Yawan Sojojin Amurka da Suka Mutu bayan Harin Iran, Wasu da Dama Sun Jikkata

Yawan Sojojin Amurka da Suka Mutu bayan Harin Iran, Wasu da Dama Sun Jikkata

  • Hukumomi a kasar Amurka sun tabbatara mutuwar wasu daga cikin sojojinsu yayin da ake ci gaba da arangama da kasar Iran
  • Majiyoyi sun ce wasu sojojin biyar sun jikkata matuka a hare-haren yaki da Iran wanda ya jawo suka daga kasashen duniya
  • Iran ta kai hare-haren ramuwar gayya kan sansanonin sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya wanda ya jawo kulle wasu filayen jiragen sama

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Rahotanni sun tabbatar da mutuwar wasu daga cikin sojojin Amurka yayin arangama da kasar Iran da ake yi.

An ce sojoji uku sun mutu a yayin artabu da Iran, yayin da wasu biyar suka samu munanan raunuka wanda ake ci gaba da ba su kulawa.

Sojojin Amurka 3 sun mutu a yaki da Iran
Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin jami’an rundunar 'United States Central Command' wanda aka wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Khamenei da manyan shugabannin tsaron Iran 4 da suka rasu, ya rasa wasu iyalansa

Sanarwar ta ce wasu karin sojoji sun samu kananan raunukan fashewar abubuwa mai taba kwakwalwa, kuma ana shirin mayar da su bakin aiki.

Yadda Iran ta mayar da martani kan Amurka

Rahotanni sun nuna cewa Iran ta kaddamar da jerin hare-haren ramuwar gayya kan sansanonin sojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, bayan harin hadin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a wani farmaki da aka yi wa lakabi da “Operation Epic Fury.”

Da fari dai, rahotanni sun nuna babu asarar rayukan Amurka, sai dai daga baya aka tabbatar da mutuwar sojojin uku.

Sanarwar ta ce:

“Manyan ayyukan yaki na ci gaba kuma martaninmu yana gudana.”
Harin Iran ya hallaka wasu sojojin Amurka
Marigayi Ayatulla Ali Khamenei na Iran. Hoto: @khamenei_ir.
Source: Twitter

Gaskiyar rahoton kai hari kan jirgin ruwan Amurka

An kuma yada jita-jita cewa rundunar IRGC ta kai hari kan jirgin ruwan yaki na Amurka, USS Abraham Lincoln, amma jami’an CENTCOM sun musanta hakan, suna cewa ko kusa makaman ba su isa jirgin ba.

Harin na hadin gwiwa ya fara da misalin karfe 1:15 na safe, inda aka nufi cibiyoyin umarni na IRGC, wuraren harba makamai masu linzami da jirage marasa matuki, da kuma filayen jiragen soja.

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki a Iran bayan rasuwar jagoran addini, Ayatullah Ali Khamenei

Rahotanni sun kuma ce an kai hari kan harabar jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, inda wani babban jami’in Isra’ila ya shaida cewa an kashe shi.

Kungiyar agajin gaggawa ta Iran ta ce akalla mutane 201 sun mutu, yayin da sama da 700 suka jikkata sakamakon hare-haren.

Hukumomi sun ce ba za a bayyana sunayen sojojin Amurka da suka mutu ba har sai an sanar da iyalansu.

Yadda CIA ta taimaka aka kashe Khamenei

Kun ji cewa rahotanni sun bayyana yadda hukumar leken asiri ta CIA ya ba da gudunmawa wurin farmaki kan Ayatullah Ali Khamenei.

Majiyoyi sun ce bayanan sirri sun taimaka wa Amurka da Isra’ila kashe jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, a harin Tehran.

An ce CIA ta dade tana bibiyar Khamenei, inda ta gano taron manyan jami’an tsaro da aka shirya a wani katafaren wuri domin tattauna halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.