El Rufai: ICPC ta Fitar da Jerin Abubuwa 67 da Ta Samu a Gidan Tsohon Gwamnan Kaduna

El Rufai: ICPC ta Fitar da Jerin Abubuwa 67 da Ta Samu a Gidan Tsohon Gwamnan Kaduna

  • Hukumar ICPC ta bayyana jerin takardu da na’urorin da ta ce ta kwaso daga gidan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da ke Abuja
  • Jami'an sun bayyana haka ne a cikin takardun shari’a domin kalubalantar karar Naira biliyan daya da El-Rufai ya shigar kan take hakkinsa
  • Iyalan tsohon gwamnan sun ce kayan da aka kwashe ba komai ba ne illa tsofaffin wayoyi da na’urorin ajiyar bayanai na kashin kai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta bayyana cikakken bayani kan wasu takardu da na’urorin da ake zargin jami’anta sun kwaso daga gidan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El‑Rufai.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin takardun da ta gabatar gaban babbar kotun Abuja inda take kalubalantar karar take hakkin dan Adam ta Naira biliyan daya da tsohon gwamnan ya shigar.

Kara karanta wannan

Asara ta fara bin Amurka, ta rasa biliyoyin Daloli kwanaki 5 da fara yakin Iran

ICPC ta ce an samu takardu a gidan El-Rufai
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i a lokacin yana mulki Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa El-Rufai ya shigar da karar ne yana kalubalantar abin da ya kira kama shi ba bisa ka’ida ba, tsare shi, da kuma binciken gidansa da jami’an ICPC suka yi.

Nasir El-Rufa'i: Abin da jami'an ICPC suka gano

Jaridar Punch ta wallafa cewa a cewar hukumar, jami’anta sun gudanar da binciken ne bisa sahihin sammacin bincike da aka bayar ranar 18 ga Fabrairu,2026.

ICPC ta kara da cewa bayan samun sammacin, ta binciki gidan tsohon gwamnan a ranar 19 ga Fabrairu 2026 tsakanin 1:37 na rana zuwa 3:56 na rana a gidan da ke titin Mambilla, Asokoro a Abuja.

Ta ce lokacin binciken, jami’anta sun samu rakiyar jami’an yan sanda, kuma binciken ya gudana ne a gaban matar tsohon gwamnan, Hadiza El‑Rufai, da dansa Mohammed El‑Rufai.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki sabuwar matsaya a shari'ar Abubakar Malami da dansa

Hukumar ta ce daga cikin takardun da aka kwaso akwai bayanan asusun masu zuba jari, takardun bayyana kadarori, takardun rajistar kamfanoni, da bayanan bin ka’idojin kamfanoni.

Sauran kayan da aka samu a gidan El-Rufa'i

Sauran abubuwan da aka samu sun hada da takardun bayanan abokan hulda da wasu takardu da suka shafi jam'iyya.

Sauran sun hada da bayanan lamuni na cikin gida da na waje da majalisar dokokin Kaduna ta amince da su tsakanin 2015 zuwa 2023.

An kuma kwaso takardun shaidar hannun jari na Ecobank Nigeria Plc, takardun filaye, rahotannin kimanta kadarori, takardun mallakar gida, da wasu takardu da suka shafi kamfanin Afri-Venture Capital.

ICPC ta shigar da kayan da ta samu a gidan El-Rufa'i gaban kotu
Ginin hukumar yaki da rashawa ta ICPC da ke Abuja Hoto: ICPC Nigeria
Source: Twitter

Dangane da na’urorin lantarki, ICPC ta ce an kwaso na’urorin ajiyar bayanai guda tara, kati guda ɗaya, manyan faifan ajiya guda bakwai, da kwamfutoci da dama

Haka kuma an ce an samu wayoyin salula da dama ciki har da Blackberry, Nokia N95, Toshiba, Samsung IDEOS da Google IDEOS, tare da wasu na’urori kusan 18.

Kara karanta wannan

Matar El Rufa'i ta lissafa na'urorin da jami'an ICPC suka kwashe daga gidansu

Matar El-Rufa'i ta magantu kan ICPC

A baya, kun samu labarin cewa Hadiza Isma El-Rufai, matar tsohon gwamnan Kaduna ta ce ICPC ta kwashe mata wasu muhimman na'urorin yayin bincike a gidansu.

Hadiza Isma ta yi zargin cewa hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta'annati mai zaman kanta ta ICPC ba ta saka na’urorin cikin jerin kayayyakin ta kwato daga gidan ba.

Uwargidan tsohon gwamnan ta bayyana haka ne a yayin da ICPC ta yi ikirarin cewa ta samu wasu na'urorin da ake zargin na kutsen waya ne a gidan Nasir El-Rufa'i.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng