Iran: Amurka Ta Yi Magana kan Najeriya bayan Zanga Zangar 'Yan Shi'a
- Gwamnatin Amurka ta fitar da sanarwa ga 'yan kasarta a Najeriya da sauran kasashen duniya yayin da ta ke gwabza yaki da kasar Iran
- A Najeriya, mabiya kungiyar IMN da suka yi fice cikin 'yan Shi'a sun yi zanga-zanga a jihohi da dama suna Allah wadai da kasar Amurka
- Yakin Iran da Amurka ya shafi kasashe da dama a Gabas ta Tsakiya, inda lamarin ya jawo asarar rayuka da dama da asarar dukiya mai yawa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ƙungiyar Islamic Movement in Nigeria ta gudanar da zanga-zangar lumana a jihar Legas, tana Allah-wadai da kisan Jagoran Addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai.
Hakan na zuwa ne bayan rahotanni sun ce matar Jagoran Addini na Iran Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh ta rasu sakamakon raunukan da ta samu a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai gidanta da ke Tehran.

Source: Facebook
Rahoton Punch ya nuna cewa gwamnatin Amurka ta bukaci 'yan kasarta su dauki matakan kariya a Naeriya domin kaucewa barazana.
Zanga-zangar 'yan Shi'a a Najeriya
Zanga-zangar da aka yi a Legas ranar Litinin ta biyo bayan irin wacce ‘yan Shi’a suka gudanar a jihohin Kano, Yobe, Gombe da Bauchi a ranar Lahadi.
A Legas, masu zanga-zangar sun yi tattaki a wasu sassan yankin Maryland, suna ɗauke da alluna da tutoci da ke Allah-wadai da abin da suka kira “mamayar” Iran da kuma kisan gilla kan jagoran Iran wanda ya daɗe yana mulki.
Mai kula da yankin Kudu maso Yamma na IMN, Muftau Zakariya, ya ce zanga-zangar za ta ci gaba cikin lumana kuma za a faɗaɗa ta a duk yankin Kudu maso Yamma.
Masu zanga-zangar sun rika tafiya suna rera taken goyon baya ga Iran tare da nuna adawa mai ƙarfi da matakan da Amurka da Isra’ila suka ɗauka.

Kara karanta wannan
Ana tsaka da musayar wuta, Iran ta samu gagarumin goyon baya a yaki da Amurka da Isra'ila
Hakazalika, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙi amincewa da kasancewar sojojin Amurka a ƙasar nan da aka ce za su taimaka wajen yaki da ta'addanci.

Source: Facebook
Iran: Maganar Amurka kan Najeriya
A halin da ake ciki, gwamnatin Amurka ta fitar da gargaɗin tsaro ga ‘yan ƙasarta da ke Najeriya sakamakon ƙarin tsanantar rikici tsakanin Amurka da Iran.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, hukumomin Amurka sun gargaɗi ‘yan ƙasarsu da ke ƙasashen waje da su kasance cikin shiri da lura, sakamakon harin soji da ke gudana da suka shafi Iran.
“Bayan kaddamar da harin sojin Amurka a Iran, ‘yan Amurka a duniya baki ɗaya, musamman a Gabas ta Tsakiya, su bi shawarwarin tsaro na baya-bayan nan da ofishin jakadancin Amurka mafi kusa ya fitar,”
- Inji sanarwar.
Maganar Najeriya kan yakin Iran
A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana cewa tana nan daram wajen lura da komai ya tafi lafiya a kasar.
Ta yi magana ne yayin da ake cigaba da gwabza yaki tsakanin Amurka/Isra'ila da Iran, lamarin da ya yadu zuwa kasashen duniya da dama.
'Yan sandan Najeriya sun bayyana cewa za su saka ido a ko ina a kasar, kuma ba za su bari a tayar da hankali saboda da yakin da ake ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
