Kisan Jagoran Iran: Kano da Jihohin Najeriya 7 da Ƴan Shi'a Suka Yi Zanga Zanga
- Mabiya akidar Shi'a a Najeriya (IMN) sun mamaye titunan jihohi takwas a Najeriya domin yin Allah wadai da kisan Ayatollah Ali Khamenei
- 'Yan shi'a dai suna kallon Khamenei a matsayin jagoran addininsu, musamman ganin cewa IMN ta samu karfi ne daga Iran a shekarar 1979
- 'Yan Najeriya sun nuna bacin ransu kan zanga-zangar 'yan Shi'a, inda suke tsoron kada Amurka ta dauki mummunan mataki kan hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Legas - An barke da zanga-zanga a akalla jihohi takwas na Najeriya domin nuna adawa da kisan gillar da Amurka da Isra'ila suka yi wa Jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, a ranar Asabar, 28 ga Fabrairu.
Mambobin harkar Musulunci a Najeriya (IMN), wadanda aka fi sani da 'Yan Shi'a, ne ke jagorantar wannan zanga-zanga a jihohin Legas, Kano, Neja, Sakkwato, Gombe, Kaduna, Bauchi, da Yobe yanzu.

Source: Twitter
Kisan Khamenei: 'Yan Shi'a sun yi zanga zanga
Masu zanga-zangar sun yi tir da harin hadin gwiwa da aka kai wa kasar Iran, lamarin da ya janyo fargaba a sassan kasar, cewar rahoton Punch.
A birnin Legas, masu zanga-zangar sun yi tattaki ta yankin Maryland, suna dauke da kwalaye da takardu dake yin Allah wadai da abin da suka kira "mamayar Amurka" da kisan gilla ga jagoran Iran.
Faya fayan bidiyo da suka karade soshiyal midiya sun nuna mutane dauke da hotunan marigayi Khamenei suna rera wakoki da addu'o'i.
Mabiya Shi'a a Najeriya, wadanda tsiraru ne idan aka kwatanta da mabiya Izala, Darika, suna kallon Khamenei a matsayin madogara ta addini da siyasa, musamman ganin cewa IMN ta samu karfi ne daga juyin juya halin Musulunci na Iran na shekarar 1979.
Martanin 'yan sanda kan zanga zangar
Hukumomin tsaro a Najeriya sun bayyana cewa sun sa ido kan wannan zanga-zanga domin tabbatar da cewa ba a tayar da hargitsi ba, in ji rahoton BBC.
Rundunar yan sandan Najeriya ta sanar da karfafa tsaro a jihohin Arewa, tare da yin gargaɗin cewa:
"Duk wani yunkuri na shigo da matsalolin addini ko na ra'ayin kasashen waje cikin Najeriya zai fuskanci fushin hukuma."
IMN ta bayyana cewa tana shirin gudanar da wasu manyan zanga-zangar a ranar Juma'a mai zuwa domin nuna goyon baya ga Iran a yakin da take yi da Amurka.
'Yan Najeriya sun dura kan 'yan Shi'a
Sai dai, wannan zanga-zanga ta janyo kakkausan martani daga bangaren 'yan Najeriya daban-daban, musamman a shafukan sada zumunta.
A karkashin rahoton Punch da ta wallafa a shafinta na Facebook, Sola Adeoye ya soki masu zanga-zangar da cewa suna janyo wa Najeriya bakin jini a idon duniya.
Shi kuwa Otunba Richard ya ce abin mamaki ne yadda wasu yan Najeriya ke zanga-zanga alhali wasu 'yan Iran din ma murna suke yi da mutuwar Khamenei.
Tako Jeremiah shi ma ya bayyana cewa ya kamata a kai masu zanga-zangar kasar Iran din domin su nuna bacin ransu a can, tare da yin gargaɗi kan irin martanin da Shugaba Donald Trump zai iya yi wa Najeriya idan aka cigaba da haka.
Asali: Legit.ng

