Abin da Nasir El Rufa'i Ya Fada wa Jami'an ICPC da Suka Matsa Masa da Tambayoyi

Abin da Nasir El Rufa'i Ya Fada wa Jami'an ICPC da Suka Matsa Masa da Tambayoyi

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce binciken da hukumar ICPC ke yi masa yana da alaka da siyasa
  • A lokacin da jami'an hukumar suka matsa masa da tambayoyi, ba su samu abin da suke bukata ba saboda matakin da El-Rufa'i ya dauka
  • Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta ce tana binciken tsohon gwamnan a kan zargin karkatar da kudi da karya dokokin kwangila

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya dage cewa bincikensa da tsare shi da hukumar ICPC na da nasaba da adawarsa da Gwamnatin tarayya.

Ya ce an sako shi a gaba ne rawar da yake takawa a jam’iyyar adawa da ADC. Ya bayyana jam'iyyar a matsayin adawa daya tilo da ta rage a kasar nan.

Kara karanta wannan

Ribadu: ICPC ta kwato na'urorin kutsen waya a gidan El Rufai

Nasir El-Rufa'i ya ki ba wa ICPC hadin kai
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Premium Times ta wallafa cewa El-Rufai yana hannun ICPC tun ranar 19 ga watan Fabrairu, 2026 bayan an sake shi daga daga hukumar yaki da rashawa ta EFCC.

ICPC, EFCC na binciken Nasir El-Rufa'i

Tun farko, tsohon gwamna Nasir El-Rufa'i ya amsa gayyatar EFCC ne a ranar 16 ga Fabrairu, kafin daga bisani ICPC ta damke shi.

A cikin rubuce-rubucen da ya yi a hannun ICPC a ranakun 19 da 20 ga Fabrairu, 2026 tsohon gwamnan ya ki amsa zarge-zargen da aka gabatar masa.

El Rufa'i ya ce zamansa a jam'iyyar adawa ne ya jawo masa matsala
Jagora a ADC kuma tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Twitter

Maimakon haka, ya bukaci a kai karar shi kotu inda zai kare kansa daga dukkanin abubuwan da ake zargin ya aikata.

Kafin nan, ya shigar da kara a babbar kotun tarayya da ke Abuja yana kalubalantar kama shi, tsare shi da kuma binciken gidansa da ke titin Mambilla 12, Asokoro.

Ya nemi kotu ta ayyana cewa an take masa hakkinsa na dan Adam tare da neman diyyar Naira biliyan daya.

Kara karanta wannan

MURIC: Kungiyar Musulunci ta kausasa harshe ga ICPC kan ci gaba da tsare El Rufai

Bukatar hukuar ICPC kan El-Rufa'i

ICPC ta bukaci kotu ta yi watsi da karar, tana mai cewa jami’anta sun gano muhimman takardu da na’urori a gidansa da ka iya barazana ga tsaron kasa.

A cewar mai gabatar da kara, David Efuk, an samu wasu na’urorin lantarki masu iya sauraron tattaunawa ta waya.

Sai dai dan tsohon gwamnan, Mohammed El-Rufai, ya musanta wannan ikirari. Ya ce tsofaffin wayoyi da kwamfutoci ne kawai aka samu a gidan.

ICPC ta bayyana cewa tana binciken El-Rufai ne bisa wata takardar koke da aka shigar a 2024.

Takardar, wacce kamfanin Nus’ab Chambers ya shigar, ta zarge shi da karkatar da kudin gwamnati, almundahana wajen sarrafa bashin da aka karba da kuma karya dokokin bada kwangila.

Alkali ya hakura da shari'ar El-Rufa'i

A baya mun wallafa cewa an samu tsaiko a karar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya shigar domin neman kare hakkinsa na dan adam.

Kara karanta wannan

Rashin El Rufa'i ya kawo tsaiko a fara shari'arsa da hukumar DSS a kotu

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya kasance a tsare tun bayan da ya kai kansa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC sannan ya fada hannun ICPC daga baya.

Alkalin kotun da Nasir El-Rufai ya shigar da kara a gabanta, ya mayar da fayil din shari'ar ga babbar alkalin kotun tarayya da ke Abuja wanda ke nufin ba zai saurari shari'ar ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng