Komai Ya Fito: An Fadi Aikin da Sojojin Amurka da aka Jibge a Bauchi za Su Yi
- Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya) ya yi karin haske game da rawar da sojojin Amurka za su taka a kasar nan
- Christopher Musa ya yi bayani ne a wani taron tsaro da aka gudanar a birnin tarayya Abuja da ya samu halartar manyan jami'an gwamnati
- Bayanin ministan ya zo ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke cigaba da tambayoyi game da zuwan sojojin Amurka da saukarsu a Bauchi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), ya tabbatar da cewa rundunar sojin Najeriya za ta ci gaba da rike cikakken iko kan dukkan ayyukan soji a cikin kasar.
Ya yi bayanin ne yayin da ake cigaba da tambayoyi game da zuwan sojojin Amurka Najeriya da rawar da za su taka a yaki da ta'addanci.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin taron farko na bayanin ayyukan soji na wata-wata da aka gudanar a hedikwatar ma’aikatar tsaro da ke Abuja.
Me sojojin Amurka za su yi a Najeriya?
Da yake magana kan rawar da rundunar Amurka ta FRICOM ke takawa a Najeriya, Ministan tsaron ya jaddada cewa jami’an Amurka suna kasar ne kawai domin bayar da horo da kuma shawarwari.
Janar Musa mai ritaya ya bayyana cewa kwamandojin sojojin Najeriya ne ke da cikakken iko kan jan ragamar hare-hare da sauran ayyukan soja.
Bayanin ministan tsaron ya zo ne a daidai lokacin da jama’a ke bukatar bayani kan kasancewar sojojin kasashen waje a Najeriya, musamman dangane da irin rawar da suke takawa a ayyukan tsaro na kasar.
Dalilin yin taron tsaro a Najeriya
Mai ba Ministan tsaro shawara kan harkokin yada labarai, Kanal Timothy Antigha (mai ritaya), ya ce taron ya jaddada bukatar kara inganta dabarun yaki da ta’addanci, tada kayar baya da kuma fashi da makami.

Kara karanta wannan
Ronaldo ya lallaɓa ya bar Saudiyya saboda rikicin Isra'ila, Iran? an ji gaskiyar zance
Ya kara da cewa Janar Musa ya yaba da sadaukarwar sojojin Najeriya tare da sake jaddada kudirin ma’aikatar na kula da walwalarsu da inganta ayyukansu.

Source: Facebook
Sanarwar ta kara da cewa:
“Taron ya bai wa Ministan damar duba ayyukan da ake gudanarwa a halin yanzu, tsara dabaru, da kuma tabbatar da cewa jami’an tsaron Najeriya suna rike da cikakken iko kan ayyukan soji a cikin gida.”
Taron ya samu halartar karamin ministan tsaro, Bello Matawalle; Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; hafsoshin rundunonin soji da kuma manyan jami’an leken asiri da sauransu.
Janar Musa mai ritaya ya wallafa wasu daga cikin hotunan da aka dauka a taron a wani sako da ya fitar a shafinsa na Facebook.
Malamai sun magantu kan tsaro
A wani labarin, kun ji cewa wasi malaman Musulunci sun yi magana game da yanayin tsaron Najeriya da yakin da ake Gabas ta Tsakiya.
Sun bayyana cewa bai kamata 'yan Najeriya su yi kokarin tayar da rikici a kasar su saboda yakin da ake yi tsakanin Amurka/Isra'ila da Iran ba.
Yayin da suka halarci taron shan ruwa a gidan gwamnatin Legas, malaman sun bukaci jama'a su guji shirya zanga-zanga saboda goyon bayan wata kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
