Magana Ta Kare: Kotu Ta Yanke Hukuncin Karshe a Shari'ar Abba Kyari da Gwamnati

Magana Ta Kare: Kotu Ta Yanke Hukuncin Karshe a Shari'ar Abba Kyari da Gwamnati

  • Babbar kotun tarayya ta wanke DCP Abba Kyari daga tuhume tuhume 23 da suka shafi kin bayyana kadarori da NDLEA ta shigar
  • Mai shari'a James Omotosho ya bayyana cewa NDLEA ta gaza gabatar da kwararan shaidu domin tabbatar da zargin da take yi wa Kyari
  • Har yanzu Kyari da wasu jami'an yan sanda hudu suna fuskantar wata shari'ar daban kan zargin safarar hodar iblis da wasu kwayoyi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Wata babbar kotun tarayya dake birnin Abuja ta yanke hukuncin karshe a shari'ar Abba Kyari, mataimakin kwamishinan yan sanda (DCP) da aka dakatar, da hukumar NDLEA.

Kotu ta wanke tare da sallamar Abba Kyari daga zarge-zarge 23 dake da alaka da kin bayyana kadarori, da NDLEA ta shigar a kansa da wasu 'yan uwansa.

Kara karanta wannan

El Rufai: ICPC ta fitar da jerin abubuwa 67 da ta samu a gidan tsohon gwamnan Kaduna

Kotu ta wanke Abba Kyari daga zarge zarge 23 da take yi wa Abba Kyari da 'yan uwansa.
Abba Kyari, mataimakin kwamishinan 'yan sanda da aka dakatar a filin Idi. Hoto: Datti Assalafiy
Source: Facebook

NDLEA: Kotu ta wanke Abba Kyari

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ce ta shigar da karar tana zargin Kyari da boye wasu kadarori da ake zargin mallakinsa ne, in ji rahoton The Cable.

An gurfanar da Kyari ne tare da kannensa guda biyu, wadanda ake zargi da yin rantsuwar karya domin boye asalin wasu kaddarori da ake alakantawa da dan sandan.

Sai dai, a hukuncin da ya yanke yau Alhamis, Mai shari’a James Omotosho ya bayyana cewa masu kara sun gaza gabatar da kwararan hujjoji kan zargin da suke yi.

Yayin da yake karanta hukuncin, Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa NDLEA ba ta gabatar da gamsassun shaidu da hujjoji da za su nuna cewa kadarorin da aka ambata a cikin karar mallakar Abba Kyari ne ba.

Lauyoyin NDLEA sun gaza gabatar da hujjoji

Mai shari'ar ya yi bayanin cewa za a iya tabbatar da mallakar fili ne kawai ta hanyar tarihin gado, takardun mallaka, ko kuma shaidar mallakar filin, amma NDLEA ba ta gabatar da ko daya daga cikin wadannan shaidun ba.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki sabuwar matsaya a shari'ar Abubakar Malami da dansa

Musamman kan gidan dake rukunin gidajen Fountain Estate dake Kasana, wanda ake zargin na Abba Kyari ne, kotu ta gano cewa na Ramatu Kyari ne, kuma babu wata hujja dake nuna cewa na d'an sandan ne.

Haka kuma, kotun ta gano cewa kadarorin dake Asokoro da Maiduguri babu shaidar dake alakanta su da Abba Kyari.

A yayin kare kansa, Abba Kyari ya shaida wa kotu cewa kadarorin dake jihar Borno na mahaifinsa ne wanda ya rasu, kuma gado ne shi da sauran yan uwansa suka raba.

Kotu ta nemi a daina gallazawa Kyari

Mai shari'a Omotosho ya bayyana cewa NDLEA ba ta iya karyata wannan ikirari na Kyari ba, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Sannan kuma, kotun ta yi watsi da zargin hadin baki da ake yi wa kannen Kyari, Mohammed da Ali Kyari, inda ta bayyana zargin a matsayin wanda ba shi da tushe.

Mai shari'a ya siffanta karar ta NDLEA a matsayin mai rauni, yana mai cewa Abba Kyari ya yi wa kasa aiki don haka bai kamata a dinga gallaza masa ba muddin babu kwararan shaidun laifi.

Kara karanta wannan

An kama wanda ke tono kabari yana cire sassan gawa a watan Ramadan

Sai dai, har yanzu Kyari da wasu jami'an yan sanda hudu suna fuskantar wata shari'ar daban a gaban Mai shari'a Emeka Nwite kan zargin safarar hodar iblis.

Kotu ta ce NDLEA ta gaza gabatar da hujjojin da za su tabbatar da laifuffukan Abba Kyari
Abba Kyari tare da tarin lauyoyinsa a cikin babbar kotun tarayya Abuja. Hoto: Hamza Nuhu Dantani
Source: Facebook

Abin da lauyan Kyari ya ce

Bayan yanke hukuncin, daya daga cikin lauyoyin Abba Kyari, watau Hamza Nuhu Dantani, ya wallafa a shafinsa na Faebook cewa:

"Nasara daga Allah!! AlhamudulilLahi.
"Yau babbar kotun dake Abuja ta wanke duk tuhuma da NDLEA sukeyi Akan Abba Kyari.. akan Laifuffuka 23.
"Tace bai dace ace sun yi mashi irin wannan mummunan sharrin ba, a kan lamari na mallakar dukiyoyin da kuma almundahana..
"Kotu ta ce sun kasa gamsar da ita akan cewa Abba Kyari mai laifi ne.
"Kotu ta ce Abba Kyari, jajirtacen 'dan sanda ne, kuma haziki ne, bai dace a ce an saka mashi da wannan sharrin ba, a matsayinsa na mutumin da ya bada gudunmawarsa a harkar tsaro.

Hamza Nuhu Dantani ya ce saura daya shari'ar wadda take gaban wata kotun, kuma suna da yakin ita ma za su yi nasara.

Wasu kadarori da aka ce Kyari ya mallaka

Kara karanta wannan

Alkali ta amince da bukatar Abubakar Malami da dansa, an kafa sharadi a kotu

Mun kawo muku labarin cewa Gwamnatin tarayya ta gano wasu kadarori 14 wanda ake zargin Abba Kyari ya mallaka na filaye, gidaje da makudan kudade.

Ofishin Ministan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin Najeriya yana zargin DCP Kyari da laifin boye gaskiya a game da mallakar wadannan dukiyoyi.

An shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CR/408/22 a kotun tarayya na garin Abuja. Mohammed Kyari da Ali Kyari suna cikin wadanda ake kara a shari'ar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com