Fasto Ya Kare Kansa game da Zuwa Makka da Madina, Ya Magantu kan Zama Musulmi
- Babban malamin addinin Kirista a Najeriya ya yi karin haske kan ziyara zuwa biranen Makka da Madina a Saudiyya
- Fasto Israel Ogundipe ya kare ziyarar da ya kai biranen masu tsarki bayan suka a kafafen sada zumunta da zarge-zarge
- Malamin ya jaddada muhimmancin fahimtar juna da ‘yancin binciken addini a duniyar da ake da mabambantan addinai
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Babban Faston cocin Genesis Global, Israel Ogundipe, ya yi karin haske bayan caccakarsa da aka yi ta yi kan zuwa Saudiyya.
Faston ya bayyana dalilin ziyararsa zuwa biranen Makka da Madina a Saudiyya, bayan hotunan tafiyar sun janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da ya aikewa jaridar Punch a ranar Litinin 2 ga watan Maris din shekarar 2026 da muke ciki.

Kara karanta wannan
Ronaldo ya lallaɓa ya bar Saudiyya saboda rikicin Isra'ila, Iran? an ji gaskiyar zance
Fasto ya magantu kan dalilin zuwa Makka, Madina
Ogundipe ya ce ziyarar ba ta da alaka da sauya addini ko kwatance tsakanin addinai, illa tafiya ce ta fahimta, tawali’u, tarihi da kuma dan’adamci.
Ya tuna cewa wata addu’a da mahaifiyarsa Musulma ta yi masa tun yana karami ita ce Allah ya ba shi damar ziyartar kasa mai tsarki idan ya girma, addu’ar da ya ce daga baya ta karbu.
Ya ce:
“Ɗaya daga cikin addu’o’inta na shi ne cewa, idan na girma, Allah ya ba ni ikon ziyartar Ƙasa Mai Tsarki. A lokacin, ban fahimci girman wannan addu’a sosai ba, amma Allah ya karba.
“Bayan shekaru masu yawa, na tsaya a Madina da Makka, kuma a wannan lokacin na gane cewa addu’o’i, idan suna da tsarki, suna wuce lokaci, mazhaba da iyakokin ɗan Adam.”

Source: Twitter
Fasto ya fadi fa'idar Makka da Madina
Ogundipe ya ce tsayuwarsa a Madina da Makka ta sa ya fahimci cewa addu’a mai tsarki ta zarce lokaci da bambancin addini.
Ya bayyana Madina a matsayin birni mai cike da natsuwa da karamci, yayin da ya ce Makka na kaskantar da zuciya, musamman ganin miliyoyin mutane daga kabilu da harsuna daban-daban suna ibada cikin hadin kai.
Malamin ya ce ziyararsa ta samo asali ne daga imanin cewa sanin juna na haifar da zaman lafiya, yana mai cewa jahilci ne ke haddasa kiyayya, amma ilimi na kawar da ita.
Game da batun binciken addini, Ogundipe ya ce ba laifi ba ne mutum ya binciki wani addini, yana mai misali da dokokin ‘yancin dan Adam na Birtaniya da ke kare ‘yancin tunani da akida.
A karshe, ya jaddada cewa tafiyarsa ta kasance ta karin ilimin addini wacce ta nuna muhimmancin tausayi, girmama juna da fahimtar addinai a duniya mai cike da sabani.
Mawakiya ta fadi dalilin rashin shiga Musulunci
Kun ji cewa mawakiya Cardi B ta yaba wa Musulmai kan juriyarsu a watan Ramadan, tana cewa ba za ta iya yin azumi na awa uku ba.
Card B ta fadi dalilin da ya sa Allah bai ƙaddara ta zama Musulma ba inda ta ce tabbas Musulmi na kokarin yin azumi a watan Ramadan.
Maganganunta sun jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, wasu na ganin abin dariya ne, wasu kuma na suka.
Asali: Legit.ng
