Amurka Ta Gaza Ceto 'Yan Kasarta a Isra'ila, Iran na Musu Luguden Wuta
- Yayin da yakin Iran da Amurka/Isra'ila ke kara kamari, Ofishin Jakadancin Amurka a Isra'ila ya sanar da cewa ba zai dauki alhakain ceto 'yan kasar ba
- Hakan na zuwa ne yayin da Iran ke cigaba da harba makamai masu linzami a Gabas ta Tsakiya tun bayan harin da Amurka/Isra'ila suka kai mata
- Baya ga kiran kowa ya yi ta kansa a Isra'ila, gwamnatin Amurka ta yi kira da 'yan kasarta su gaggauta barin kasashen da ke Gabas ta Tsakiya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Israel - Gwamnatin Amurka ta fitar da sanarwa game da 'yan kasarta yayin da Iran ke cigaba da luguden wuta a Isra'ila da sauran kasashen Gabas ta Tsakiya.
'Yan Amurka na kokarin barin Isra'ila saboda hare-haren da ke kaiwa, amma kasar ta ce ba za ta dauki alhakin mayar da su gida ba a halin yanzu.

Kara karanta wannan
An ji duriyar Firaministan Isra'ila, Netanyahu ana tsaka da rade radin Iran ta tura shi lahira

Source: Getty Images
Ofishin jakadancin Amurka a Jerussalem ya fitar da sanarwa a X game da matakan da 'yan kasar za su iya dauka ba tare ya shiga ciki ba kai tsaye.
Sakon Amurka ga 'yan kasarta a Isra'ila
Ofishin jakadancin Amurka a Isra'ila ya ce ba ya cikin halin da zai kwashe ko ya taimaka kai tsaye wa ‘yan Amurka su bar Isra’ila a wannan lokaci.
Sai dai ya bayar da bayanai domin kowa ya yi ta kansa, inda ya ce:
"Ma’aikatar yawon buɗe ido ta Isra’ila ta fara jigilar fasinjoji ta motoci zuwa mashigar Taba tun daga ranar 2 ga Maris.
"Domin a saka sunanka cikin jerin fasinjojin motar, dole ne ka yi rajista ta hanyar fom ɗin fitar da jama’a na ma’aikatar.
"Ofishin jakadancin Amurka ba zai iya ba da shawarar shiga ko kin amfani da wannan tsarin motar ba. Idan ka zaɓi amfani da wannan dama domin barin ƙasar, gwamnatin Amurka ba za ta iya ba da tabbacin tsaronka ba."
Amurka ta kara da cewa ta bayar da bayanan ne a matsayin taimako ga waɗanda ke son barin Isra’ila yayin da hare-hare ke karuwa.

Source: Getty Images
Ta kara da cewa fasinjojin da ke son ketarewa zuwa Jordan za su iya ɗaukar motar zuwa Eilat sannan su ci gaba da tafiya da kansu (ta tasi) zuwa mashigar iyaka ta Yitzhak Rabin.
Gargadi kan zama a Gabas ta Tsakiya
Time Magazine ta ce Ma’aikatar harkokin Wajen Amurka ta buƙaci ‘yan kasarta a duk faɗin Gabas ta Tsakiya da su bar yankin nan take saboda “babbar barazanar tsaro” da yaƙin Amurka da Isra’ila da Iran ya haifar.
Sanarwar ta shafi ƙasashen Saudiyya, Bahrain, Masar, Iran, Iraq, Isra’ila, Gaza, Jordan, Kuwait, Lebanon, Oman, Qatar, Syria, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Yemen.
Kurji ya fito a wuyan Shugaban Amurka
A wani labarin, kun ji cewa ana fara muhawara game da lafiyar shugaban Amurka, Donald Trump bayan fitowar kurji a wuyan shi a makon nan.
Likitan shugaba Trump ya bayyana cewa wani mai yake shafawa domin samun kariyar fata, wanda kuma shi ne ya haifar masa da kurjin.
Fitar kurjin ya dauki hankali, inda ya jawo tambayoyi musamman lura da yakin da ake cigaba da gwabzawa tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
