Yan Shi'a Sun Yi Zanga Zanga a Kano da Jihohin Arewa kan Kashe Khamenei a Iran

Yan Shi'a Sun Yi Zanga Zanga a Kano da Jihohin Arewa kan Kashe Khamenei a Iran

  • 'Yan kungiyar IMN sun gudanar da zanga-zanga a jihohi akalla shida kan kisan jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei
  • A ranar 28 ga watan Fabrairu, 2026 ne harin hadin gwiwa da Amurka da Isra'ila suka kai Iran ta hallaka jagoran addinin
  • Masu zanga-zanga a Najeriya sun ce sun fito ne domin nuna goyon baya ga Iran da neman adalci kan mummunan aikin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Mambobin kungiyar IMN, wadda aka fi sani da ‘yan Shi’a, karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, sun gudanar da zanga-zanga a Najeriya.

Sun yi zanga-zangar ne a jihohin Gombe, Neja, Kano, Bauchi, Yobe da Sakkwato kan kisan Jagoran addinin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Yan Shia sun yi zanga-zanga kan mutuwar Khamenei
Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei Hoto: Getty
Source: Getty Images

Daily Trust ta wallafa cewa rahotanni sun bayyana cewa zanga-zangar ta biyo bayan wani harin sama da aka ce hadin gwiwar Amurka da Isra’ila ne suka kai a Iran, wanda ya janyo mutuwar Khamenei.

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki a Iran bayan rasuwar jagoran addini, Ayatullah Ali Khamenei

'Yan Shi'a sun shiga jimami a Najeriya

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa daruruwan 'yan Shi'a sun gudanar da zanga-zanga a birnin Kano ranar Lahadi kan rahoton kisan Jagoran Addinin Musulunci na Iran, Ali Khamenei.

Masu zanga-zangar, dauke da tutocin Iran da hotunan Khamenei, sun rika tattaki a wasu sassan birnin, suna mai bayyana cewa fitowarsu wani mataki ne na nuna goyon baya ga al’ummar Iran.

Sun danganta zanga-zangar da hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra’ila da aka ce su ne suka janyo mutuwar jagoran na Iran.

Tattakin na lumana ya fara ne daga Masallacin Fagge ta Tsakiya da 3:00 na rana, inda mahalarta suka nufi Cibiyar IMN da ke Kofar Waika.

A can ne aka gudanar da jawabai da kuma addu’o’i na musamman domin nuna alhini da kuma neman taimakon Ubangiji ga al’ummar Iran yayin da rikici ke kara kamari a yankin Gabas ta Tsakiya.

Yadda 'yan Shi'a suka yi zanga-zanga

A jihar Gombe, 'yan IMN sun gudanar da zanga-zanga cikin lumana bayan idar da salla a cibiyarsu da ke Tudun Wadan Pantami.

Kara karanta wannan

Iran ta dauki manyan matakai 3 bayan Amurka ta kashe jagoran Musulunci, Khamenei

Suna dauke da alluna masu dauke da sakonnin Allah wadai da harin Amurka da Isra'ila, tare da kiran a yi adalci.

Da yake magana a madadin masu zanga-zangar, Sheikh Muhammad Abbari Gombe ya bayyana harin da aka kai wa Iran a matsayin abin takaici da ba za a amince da shi ba.

Yan Shia sun yi tir da hallaka Khamenei
Shugaban kungiyar yan Shia ta IMN a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky Hoto: @am_ghoulam
Source: Twitter

Ya kuma bukaci mabiyansu su kwantar da hankalinsu, su bi doka da oda, tare da ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu ta hanyoyin lumana.

An kuma ga jami’an tsaro sun bazama a wasu sassan birnin Gombe yayin da ake gudanar da tattakin.

A jihar Neja ma, an ruwaito cewa ‘yan Shi’a sun yi irin wannan zanga-zanga, inda suka rika daga tutocin Iran da alluna masu dauke da rubuce-rubuce irin su "muna tare da Iran."

A wata sanarwa da aka rabawa magoya baya, IMN ta nuna alhini kan rasuwar Khamenei, tare da jaddada kudurinsu na ci gaba da goyon bayan al’ummar Iran.

Haka kuma kungiyar ta bayyana adawa da abin da suka kira tsoma bakin kasashen Yamma a harkokin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Amurka da Isra'ila sun kashe jagoran addinin Musulunci na Iran

Haka zalika, a jihar Sakkwato, wasu Musulmi sun fito zanga-zanga, suna rera taken nuna goyon baya da dauke da alluna masu nuna adawa da kisan jagoran na Iran.

Iran: 'Yan sanda na sa ido a Arewa

A baya, mun wallafa cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi magana game da yanayin tsaron kasa yayin da ake cigaba da gwabza yaki tsakanin Iran da Isra'ila da Amurka.

Mukaddashin sufeto janar na ’yan sanda, Olatunji Disu ya umarci dakarunsa da su kara sa ido domin tabbatar tsaro dukkannin sassan Najeriya don tabbatar da tsaro.

Olatunji Disu ya bukaci bayar da kulawa ta musamman ga wasu yankunan Arewacin Najeriya domin tabbatar da komai ya tafi lafiya yayin rikicin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng