Mutane Sun Mutu Ana Azumi, Wasu da Yawa Sun Jikkata yayin Karbar Zakka a Katsina
- An rasa rayuka yayin rabon Zakkar Ramadan a gidan wani attajiri da ke Kofar Guga a jihar Katsina wanda ta tayar da kura
- Mutane 18 sun jikkata, an garzaya da wadanda suka ji raunuka zuwa Babban Asibitin Katsina domin kulawar gaggawa
- ‘Yan sanda sun gayyaci wadanda suka shirya rabon Zakkar domin tambayoyi yayin da bincike ke gudana kan iftila'in
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Mutum hudu sun rasa rayukansu yayin da suka je karbar Zakka da ake raba wa sakamakon turmutsitsi da aka samu a jihar Katsina.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa wasu mutane 18 suka jikkata sakamakon hargitsin da ya faru a wani gida da ke cikin birnin Katsina.

Source: Original
Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama cewa lamarin ya faru da misalin karfe 9:00 na dare ranar 26 ga watan Fabrairun 2026 a gidan Alhaji Dahiru Usman Sarki da ke unguwar Kofar Guga.
Yadda halin matsi ke jawo rasa rayuka
Ana yawan samun rasa rayuka musamman a rabon Zakka ko kayan abinci wanda mutane da dama ke tururuwa saboda su samu na rufin asiri.
Wasu na ganin hakan bai rasa nasaba da halin kunci da aka jefa al'umma tun bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Tinubu ta yi.
Zakka: An rasa rayukan mutane 4 a Katsina
Rahotanni sun nuna cewa an samu taron jama’a mai yawa domin karbar Zakkar Ramadan, inda wasu ake zargin sun yi kokarin kutsa kai cikin harabar gidan, lamarin da ya haddasa turmutsitsi.
Jami’in ‘yan sanda mai kula da ofishin yan sanda a Katsina ya gaggauta isa wurin tare da jami’ansa, inda suka samu nasarar shawo kan lamarin.
Sakamakon turmutsitsin, mutane 18 sun samu raunuka daban-daban, kuma an garzaya da su zuwa Babban Asibitin Katsina domin samun kulawar likitoci.

Source: Facebook
Sunayen wadanda suka mutu yayin turmutsutsun
Daga bisani, likita ya tabbatar da mutuwar mutum hudu wanda aka bayyana sunayensu da Bilkisu Mamman mai shekaru 40 daga Kerau; Ihsan Musbahu mai shekaru 40 daga Abattoir.
Sauran sun hada da Aisha Sani mai shekaru 16 daga Kofar Sauri; da Salamatu Kabir mai shekaru 45 daga Sabuwar Unguwa.
An mayar da wata yarinya mai suna Hafsat Zubairu mai shekaru 15 daga Masanawa Asibitin Koyarwa na Tarayya domin ci gaba da duba lafiyarta.
Hukumomin ‘yan sanda sun ce an gayyaci wadanda suka shirya rabon Zakkar domin amsa tambayoyi, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin lamarin.
An rasa rai yayin turmutsitsi a sallar Idi
Mun ba ku labari a baya cewa rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta tabbatar da mutuwar yara biyu sakamakon turmutsitsi da ya auku a babban filin Sallar idi na Gombe.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:45 na safe yayin da jama’a suka yi kokarin fita cikin gaggawa, lamarin da ya janyo jikkatar mutum 22.
An garzaya da wadanda suka jikkata asibitoci daban-daban, yayin da Gwamna Inuwa Yahaya ya dauki nauyin jinyar dukkan wadanda suka sami raunuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

