin Kano ta fara bin matakan da doka ta tanada da nufin tsige mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo
- Rahoto ya nuna cewa Majalisar jihar ta sanar da Aminu Gwarzo shirinta na tsige shi a wata takarda da ta aika ofishinsa yau Alhamis
- Takardar na kunshe da duka tuhume-tuhumen da Majalisar take yi masa, wanda ya kunshi amfani da mukaminsa ta hanyar da ba ta dace ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Majalisar Dokokin Kano ta aike wa Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, takardar sanarwa a hukumance kan fara shirin tsige shi daga mukaminsa.
Hakan na zuwa ne sa'o'i kadan bayan Shugaban masu rinjaye a Majalisar, Hon. Lawan Hussaini Dala ya gabatar da takardar neman sauke Aminu Abdussalam Gwarzo daga kujerarsa.

Source: Facebook
Majalisar Kano ta tura sako ga Aminu Gwarzo

Kara karanta wannan
"Kada a dagula siyasar Kano": NNPP ta aika sako kan shirin tsige Mataimakin gwamna
Daily Nigerian ta rahoto cewa Majalisar ta tura wasika domin sanar da mataimakin gwamnan shirin sauke shi bisa zargin aikata manyan laifuffukan da suka shafi almundahana.
Majalisar ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan zarge-zargen da ake masa tun lokacin da yake rike da mukamin kwamishinan kananan hukumomi na jihar.
Ta ce an dauki matakin ne bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, musamman sashe na 188 da ya fayyace yadda ake tsige manyan jami’an gwamnati.
Abubuwan da ke cikin takardar majalisar
A cikin sanarwar da majalisar ta fitar, an zargi mataimakin gwamnan da cin amana yayin da yake kula da harkokin kananan hukumomi 44 na jihar Kano, cewar rahoton Daily Trust.
Majalisar ta lissafa tuhume-tuhumen da take wa Aminu Gwarzo a takardar da ta tura ofishinsa ciki har da batun karbar wani kaso daga kowace karamar hukuma lokacin da yake kwamishinan kananan hukumomi.
Majalisar ta bayyana cewa irin wannan dabi’a ta saba da ka’idojin gaskiya da rikon amana da ake bukata daga jami’in gwamnati, kuma ta lalata martabar ofishin mataimakin gwamna.

Source: Facebook
Majalisa ta fadi girman laifin da ake zarginsa
’Yan majalisar sun kara da cewa amfani da mukamin gwamnati wajen karkatar da kudaden jama’a ya saba wa nauyin da kundin tsarin mulki ya dora wa masu rike da mukaman gwamnati.
A cewarsu, irin wannan laifi ya shiga cikin abin da kundin tsarin mulki ya ayyana a matsayin “mummunan laifi” wanda zai iya kai ga tsige jami’in gwamnati daga mukaminsa.
A karshe, ta bayyana cewa ’yan majalisa da suka sanya hannu kan kudurin sun bukaci a tsige Aminu Abdulsalam Gwarzo daga mukaminsa, bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.
Wani dan Kwankwasiyya a Kano, Malam Said Abdullahi ya shaidawa Legit Hausa cewa dama sun san za a zo nan wurin game da batun Aminu Gwarzo.
A cewarsa, duk dalilan da 'yan Majalisar suka bayyana ba gaskiya ba ne, kawai sun fake da su ne domin cimma burinsu na siyasa.

Kara karanta wannan
Murtala Garo da 'yan siyasa 6 da ake gani za a dauko idan aka tsige Mataimakin gwamnan Kano
"Ya ki bin 'yan a ci dadi lafiya shi ne dalilin shirin tsige shi, amma maganar da ya ci kudaden kananan hukumomi ba gaskiya ba ne, kawai dai sun fake da hakan ne, ba komai siyasa ce," in ji shi.
Yadda aka fara shirin tsige Aminu Gwarzo
Tun farko, kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Kano ta fara shirin tsige Mataimakin gwamna, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kano, Hon. Lawan Hussaini Dala, ne ya gabatar da takardar kudirin tsige mataimakin gwamnan.
Hon. Lawan Dala ya bayyana zarge-zargen da ake wa mataimakin gwamnan, inda ya ce cewa ‘yan majalisa 38 ne suka sanya hannu kan kudirin tsige shi, adadin da ya kai wanda doka ta tanada.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
