Yakin Iran da Isra'ila: Amurka Ta Yi Gargadi da Ake Fargabar Barkewar Zanga Zanga a Abuja
- Ofishin Jakadancin Amurka da ke birnin Abuja ya fitar da sanarwa game da barazanar yin zanga-zanga a Najeriya
- Fargabar ta ya jawo soke duk wani shiri na ba da biza na ranar Laraba, 4 ga Maris, 2026 domin ci gaba da kula da tsaro
- Hakan na zuwa ne bayan barkewar rikici a Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da Kasar Isra'ila wanda ya yi sanadin Ayatollah Ali Khamenei
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ana fargabar barkewar zanga-zanga a birnin Abuja game da rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya
Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja ya soke duk wata ganawa da masu neman biza da aka tsara ranar Laraba, 4 ga Maris, 2026, bisa hasashen yiwuwar zanga-zanga a birnin.

Source: Getty Images
Zanga-zanga a Abuja: Amurka ta yi gargadi
Hakan na cikin wata sanarwa da aka fitar da shafin US Mission Nigeria ya wallafa a X a yau Labara 4 ga watan Maris din shekarar 2026.
Ofishin ya sanar wa ‘yan kasarsa cewa akwai yiwuwar a gudanar da zanga-zanga a babban birnin tarayya Abuja saboda rikicin da ake ciki tsakanin Isra'ila, Amurka da Iran.
Ya ce sakamakon wannan yiwuwar zanga-zanga sun soke dukkan ganawa da masu neman biza da aka tsara a ranar Laraba.
An ce kuma wadanda abin ya shafa za a tuntube su don a sanar da su yadda za su sake tsara lokutan su.
Har ila yau, ofishin ya kuma gargadi ‘yan kasar Amurka da su zauna a cikin gidajensu, su guji wuraren da ake tattaunawa ko za a yi gangami.

Source: Twitter
Shawarar Amurka ga yan kasarta a Najeriya
Amurka ta bukaci su kauce wa taron jama’a, su kasance masu kula da abin da ke kewaye da su, su rika sauraron labarai daga kafafen yada labarai na gida, tare da tabbatar wayoyinsu suna da caji don kiran agajin gaggawa idan bukata ta taso.
Sanarwar ta ce wannan gargadi ya biyo bayan tashin hankali da rikicin da ya ƙaru tsakanin kasashen Amurka, Isra’ila da Iran, wanda ke haifar da fargabar gangamin nuna adawa.
Matakin na zuwa ne yayin da rikici tsakanin Amurka da Iran ke ƙaruwa, lamarin da ka iya haddasa zanga-zanga a Abuja kamar yadda ya faru baya.
Ofishin ya ƙara da cewa za a ci gaba da bayar da sauran ayyukan ofishin jakadanci a Abuja da kuma ofishin jakadancin Amurka da ke Lagos.
Yan Shi'a sun magantu bayan kisan Khamenei
Tun farko, kun ji cewa jagororin Shi’a a Najeriya sun yi magana bayan rasuwar Ali Khamenei inda suka ce rasuwarsa ta kara fito da tasiri da martabar akidarsu.
Sun bayyana cewa ya bi turbar Ruhollah Khomeini tun daga hawansa mulki a 1989 tare da kawo sauyi da hadin kai a tsakaninsu .
Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da jimami bayan kisan jagoran addinin Musulunci a kasar Iran, Ali Khamenei wanda ya jefa Musulmai cikin damuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

