Tura Ta Kai Bango: Dan El Rufai Ya Tona Makarkashiyar ICPC kan Mahaifinsa, Ya Yi Zarge Zarge

Tura Ta Kai Bango: Dan El Rufai Ya Tona Makarkashiyar ICPC kan Mahaifinsa, Ya Yi Zarge Zarge

  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta ce ta gano nau'rorin yin kutse ta waya a gidan Malam Nasir Ahmad El-Rufai
  • Dan tsohon gwamnan na jihar Kaduna, Mohammed Bello El-Rufai, ya fito ya yi magana kan zarge-zargen da ICPC ke yi wa mahaifinsa
  • Bello El-Rufai ya bayyana cewa hukumar tana son yin amfani ne da shirun da mahaifinsa ya yi a matsayin makamin da za ta yi yaki a kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hon. Mohammed Bello El-Rufai, mamba a majalisar wakilai, ya zargi hukumar ICPC da kaddamar da yakin neman ɓata suna ga mahaifinsa, Malam Nasir El-Rufai.

Bello El-Rufai ya zargi ICPC da kokarin bata sunan mahaifinsa ta hanyar mayar da haƙƙinsa na yin shiru da tsarin mulki ya ba shi dama ya zama wani makami na yaƙi da shi.

Kara karanta wannan

Jagoran Musulunci na Iran: Mutane 5 da za su iya maye gurbin Ayotallah Khamenei

Dan El-Rufai ya yi zarge-zarge kan ICPC
Mohammed Bello El-Rufai da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: Bello El-Rufai
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata doguwar sanarwa da Mohammed Bello El-Rufai ya fitar a madadin iyalan El-Rufai, a ranar Litinin, 2 ga watan Maris 2026 a shafinsa na Facebook.

Bello El-Rufai ya caccaki hukumar ICPC

Bello El-Rufai ya bayyana cewa "abin takaici ne kwarai" yadda wata hukuma da tsarin mulki ya samar ta koma yin "wasan kwaikwayo na yaudara,"

'Dan majalisar ya yi zargin cewa ICPC ta fi mayar da hankali kan yaƙin kafofin yaɗa labarai maimakon bin tafarkin doka.

Dan El-Rufai ya musanta ikirarin ICPC

Yayin da yake martani kan iƙirarin hukumar na cewa Nasir El-Rufai ya ƙi ba da haɗin kai ga masu bincike, ɗan majalisar ya ce wannan zargi ya nuna rashin fahimtar muhimman kariya da tsarin mulki ya ba ɗan ƙasa.

Ya kafa hujja da cewa tsarin mulki na shekarar 1999 ya ba kowane ɗan ƙasa haƙƙin yin shuru, sannan ya jaddada cewa yin amfani da wannan haƙƙi ba zai zama dalilin da za a fassara shi a matsayin rashin ba da haɗin kai ko kuma tabbacin laifi ba.

Kara karanta wannan

Macron ya fadi shirin da Faransa ke yi bayan Amurka da Isra'ila sun kai wa Iran hari

“Mahaifinmu ya dade yana gaya wa hukumomin tsaro: ‘Ku gurfanar da ni idan kuna da wani abu a kaina. Kun kwashe sama da shekaru biyu kuna bincike na. Ku kai ni kotu,’”

- Bello El-Rufai

Iyalan El-Rufai sun yi zargi

Haka kuma, iyalan sun yi zargin cewa duk binciken da aka gudanar an gina shi ne a kan takardar izinin bincike ta jabu kuma marar inganci a shari’ance.

Sun bayyana cewa lauyoyinsu sun riga sun ƙalubalanci takardar a kotu, suna masu cewa duk wata shaida da aka samu ta wannan hanyar ba za a amince da ita ba.

Bello El-Rufai ya ragargaji hukumar ICPC
Dan majalisar wakilai mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Mohammed Bello El-Rufai Hoto: Bello El-Rufai
Source: Facebook

Iyalan sun ce za su bi duk hanyoyin shari’a da suka dace, kuma suna da yaƙinin cewa sashen shari’a na Najeriya zai kare haƙƙoƙinsu.

Har ya zuwa yanzu, hukumar ICPC ba ta mayar da martani a fili game da waɗannan sabbin zarge-zargen ba.

Alkali ya mayar da shari'ar El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta mayar da karar da Nasir El-Rufai ya shigar zuwa ga babban alkalin babbar kotun tarayya.

Alkalin da ke sauraron karar, mai shari'a Belgore, ya sanar da cewa ya mayar da shari'ar ne domin a ba da ga wani sabon alkali.

Sanarwarsa ta sa ta tafiya hutu ta sa ya zama dole a mayar da takardar shari’ar don a damƙa ta ga wani alƙali na daban.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng