Kwana Ya Kare: Sarki Mai Martaba a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Watan Azumi

Kwana Ya Kare: Sarki Mai Martaba a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Watan Azumi

  • A yau Litinin, 2 ga watan Maris, 2026, aka tabbatar da rasuwar Sarkin Ikire da ke jihar Osun, Oba Olatunde Falabi, yana dan shekara 91
  • Shugabar karamar hukumar Irewole da ke jihar Osun, Dr Esther Okunola ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin
  • Ta ce al'ummar yankin masarautar sun yi rashin uba, wanda hikimarsa, jarumtarsa da shawarwarinsa suka kasance ginshikin hadin kan al'umma

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun, Nigeria - Sarkin Ikire da ke jihar Osun a Kudancin Najeriya, Oba Olatunde Falabi, ya riga mu gidan gakiya, yana da shekaru 91 a duniya.

Shugabar karamar hukumar Irewole da ke jihar Osun, Dr Esther Okunola, ce ta sanar da rasuwar sarkin a wata sanarwa da aka samu a Osogbo a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Arewacin Najeriya ya shiga yankunan da ake sa wa ido

Oba Olatunde Falabi
Wani basarake a jihar Osun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya, Oba Olatunde Falabi Hoto: Ashabe Okfor
Source: Facebook

Wani Sarki a jihar Osun ya rasu

Sai dai majiyoyi na kusa da fadar sarkin sun ce Oba Falabi ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya a karshen mako, kamar yadda jaridar Punch ta kawo.

A sakon ta’aziyyarta da ta aika, Okunola ta bayyana rasuwar a matsayin “faduwar giwa babba,” tana mai cewa Ikire da daukacin karamar hukumar Irewole sun yi babban rashi

Shugabar karamar hukumar ta ce al'ummar yankin masarautar sun yi rashin uba, wanda hikimarsa, jarumtarsa da shawarwarinsa suka kasance ginshikin hadin kai da cigaba.

An yabi marigayi Oba Olatunde Falabi

Ta ce mulkinsa ya kasance mai cike da zaman lafiya, kare al’adu da kuma jajircewa wajen bunkasa yankin masarautar Ikire

“Jagorancin da marigayin ya yi, ya kara karfafa harkokin gargajiya da al'adu tare da samar da zaman lafiya a tsakanin al’ummarsa.
“Lallai idan giwa babba ta fadi, daji kan girgiza. Mai martaba ya rayu rayuwa ta kima da hidima. Gadon da ya bari na aiki da hidima za su ci gaba da zama abin koyi ga muate a nan gaba," in ji ta.

Kara karanta wannan

Jagoran Musulunci na Iran: Mutane 5 da za su iya maye gurbin Ayotallah Khamenei

Hon. Okunola ta kuma mika ta’aziyya ga iyalan gidan sarauta, Majalisar Gargajiya ta Akire da al’ummar Ikire, tana mai hadawa da addu’ar Allah Ya jikansa da rahama.

Olatunde Falabi.
Mai martaba Akire na masarautar Ikire a jihqr Osun, Oba Olatunde Falabi Hoto: Tajudeen Adekola
Source: Facebook

Takaitaccen bayani kan marigayi Sarki

Punch ta ce Oba Falabi, wanda kwararren masanin harkokin magunguna ne, an nada shi a matsayin Akire na Ikire a watan Mayu 1993, inda ya yi sarauta sama da shekaru 30.

A lokacin mulkinsa, garin ya samu ci gaban tattalin arziki da siyasa, ciki har da kafa Kwalejin Harsuna da Ilimin Dan Adam ta Jami’ar Jihar Osun a Ikire, da kuma fitowar Benedict Alabi, dan asalin garin, a matsayin mataimakin gwamnan jihar Osun.

Tsohon mataimakin gwamnan Delta ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, ya bayyana alhininsa kan rasuwar tsohon mataimakin gwamna da aka taba yi a jihar.

Gwamnan ya ce ya samu labarin rasuwar cikin kaduwa da radadi, amma tare da godiya ga Allah kan rayuwa mai cike da hidima da marigayin ya yi wa Osun da Najeriya baki daya.

Oborevwori ya bayyana marigayin a matsayin dan kishin kasa, gogaggen mai ma'aikaci, kuma jajirtaccen dan jam’iyya wanda za a ci gaba da tunawa da ayyukan alherinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262