Sojojin Najeriya Sun Harbo Jirgin Iran Marar Matuki a Sokoto? An Samu Bayanai

Sojojin Najeriya Sun Harbo Jirgin Iran Marar Matuki a Sokoto? An Samu Bayanai

  • Wasu rahotanni sun yada cewa rundunar sojojin Najeriya ta harbo wan jirgi marar matuki mallakin kasar Iran a jihar Sokoto
  • Rahoton da aka yada kan lamarin ya jawo fargaba duba da yadda ake ci gaba da rigima tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka
  • Wani bincike ya nuna ainihin inda bidiyon ya fito da aka danganta da kasar Iraki, ba daga Najeriya ba kamar yadda ake ta yadawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto – Mutane da dama sun yi ta yada wani labari cewa wai sojojin Najeriya sun kado jirgi marar matuki mallakin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Wani mai amfani da kafofin sadarwa ya yi ikirarin cewa wani jirgin yaki mara matuki na Iran ya yi batan hanya ya shiga Najeriya, inda rundunar sojoji ta harbo shi a kauyen Dan Musa da ke Sokoto.

Kara karanta wannan

Ronaldo ya lallaɓa ya bar Saudiyya saboda rikicin Isra'ila, Iran? an ji gaskiyar zance

An musanta labarin harbo jirgin Iran a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto da Amurka ta taba kai hari. Hoto: Legit.
Source: Original

Sai dai binciken Dubawa ya bayyana cewa wannan ikirari ba gaskiya ba ne, domin bidiyon da aka yada ya samo asali ne daga kasar Iraki, ba Najeriya ba.

An yada cewa sojoji sun harbo jirgin Iran

Rahoton ya ce yayin da rikici ke kara kamari a Gabas ta Tsakiya tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran, ana amfani da jiragen yaki mara matuki sosai wajen leken asiri da kai hare-hare.

Bidiyon da aka yada ya nuna wani jirgin yaki mara matuki da ya fadi a kan ciyawa mai yalwa a wani wuri na karkara, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.

Binciken da aka gudanar kan jita-jitar

Sai dai bincike ya nuna cewa Sokoto na cikin yankin Sahel mai yanayi busasshe ne, inda a watannin Fabrairu da Maris kasa ke kasancewa a bushe, ba kore mai yalwar ciyawa ba kamar yadda aka gani a bidiyon.

Haka kuma, an ambaci kauyen “Danmusa” a Sokoto, amma binciken taswira bai gano wani kauye mai wannan suna a jihar ba.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi kamari, Faransa ta tura jirage UAE da Iran ke kai hare hare

Maimakon haka, Danmusa karamar hukuma ce a Katsina, ba a Sokoto ba, lamarin da ya kara raunana sahihancin ikirarin.

An yada labarin kado jirgin Iran a Sokoto
Jirgi marar matuki a sararin samaniya da taswirar jihar Sokoto. Hoto: Legit, Chaiwat Subprasom/NurPhoto.
Source: Getty Images

Yadda aka gano gaskiya kan jita-jita a Sokoto

Masu binciken sun yi amfani da dabarun gane inda aka dauki hoto da bidiyo inda suka gano cewa kafar yada labarai ta Rudaw Türkçe da ke Erbil a Iraki ta taba wallafa wannan bidiyo tun da farko.

An wallafa bidiyon tare da bayanin cewa jirgin mara matuki na Iran ya fadi ne a kauyen Gırdaçal da ke da alaka da Erbil a Arewacin Iraki.

Bugu da kari, babu wata sanarwa daga Hedikwatar Tsaron Najeriya da ta tabbatar da cewa wani jirgin Iran ya shiga sararin samaniyar Najeriya ko an harbo shi.

A karshe, an tabbatar da cewa ikirarin cewa sojojin Najeriya sun harbo jirgin Iran a Sokoto ba gaskiya ba ne.

Iran ta hallaka sojojin Amurka a Kuwait

Mun ji cewa ana ci gaba da gwabza fada tsakanin Amurka da Iran bayan da aka fara fafatawa a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Makaman Iran sun dura babbar matatar mai a Saudiyya, gobara ta tashi

A cikin hare-haren da Iran ke kai wa kan sansanonin sojojin Amurka da ke wasu kashen Gabas ta Tsakiya, an kashe dakarun tsaron Amurka.

Majiyoyi sun bayyana cewa harin da Iran ta kai kan sojojin ya jawo an samu asarar dakarun tsaron Amurka da ke aiki a kasar Kuwait.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.