Yadda Kisan Khamenei Zai Shafi ’Yan Shi’a a Najeriya, Rashinsa Ya 'Hada' kan Musulmi

Yadda Kisan Khamenei Zai Shafi ’Yan Shi’a a Najeriya, Rashinsa Ya 'Hada' kan Musulmi

  • Ana ci gaba da jimami bayan kisan jagoran addinin Musulunci a kasar Iran, Ali Khamenei wanda ya jefa Musulmai cikin damuwa
  • Jagororin Shi’a a Najeriya sun ce rasuwarsa ta kara fito da tasiri da martabar akidarsu a kasar wanda suka shafe shekaru suna bi
  • Sun bayyana cewa ya bi turbar Ruhollah Khomeini tun daga hawansa mulki a 1989 tare da kawo sauyi da hadin kai a tsakaninsu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kisan jagoran addinin Iran, Ali Khamenei, ya girgiza duniya, musamman mabiya akidar Shi’a a sassa daban-daban na duniya ciki har da Najeriya.

An kashe Khamenei mai shekaru 86 a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran, lamarin da ya haifar da alhini da jimami a tsakanin mabiyansa.

Kisan Khemenei zai jefa mabiya Shi'a a Najeriya cikin zullumi
Shugaban kungiyar IMN ta mabiya Shi'a a Najeriya, Malam Ibrahim Zakzaky da marigayi Ali Khamenei. Hoto: Elite Pakistan, Islamic Movement of Nigeria.
Source: Facebook

A Najeriya, mabiya Shi’a sun fara gudanar da muzaharori da zanga-zangar lumana domin nuna alhininsu kan rasuwar jagoran, cewar BBC Hausa.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Yadda aka tsara hallaka Khamenei yayin da yake ganawar tsaro

Yadda harin Isra'ila ya hallaka Ali Khemenei

Kisan Ayatollah Ali Khamenei ya jawo tashin hankali ga al'ummar Musulmi duba da tasirin kasar Iran a cikin sauran kasashen Musulunci.

Hare-haren Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka ne suka yi nasarar kashe Khamenei yayin da yake ganawar tsaro da wasu manyan jami'an gwamnati.

Majiyoyi sun ce hukumar leken asiri ta CIA ta taka rawar gani wurin kisan bayan shafe lokaci mai tsawo tana bibiyar dukan lamuransa har zuwa ranarsa ta karshe a duniya.

Kisan Khamenei ya hada kan Musulmi
Marigayi jagoran addini a Iran, Ali Khamenei. Hoto: @khamenei_ir.
Source: Twitter

Kisan Khemenei: Martanin mabiya Shi'a a Najeriya

Daya daga cikin manyan almajiran Sheikh Ibraheem El-Zakzaky, Malam Sidi Mannir Mainasara, ya bayyana cewa rasuwar ta girgiza mabiya Shi’a a duniya baki daya.

Ya ce mutuwar bazata ta Ayatollah Ali Khamenei ta sake haskaka tasiri da martabar akidar Shi’a ke da shi a Najeriya

A cewarsa, mutane da dama sun ajiye bambancin akida tare da mika ta’aziyya, abin da ya ba su mamaki matuka.

Kara karanta wannan

Bayan hari a Saudiyya, Iran ta gamu da farmakin Isra'ila, an gano asarar da aka yi

Ya kara da cewa rasuwar ta sa mutane sun manta da sabanin fahimta na akida, suka hada kai wajen nuna alhini.

Malam Mainasara ya bayyana cewa tun daga 1989, lokacin da Khamenei ya zama jagoran addinin Iran bayan rasuwar Ruhollah Khomeini, ya ci gaba da tafiya a kan turbar da magabacinsa ya shimfida.

Ya ce duk da radadin rashinsa, mabiyansa na samun natsuwa idan suka tuna cewa sun dauki mutuwarsa a matsayin shahada.

Yadda aka kitsa kashe Ali Khamenei

Mun ba ku labarin cewa rahotanni daga hukumomi a Iran sun tabbatar da cewa an hallaka jagoran addini a kasar, Ali Khamenei ne a birnin Tehran.

Wasu majiyoyi sun ce ya mutu a hare-haren sama na hadin gwiwar Amurka da Isra’ila a Tehran da taimakon hukumar leken asiri ta CIA a ranar Asabar 28 ga watan Fabrairu, 2026.

Akalla mutane 787 sun mutu a Iran yayin da hare-hare da ramuwar gayya ke ci gaba kan Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka da wasu kasashen Larabawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.