Yan Ƙadiriyya Sun Shiga Jimami, Sun Yi wa Khamenei Sallar Jana'iza a Kano

Yan Ƙadiriyya Sun Shiga Jimami, Sun Yi wa Khamenei Sallar Jana'iza a Kano

  • Dubbunnan mabiya ɗariƙar Ƙadiriyya sun yi wa Ayatollah Khamenei sallatul Gha'ib a Darul Ƙadiriyya da ke Kabara Kano
  • Sheikh Mu’azzamu Nasiru Kabara ne ya jagoranci sallar gawar bayan sallar La’asar inda aka yi wa jagoran Iran addu'o'i
  • Wannan na zuwa ne bayan da aka kashe Ayatollah Ali Khamenei a harin haɗin gwiwa tsakanin kasashen Amurka da Isra’ila

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Daruruwan mabiya ɗarikar Kadiriyya a birnin Kano sun gudanar da Sallatul Ghaib ga marigayi jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Ali Khamenei ya rasu a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairu, 2026 bayan Amurka da Isra'ila sun haɗa hannu wajen kai masa hari har gida.

An yi sallar jana'izar Khamenei a Kano
Wasu daga cikin mabiya Ƙadiriyya a Kano, Ayatollah Ali Khamenei Hoto: Nafi'u Musa Bajabbare Kazaure/Iran Military
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa an gudanar da sallar ne a harabar Darul Kadiriyya da ke unguwar Kabara a Kano a ranar Litinin, 2 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Rana ta 3: Hezbollah ta shigar wa Iran fada, an kashe mutane 31 a harin sama

An yi jana'izar Ali Khamenei a Kano

21st Century Chronicles ta wallafa cewa an yi sallar jana'izar bayan sallar La’asar inda aka nuna jimaminrasuwar jagoran addini a Iran.

Wurin dai shi ne mazaunin marigayi Sheikh Nasiru Kabara, jagoran ɗarikar Kadiriyya a Afrika, wanda ya rasu a shekarar 1993.

Babban ɗansa, Sheikh Mu’azzamu Nasiru Kabara ne ya jagoranci sallar jana’izar, inda aka roƙi Allah Ya gafarta wa mamacin, Ya kuma yi masa rahama da.

Sallar ta samu halartar mabiya da dama da suka taru domin nuna alhini da addu’a ga mamacin da Amurka da Isra'ila suka kashe.

An yi wa Ayatollah Khamenei addu'a

Daga cikin fitattun mutanen da suka halarci sallar jana'izar gha'ib har da Sheikh Musal Kasiyuni Nasiru Kabara.

Tun da fari, Sheikh Musal Kasiyuni ya sanar da shirin gudanar da sallar ta cikin wani bidiyo da ya fitar bayan rasuwar Khamenei.

An yi addu'a don nema wa Khamenei rahamar Allah
Marigayi jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei Hoto: Getty
Source: Getty Images

Ana yi wa gawa sallah ko ba ta nan?

Salatul gha'ib wata salla ce ta jana’iza da ake yi wa mamaci idan gawarsa ba ta wurin, ko kuma idan ya rasu a ƙasar da babu Musulmai da za su gudanar masa da jana’iza.

Kara karanta wannan

Yan Shi'a sun yi zanga zanga a Kano da jihohin Arewa kan kashe Khamenei a Iran

A tarihin Musulunci, an fara yin irin wannan salla ne a zamanin Annabi Muhammad (SAW), lokacin da ya yi wa sarkin Habasha, Najashi, sallar Ghaib bayan rasuwarsa.

Gudanar da Sallar gha'ib a Kano ya nuna yadda wasu mabiya darikar Kadiriyya ke nuna damuwa da alhini kan rasuwar jagoran na Iran, tare da roƙon Allah Ya jikansa da rahama.

Matar Khamenei ya rasu

A baya, mun wallafa cewa kwanaki biyu bayan kashe jagoran addinin kasar Iran, Imam Ayatollah Ali Khamenei, matarsa ta riga mu gidan gaskiya a ranar Litinin 2 ga watan Maris 2026.

Rahotanni sun nuna cewa matar Ali Khamenei, Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh ta rasu ne sakamakon raunukan da ta samu a harin Amurka da Isra'ila suka kai ƙasar.

Wannan dai na zuwa ne bayan harin hadin gwiwa da Amurka da Isra'ila suka kai birnin Tehran, wanda ya taba ofishin jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei har ya rasu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng