Ana Azumi Sanata Ya Gano Laifuffukan da Ba Su Kai 'Yan Siyasa Shiga Jahannama ba

Ana Azumi Sanata Ya Gano Laifuffukan da Ba Su Kai 'Yan Siyasa Shiga Jahannama ba

  • Sanata Adams Oshiomhole ya halarci babban taron jam'iyyar APC na jihar Edo inda aka zabi shugabannin jam'iyya
  • A wurin taron, sanatan mai wakiltar Edo ta Arewa ya yi tsokaci kan takaddamar da ya taba samu da shugaban jam'iyyar na jihar
  • Hakazalika, ya bayyana cewa kura-kurai a siyasa abubuwa ne wadanda dole ne a samu 'yan siyasa da aikata su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Edo - Sanata Adams Oshiomhole, mai wakiltar mazaɓar Edo ta Arewa, ya yi magana kan laifuffukan siyasa.

Sanata Oshiomhole ya bayyana cewa ’yan siyasa ba za su shiga wutar jahannama ba saboda zunuban da suka aikata na fannin siyasa.

Oshiomhole ya yi magana kan laifuffukan siyasa
Sanata Adams Oshiomhole mai wakiltar Edo ta Arewa Hoto: Sen Monday Okpebholo
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce tsohon gwamnan na jihar Edo, Oshiomhole, ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 3 ga watan Maris 2026 a birnin Benin, babban birnin jihar Edo.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Abba da ya yi murabus ya zama Shugaban APC bayan awanni a Kano

Adams Oshiomhole ya yi magana kan siyasa

Oshiomhole ya yi magana ne lokacin gudanar da babban taron jam’iyyar APC na jihar, inda aka sake zaɓar Jarret Tenebe a matsayin shugaban jam’iyya, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.

Yayin da yake magana kan zargin takaddama tsakaninsa da shugaban APC na jihar, Oshiomhole ya ce:

"Laifuffukan siyasa abu ne da aka saba da shi a fagen siyasa, kuma ba zai kai kowa wutar jahannama ba."

A cewarsa, Tenebe ya aikata wasu zunubai a kansa (Oshiomhole), amma ya riga ya yafe masa, ganin cewa sun riga sun shirya.

"Dole ne 'yan siyasa dole ne su yi wasu kura-kurai, amma hakan ba zai kaisu wutar jahannama ba”.

- Sanata Adams Oshiomhole

Oshiomhole ya yi watsi da ikirarin 'yan adawa

Game da kukan da jam’iyyun adawa ke yi na cewa APC tana neman mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya tilo, Oshiomhole ya ce babu wata shaida da ke nuna cewa ana tilasta wa wani barin jam’iyyarsa domin ya shiga APC.

Kara karanta wannan

"Ba da jam'iyyu ba ne"; Atiku ya fadi masu fafatawa da Tinubu a zaben 2027

“A makon da ya gabata, ɗaya bayan ɗaya, ’yan adawa na ta kukan cewa APC na mayar da Najeriya kasa mai jam’iyya ɗaya."
"Amma har yanzu, ba su kawo shaidar mutum ko ɗaya da aka tilasta masa barin jam'iyyarsa don ya shiga APC ba."

- Sanata Adams Oshiomhole

Oshiomhole ya yi magana kan maida Najeriya kasa mai jam'iyya daya
Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole Hoto: Adams Oshiomhole
Source: Facebook

Batun maida Najeriya mai jam'iyya daya

Sanata Oshiomhole ya jaddada cewa tsarin mulkin Najeriya bai ba wata jam’iyya damar hana kowa haƙƙinsa na shiga jam’iyyar da yake so ba.

“Kuma ya zama dole Shugaba Bola Tinubu ya mutunta tanadin wannan tsarin mulkin. Kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) yana bin ƙa’idojin wannan tsarin mulkin, saboda haka ba mu da ikon hana duk wanda yake son shiga sahunmu”.
“Masu kukan cewa mutane na komawa APC, ya kamata su bincika dalilin da ya sa suka kunna wa jam’iyyunsu wuta har mutane ke fita daga cikinsu."

- Sanata Adams Oshiomhole

Oshiomhole da Ndume sun yi musayar yawu

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu hatsaniya a zauren majalisar dattawa bayan cacar baki ya barke tsakanin Sanata Adams Oshiomhole da Sanata Ali Ndume.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An bukaci shugaban hukumar zaben Najeriya, INEC ya yi murabus

Sanatocin sun yi wa juna zafafan maganganu yayin zaman tantance sababbin jakadu da aka tura domin amincewa da su.

Hatsaniyar dai ta faru ne a gaban kwamitin harkokin ƙasashen waje da Sanata Abubakar Sani Bello ke jagoranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng