Yaki da Iran: Amurka Ta Hango Barazana a Najeriya, Ta Rufe Ofishinta Kirif

Yaki da Iran: Amurka Ta Hango Barazana a Najeriya, Ta Rufe Ofishinta Kirif

  • Rikicin kasashen Amurka/Isra'ila da Iran da ya shiga rana ta shida na cigaba da shafar harkokin tattalin arziki da zirga-zirga a fadin duniya
  • A Najeriya, ofishin jakadancin Amurka a Abuja ya sanar da dakatar da aiki na wasu kwanaki sakamakon barazana da ya ke hangowa
  • Ya bayyana matakan da ya kamata wadanda ya yi wa alkawarin biza su dauka tare da sanar da ranar da ya ke hasashen zai dawo aiki a Abuja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Amurka na cigaba da daukar matakai a fadin duniya bayan fara yaki da kasar Iran a ranar Asabar da ta wuce.

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya da ke birnin tarayya Abuja ya sanar da dakatar da aiki saboda wata barazana da ya hango a kasar.

Kara karanta wannan

Iran ta ce ta kashe sojojin Amurka 500 a luguden wuta da ta masu

Shugaban Amurka, Donald Trump
Donald Trump yayin wani taro a kasar Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Legit Hausa ta tattaro bayanan da ofishin jakadancin Amurka ya fitar game da dakatar da aiki na a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

Amurka ta rufe ofishin jakadanci a Najeriya

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya sanar da dakatar da aiki saboda yiwuwar zanga-zangar da za ta iya jawo tashin hankali.

Ofishin ya ce:

Saboda yiwuwar zanga-zanga a Abuja, ofishin jakadancin Amurka zai kasance a rufe ga harkokin yau da kullum har zuwa ranar Litinin, 9 ga Maris, 2026."

Game da wadanda suke neman biza, ofishin ya ce:

"Alƙawuran neman biza da aka tsara a ranakun 4 da 5 ga Maris, da kuma alƙawuran ACS ga 'yan Amurka na ranar 5 ga Maris, an dage su zuwa mako mai zuwa."

Kiran Amurka ga masu neman biza

Biyo bayan dakatar da tsarin bayar da biza, Amurka ta bukaci dukkan wadanda suka tura bukatu su duba asusun imel dinsu.

Kara karanta wannan

Komai ya fito: An fadi aikin da sojojin Amurka da aka jibge a Bauchi za su yi

Punch ta rahoto sanarwar ta ce:

"Masu neman biza, ku duba imel ɗinku ko kuma asusun AVITs domin ganin sabuwar ranar da za mu hadu."
"Masu bukatar ACS, Ku duba imel ɗinku domin ganin sabuwar ranar haduwarmu..

Karin bayani daga ofishin Amurka

Saboda fargabar rashin ganin sako a imel din masu neman biza, Amurka ta fadi hanyar da ya kamata mutane su bi idan ba su ga sakon da aka tura musu ba.

Ta ce:

"Idan ba ku ga sabon ba, masu neman biza su tuntube mu ta hanyar Visa Navigator domin samun taimako."
"Ku ci gaba da bibiyar shafin yanar gizonmu da kuma kafafen sada zumunta domin samun ƙarin bayanai."
"Muna godiya da fahimtar da kuka mana da kuma haɗin kan da kuke bayarwa."

Me sojojin Amurka za su yi a Najeriya?

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta yi karin bayani game da abin da sojojin Amurka za su yi a Najeriya bayan zuwansu.

Kara karanta wannan

Yakin Iran da Isra'ila: Amurka ta yi gargadi da ake fargabar barkewar zanga zanga a Abuja

Ministan tsaro, Janar Christopher Musa (Mai ritaya) ya ce sojojin Amurka za su ba na Najeriya horo ne kawai, ba za su jagoranci yaki ba.

Ya yi karin bayani ne yayin da 'yan Najeriya ke cigaba da tambayoyi kan hakikanin abubuwan da sojojin Amurka da aka kai Bauchi za su yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng