Yadda Yakin Iran, Amurka da Isra'ila zai Jawo Tarnaki a Najeriya
- Masana makamashi sun yi gargaɗin cewa rikicin Amurka da Iran na iya jawo tashin farashin fetur da dizal a Najeriya
- Wannan barazana za ta tabbata ne idan farashin ɗanyen mai ya haura Dala 90 kan kowace ganga a kasuwar duniya a yanzu
- Duk da fara tace mai a gida, Najeriya na dogaro da ɗanyen mai da ake shigowa da shi daga waje, wanda aka tacewa a nan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Nigeria – Masana makamashi da masu harkar kasuwar man fetur sun ce rikicin da ke ƙara kamari tsakanin Amurka da Iran na iya jawo sabon tashin farashin fetur a Najeriya.
Sun bayyana cewa idan farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya haura Dala 90 kowace ganga, lallai hakan zai shafi farashin man fetur da dizal a cikin gida.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa a yanzu, ana sayar da fetur tsakanin N824 zuwa N880 kan kowace lita a manyan birane, gwargwadon nisan gari da farashin sufuri.
Wannan na zuwa ne bayan matatar Dangote ta rage farashin man fetur daga N799 zuwa N774 kan lita a watan Fabrairun 2026.
Masana a bangaren fetur sun hango matsala
Daily Trust ta wallafa cewa masana sun ce duk wani dogon rikici a Gabas ta Tsakiya, musamman a mashigar ruwan 'Strait of Hormuz', na iya ƙara farashin mai a duniya.
Mashigar ruwan na haɗa Tekun Farisa da Tekun Indiya, kuma sama da 20% na man duniya na wucewa ta cikinta. Idan aka samu tangarda, farashi kan tashi.
Rahotanni sun nuna cewa farashin a yanzu ya kai kusan Dala 80 kowace ganga, yayin da na Najeriya ya kai sama da Dala 78. Masu hasashe sun ce farashi na iya kaiwa Dala 100 idan rikicin ya tsananta.

Source: Facebook
Shugaban kamfanin Dairy Hills, Kelvin Emmanuel, ya ce har yanzu matatar Dangote na shigo da mafi yawan ɗanyen man da take tacewa daga waje.
A cewarsa, daga kusan ganga miliyan 18 da ake tacewa duk wata, fiye da miliyan 12 na shigo wa ne daga ƙasashen waje.
Tsarin farashin mai a Najeriya
Shugaban Petroleumprice.ng, Olatide Jeremiah, ya ce duk da cewa Najeriya ce babbar mai fitar da ɗanyen mai a Afrika, har yanzu farashin cikin gida na karkashin tasirin kasuwar duniya.
Ya ce dokar 'PIA' ta fifita matatun gida wajen rabon ɗanyen mai, amma ba a cika samar masu isasshe ba.
Wani masani a fannin dokar makamashi daga jami'ar Legas, Dayo Ayoade, ya ce tun bayan cire tallafin fetur, mai a cikin gida ya koma kasuwanci, don haka duk wani tashin farashin ɗanyen mai zai bayyana kai tsaye .
Sai dai Farfesa Wumi Iledare ya ja kunnen jama’a da kada su firgita, yana mai cewa kasuwar mai ta duniya yanzu ta fi daidaito da faɗi fiye da shekarun baya..

Kara karanta wannan
Dangote ya shiga yarjejeniya da manyan kamfanoni, za a rika fitar da lita miliyan 65 kullum
Ana rage farashin man fetur a Najeriya
A baya, mun wallafa cewa 'yan Najeriya na ci gaba da ganin gasa tsakanin masu kasuwancin man fetur a kasar tun bayan cire tallafin da shugaba Tinubu ya yi .
Rahotanni sun nuna cewa ana samun ragin farashi biyo bayan sauye-sauyen da aka samu kwanan nan a farashin fetur a gidajen mai da ke sassan Najeriya.
Gasa tsakanin manyan masu samar da mai, ciki har da matatar Dangote, na taka muhimmiyar rawa wajen saukar da farashin mai wanda ƴan Najeriya ke mora.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

