Iran/Isra’ila: Izalah Ta Magantu kan Fara Al Kunut a Masallatai, Ta Tabo Matsalolin Najeriya
- Shugaban kungiyar Izala ta JIBWIS, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bukaci limamai su tsayar da addu’ar Al-Kunuti
- Bala Lau ya ce mafi yawan wadanda rikice-rikicen ke shafa Musulmi ne da ba su da laifi, yana mai nuna alhini kan salwantar rayuka
- Malamin ya roki Allah SWT ya kawo karshen zubar da jini tare da dawo da zaman lafiya a duniya da Najeriya baki daya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yola, Adamawa – Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Abdullahi Bala Lau, ya yi magana kan fara Al-Kunut a Najeriya.
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi kira ga daukacin limamai da al’ummar Musulmi a fadin Najeriya da su fara yin addu’o’in Al-Kunut a cikin sallolinsu.

Source: Facebook
Kungiyar Izala ta bukaci Al-Kunut a Najeriya
Malamin ya bayyana hakan ne ranar Talata, 3 ga Maris, 2026, yayin Tafsirin Ramadan da yake gabatarwa a Yola da ke Adamawa, kamar yadda JIBWS Nigeria ta wallafa a Facebook.
Ya ce an dauki wannan mataki ne sakamakon ta’azzarar rikice-rikice a Gabas ta Tsakiya da kuma karuwar hare-haren ta’addanci da ake fuskanta a Najeriya.
A jawabin nasa, ya nuna alhini kan yadda ake ci gaba da salwantar da rayukan jama’a, yana mai cewa mafi yawan wadanda abin ya shafa Musulmi ne da ba su san komai ba.
“Abu ne mai tayar da hankali yadda rayuka ke salwanta ba gaira ba dalili, iyaye, mata da yara suna shiga cikin halin kunci da rarrabuwar kawuna sakamakon rikice-rikicen da ke kara tsananta.”
Malamin ya bayyana halin da ake ciki a matsayin babbar jarabawa ga al’ummar Musulmi da ma duniya baki daya, musamman ganin cewa tashe-tashen hankulan na faruwa ne a yankunan da ke da muhimmanci a tarihin Musulunci.
Haka kuma, ya nuna damuwa kan yadda hare-haren ta’addanci ke kara kamari a wasu sassan Najeriya, inda ya ce al’ummomi da dama na rayuwa cikin fargaba sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.
“Ba za mu manta da abin da ke faruwa a kasarmu ba, yan ta’adda na ci gaba da kai hare-hare, al’ummomi na fuskantar barazana, kuma zaman lafiya na kara shiga hatsari. Wannan na bukatar mu tashi tsaye da addu’a da kuma gyaran halaye.”

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta tsoma baki a rigimar Iran da Isra'ila, Najeriya ta ba da shawara

Source: Facebook
Umarnin da Sheikh Bala Lau ya ba limamai
Sheikh Bala Lau ya bukaci limamai su ware lokaci a cikin salloli domin yin Al-Kunut, tare da rokon Allah ya kawo karshen zubar da jini, ya kare bayinsa, ya ba shugabanni hikima, tare da dawo da zaman lafiya a duniya da Najeriya baki daya.
Ya kara da cewa watan Ramadan wata dama ce ta tuba, komawa ga Allah, da neman rahama a lokutan kalubale.
A karshe, ya yi addu’ar Allah ya kawo sauki ga wadanda ke cikin kunci, a kawo karshen rikice-rikice, kuma ya wanzar da zaman lafiya mai dorewa a duniya da Najeriya.
“Allah shi ne mai iko a kan komai, gare shi muka dogara, kuma gare shi mu ke rokon mafita da zaman lafiya.”
Sheikh Jingir ya maganatu kan yan sandan jihohi
An ji cewa Shugaba majalisar malamai na kungiyar Izala reshen Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya nuna adawa da shirin kafa ‘yan sandan jihohi.
Sheikh Jingir ya yi gargadin akwai yiwuwar amfani da su don murkushe abokan adawa a Plateau wanda ba zai zama da dadi ba.
Malamin ya roki Bola Ahmed Tinubu da ya yi taka-tsantsan kafin amincewa da tsarin ‘yan sandan jihohi a fadin kasar baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

